Chapter 23

504 60 0
                                        

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍🏻 Rashida Bature

PAGE2️⃣2️⃣

Shiru nayi na dubi hajiya kaka nace amma hajiya ke kina ganin da gaske halintan ta gyara ko kuma wani salon ta take ?

"to khubra inma salo ta sake ai Allah baya barci shi zaimana maganin kowa dayake nufinmu da sharri ,karki manta infa baka da alhakin wani tofa asannu Kai da aka d'auki naka alhakin Allah zai maka sakayya da Wanda ya cuceka ,kedai ki dage ki rike Allah akoda yaushe karkiyi sakaci da addu'a domin shine madogaranki, kikuma rike sallah banda wasa da ita na haneki dakinyin sallah akan lokaci allah ya shiryaku da dukkan musulmi baki d'aya  amiin kaka in sha Allah zan dage .

"nikuwa khubra Anya kinyi lissafin kud'in dakika gayama hajiyan alhaji majeed kuwa ?senaga kamar ba dai dai kika gaya mataba .

"Kaka bafani na gaya mata ba ita ta fad'a da kanta in zaki tuna cewafa nayi kowani kaza 1, 2000 ne to tace 20k aikinga bazan musa ba kumani wllh kaka banso na amshi ko kwandala ba saboda kinga filinta dana diba batace na biyata ba ga wani dilin data bayar in zanyi ma kaina adalci Inna bata kaji ko guda hamsinne ban fadi ba don in biyanta zanyi kudin filinta senabiya samada dubu dari nawa Amma bataga hakaba ta bani kudin kajina .

"hakane kuma sudai kam  halinsu yanada kyau sunada taimaka ma nakasa dasu Allah yabiyasu .mikewa mukayi muka nufi d'aki domin yin alwalan magriba .

"Hajiya Sun iso gida ana Kiran sallan magriba sun iske mom itada sateera da ma'aikatan gidan awaje sunshigo yayi dai dai da isowar alhaji majeed arab daga falonsa rike da waya ahannu ganin motarsu amjaad  yasashi nufo inda suke , kofar motar ya bud'e ma hajiya ta futo yace hajiya ashe keda yaronki ma kuka futa ?munan hankalinmu duk ya tashi don na tambayi Ina kike rukayya tace bataji futarkiba me gadi kuma yace yaga futarki da direba amma besan Ina kukajeba ganin  kunjima baku dawoba duk hankalinmu ya tashi ,yanzuma komawata daki kenan zam dauko wayata nakira dpo na sanar masa .

"Inbanda abunka bata zanyi ai zan dawo kuma ai tare muke da d'an hajiya .

"To gani nayi hajiya baki zuwa ko ina shiyasa Amma yazu alhamdulillah tunda gaki kin dawo .

Mom ne ta karaso tanama hajiya barka da dawowa tareda karb'an jakar hannunta Wanda take Sanya cover din glass dinta aciki .

"Rukayya idan mukayi sallah kizo ki sameni keda mijin naki idan suma sun dawo daga masallaci inason magana daku.to hajiya in sha Allah ahuta gajiya.

Bayan sallah isha'i hajiya ne zaune itada mom da alhaji majeed arab akatafaren falon ta tamkar ba falon tsohuwa ba don komai da akesawa adakin matar mashiya itama haka danta alhaji majeed yayi mata gawani raban sannyin ac na aikinsa .

"Dubansu hajiya tayi tace  majeed gaka ga matarka shawara nakeson nabaku amma inkunga tayi duk da nasan yau ne aka tura gidan su waccan yarinyar , to hakan bashine zaisa na fasa zancena ba.
Shiyasa nace gaka gani ga matarka inkunji abun be mukuba ku bude baki kumin magana don shiyasa nace shawara ba umurni ba kema rukayya karkiji nauyin don Ina uwar mijinki kice zakimin kara ki cuci kanki dana yaronki inkikayi haka baki kyauta minba domin ni a ya na daukeki .

"Abunda yasa nace kuzo ba komai bane illa naje na nemo ma amjaad matar aure.....

Dasauri alhaji majeed ya d'ago kanshi yana me duban haifiyar tashi donjin wannan kalma data futo daga bakinta .

"Itakam mom kanta yana asunkuye tunda hajiya tafara maganar dama ta sunkuyar da kanta don bazata iya zuba ma bakinta ido tana kallon duk wani harafin da zai futo daga bikinba.

"Ey nasan dole hakan ta faru zakace ko na manta da wancan auren ne , a'a ban manta ba ,kasani yau daya nafara ganin yarinyar naji ta kwantamin arai atake kuma nasa akamin bincikenta tunkafin nabar gurin danaga yarinyar,kuma alhamdulillah duk wani abunda akeso ga diya mace takasance yarinyar nan ta samu don haka nayi sha'awar ta kasance  acikin family mu nama jikana sha'awar sama mishi abokiyar rayuwa tagari wacce zata zamo mishi uwar yayansa ta kwarai na tabbata kuma inkukaji shaidar data samu agarin dakuma abunda idona ya ganemin na tabbata zaku so kasancewa da ita a inuwa d'aya.

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now