💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
Wattpad https://my.w.tt/Su8JNMVKlcb
PAGE4️⃣7️⃣
"Au kema haka zakice ko?
ban kulasuba nayi fucewa ta f,arar mota na na tarar da an wanke mun ita se d'aukar ido takeyi ,sauri nayi na bud'e gidan baya na zauna , amjaad daya futo yaganni yace "yah haka madam?
kaina langab'e nayi kalan tausayi "zawjy a tausaya min bazan iya tuka manya kamar kuba.
to tanan kika bullo kenan ?
to sedai akoma gida don nima ban shirya tuka manyan mata kamarku ba ya bud'e k'ofar gefen direba gurin me zaman banza agurin ya zauna "to anty rumana se ki zo ki tukamu muje .
"wato wayo kukamin ?kunci bashi zanyi rabi anjima dayanku zai amsa ya k'arasa ,ta shiga motar muka futa agidan tace "wai gaskiya kuna da nauyi kai ,ga mai nauyi a baya ita yanzu ai nauyin mutum uku ne gare ta ."oho dai haka dai mutum zasu jamu muje .
ranar danaje gidan mu kamar kar na dawo haka nakeji ,mun wuni da 'yan uwana munsha hira daganan muka zazzaga dangi da makwafta se dare amjaad yazo yaja motar danazo da ita muka koma gida.
a hankali nida rumana muka sake ba wani fad'a ko nuna kishi a fili kowa ya sake da dan uwanshi ,don ko shawara zatayi takanzo gurina ta nemi shawara kuma takanyi aiki dashi ,a hankali tafara koyon karatun addini aguna abun dai se Wanda ya ganmu kanmu ahade yake se abhnda ba'a rasaba .
kwance tashi ba wuya yau juma'a na tashi da labour tun asuba nake abu d'aya dayake amjaad ba agurina yake ba yau ,na daure nace hala ciwon zai lafamin anjima ,amaimakon naji abu ya lafa se gaba gaba naji abu yakeyi karfe bakwai dai dai agogon d'akina yana bugawa wani abu ya fashe daga gabana se ruwa ya biyo baya ba'a jimaba kuwa sega nishi me karfi ya tahomin duk azaban danakeji na ciwo bai hanani takarkarewa nayi nishi ba,inayi naji kamar ana ballamin kasusuwan k'uguna sallati nakeyi hade da nishi futttt naji abu ya fito ta gabana naji kamar an yayemin duk wata cutar duniya hamdala nayi bankai ga sauke hamdalan danayiba naji wani nishin ya tahomin da karfi tareda wani azababben ciwo kasa daurewa nayi nasa kuka Ina had'awa da salati don nakasa rik'e komai akaina ,cikin ikon Allah shima naji abu ya tokaremin gaba can sega wani nishin ya zomin na daddage nayi naji abu yafuta tareda ihun kukan jinjiri ,komawa nayi na kwanta a yanda nake Ina me sauke ajiyar numfashi tareda lumshe ido na don wani barci me mugun dad'i ne yake son d'auka na ,kukan da jariran sukeyi ne ya dawo dani daga barcin dayakeson ya d'aukeni zanin gadon na janyo na rufa musu don sanyin gurin gashi bansan yaya zanyi dasuba , d'akin nakebi da Ido can na hango wayata akan gadon don bani barin wayata tayi nisa dani tunda nashiga watana mom tanemi daya dawo dani gurinta yak'i tace nake ajiye waya akusa dani ,hannu nakai kan gadon don na dauka amma bankai gurinba fulan dayake kusa dani na sa na janyo wayar dashi amjaad nafara lalub'o wa a wayar tayi ringin harta katse ba'a d'aga ba,dole na nemo number mom ringing biyu tayi ta d'aga "daughter lafiya?
"lafiya lw mom so nakeyi kizo yanzu ki dubani nayi maganar a wahale ..batajira na gama maganar ba ma takashe tana neman mayafin ta ,tsabar rikicewa ma rasa yanda mayafin suke tayi don haka ta d'auki mayafin abayan sateera data gani a falo ta yafa tafito ,sashin hajiya ya nufa a hanzarce ta shaida mata abunda nace itama futowa sukayi atare suka nufo gidanmu ,basu tsaya buka k'ofar falon ba murd'a wa sukayi sukaci sa'a tana bud'e tunda amjaad yaje masallaci yadawo se bai sake rufewa ba , direct sashina suka nufo .
salatin hajiya ne ya tayar dani a barcin daya d'auken ga yaran a lullube agun suna kananan kuka ,d'aukar su hajiya tayi ta rabasu da kasa mom kuma ta nufi kwatin dana had'a don zuwa asibiti,yanke cibi suka farayi tareda gyara gurin ,sanda mukayi wankan dukanmu muka futo fes sannan hajiya tamin fad'an gangacin danayi na haihuwa ni kadai a d'aki ,mom ta koma sashinta ta had'omin lafiyayyan abincin da me aikinta tayi sanda na fara shan tea me kauri sannan nasha farfesun kan saniya take take zufa ya karyo min hajiya ta mikomin yaran tace maza karb'i masu cinnan ce tand'e baki sukeyi suna neman abincinsu ,tunda kin k'oshi suma a daure abasu nasu .
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Ficción GeneralLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...
