chapter 3

1K 73 1
                                    

💍 CIKAKKIYAR MACE💍

✍️ Real Rashida Bature.

PAGE2️⃣

Wani kallo yabi inna saratu dashi irin kallon baki da hankali yakad'a kansa yayi wucewarsa cikin dakinsa,sororo inna saratu tayi tana me binsa dakallon mamaki ta tafa hannu oh ni saratu! aikuwa malam zama bai gankaba futowa zakayi kasayomin kwai don tunda nasa ran cin kwai yau fa senaci ,inna tunda adda khubra bata bayarba to kikawo kudi nasiyo Miki a gun isibu me shago cewar rabe dayake gefen inna saratu azaune,ey lallai kam tunda ance maka sunana saratu sarkin asara ai dole nasaya ma kartin banza kwai suci su lashe baki to wllh kowama ya hakura inbe karbo agun Yar gadaran ba to nima bazan cire sisi na na siyaba ehe tajuya dakinta tana cigaba da surutai .kamal ne yadubi kaninsa ,rabe wai yau waya tabo mana innar mu ne da safiyar nan haka ? hmm wllh ya Kamal inna ce yau ta dage setaci kwai kuma bata da ko kwandala kuma kasan Adda khubra bata bada bashin kwai shinefa taketa fada cewar rabe.

nikuwa bayan naji alhaji ya futa nadawo falon na zauna kusa da hajiya kaka tanata santin dankali da kwai d'in dana soya mata ,Kai hajiyata irin wannan Santi haka ?bata kulaniba har sanda tagama tas sannan ta dubeni daman sonakeyi nagama nakiraki don haka gyara zama dakyau ,magana zamuyi akan kudin da alhajinku yace zai baki me kike ganin zakiyi dashi ?kai hajiya kaka wllh nazaci wani magana me girma ne har kinsa gabana ya badi, kinci gidanku wannan ba magana megirma bane kike nufi amma dai kekam khubura Allah ya gyaramin ke.to inbanda abunki kakus Ina kikaga antaba lissafin kudi sannan mutum besan yawan kudinba ai jira zamuyi idan yakawo mukaga nawa ne se nazauna na tsara abunda nakeso nayi dasu se daga baya nayi lissafi kedai kawai mu zuba masa ido muga nawa zai bayar .kanne ido kakus tayi wai yaya naji kike cewan mujira mugani Ina cewan yanzu zai bayar yatafi dauko wane ? kakus tayi maganar tana me mikewa tsaye , gaskiya nikam inaga ba yau yake nufiba amma baridai mugani "muga wa"? kakus tafada tana me zaro ido waje ,cab din ai zama bata ganni ba, bakin daya furta shi zaisa yabamu kudinnan yau yau don bazan tsaya sanya har matansa su juya masa lissafi ya hana kudinnnan ba ,don ba k'aramar aikin subane tana karasa fucewa a falon .

Jamilu !jamilu "kana Ina "?kakus tana me keala ma baba me zuma kira.

Inna tabawa ne tajiyo muryan hajiya kaka tafuto daga dakinta tana murmushi .
"ah hajiya kaka kene tafe"? maraba.

"Ina kwana hajiya kaka"

wani kallo hajiya kaka tabi ta dashi sannan ta kauda baki tace
Amma dai kukam kun yi haddar gulma kwararo kwararo inbanda jin tsegumi dagajin nakira jamilu kinyi futttt kinfito inake Ina futowa ,waini tsayama tukum

" ko kin canza sunane bansaniba?"

"daga tabawa kin koma jamila "

Inna tabawa ta sadda Kai qasa don tarasa abun cewa.

Ina tambayarki nace kokin sake tabawa ne kika riqi Jamila?
inba gulmaba daga jin nace jamilu kinfito Salam Salam dake , dama sunanki Jamila ne sekice yayi kusan sunanki to Ina had'in tabawa da jamilu inaba gulmaba inda kuma kinason gaisheni dakinje yanda nake, to bazan amsa gaisuwarki ba juya kiyi sashinki kuma kiji dakyau gun jamilu d'ana nazo bagun jamila ba kuma kusani duk abunda kukayi ma uwar wata tofa kushirya karb'an saka mako don kun haifi mace kun haifi namiji tas se anrama ma kakus ato, sim sim inna tabawa tayi ciki, inna saratu dake labe me zatayi inba dariya ba ,tayi futttt tafito ta d'aya kofar da zai hadasu a tsakar gidan ta dubi inna tabawa tace

"jamila Ina zakije ne haka?"

inna tabawa bata kula taba domin taji haushin kwafsa mata da kakus tayi don taso jin dame hajiya kaka tazo don tasan bata xuwa sashin su haka kurin seda dalili ,tayi wucewarta tabar inna saratu tana mata dariyar mugunta.

**************

Da futar hajiya kaka na mike nacigaba da gyaran sashin ,nagama goge ko Ina se kyalli yakeyi na sauke labulaye tare da rufe kofar falon nashiga cikin gidan na dibo gaushin wuta nazo na kunna turaren wuta d'an maiduguri Wanda fatee ta aikomin dashi nantake dakin yadau qamshi me sanyi ,sannan na nufi bayi (toilet) don nayi wanka .

***************

Qamshi ! qamshi!! Nifa tsiyana dake kenan ata kiranki kina nan kina wannan wahallan lissafin to maza fito ga babban lissafi ya samu ,fitt nafito daga cikin dakina Wanda yake acikin falon,Ina ware ido naga wani lissafin hajiya kaka ke fadi,bakar laidan dake hannun ta tamikomin ,kallon miye wannan na mata Ina me bin laidar da kallo.ke banson iya shege miye hakan Ina baki abu kamar Ina baki Kashi bazaki kar6a, to kudin da alhajinku yace zai baki ne naje na karbo don ni banison jira ...ai banji karshenba na wafce laidar har sanda hajiya kaka ta furgita ta kurma salati , innalillahi khubra kinada lafiya kuwa yqnzu sakayyar dazakimin kenan ,naje na titsiye dan marayan allah na karbo miki kudin wai don karki rasa shine zaki zubar dani agefe to kidai gyara halinki nikam bazan iya mikiba inkin isheni zakibarmin sashi kikoma can gun matan ubanki suyi yanda sukeso dake .dariya nayi Ina me rungumeta wllh kakus me rabani dake se Allah kuma inbanda abunki kakus murnane tamin yawa har na rasa yanda zanyi .nasaketa da sauri nashige cikin dakina ,banwani dauki lokaci ba nafito nasake fadawa jikinta Ina murnan don Sam murmushi yakasa barin fuskata ,ina kuma kika Kai kudin cewar kakus,Kai my kakus sam ke baki jaa ,ke inbanda abunki kakus taya zamu bude kud'i irin wannan rana tsaka ,salon kiga manyan garada akanmu to nikam badaniba se dare ya raba ake lissafin irin wannan kud'in don haka ki jira se zuwa jibi zamu bude mu k'irga ,au bama daren yau za'a bude kudinba? Kakus tayi tambayar tana bud'e baki A'a ba haka nake aikina ba nifa kakus,dole ne gobe na tara yara namusu daka, sannan nayi istihara mu roki alkhairi game da abunda zamu fara da kudin .

Allah yajikan iyayenmu.

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now