💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Rashows Bature.
PAGE1️⃣4️⃣
*INA MATUKAR IN DAD'IN COMMENTS DINKU TAKO INA ACIGABA DOMIN YIN SHARHIN KU SHINE ZAI DAD'A BANI KWARIN GWUIWAN RUBUTAWA NAGODE*
Dubansu kakus tayi sannan ta gyara tsauwanta tace kukuma daga Ina zaku shigomin kanku tsaye batare da neman izinana ba sekace wasu kwartaye ?karasowa sukayi suka tsuguna mama barka da safiya amjaad da safwan suka Mika ma kakus gaisuwar su sannan amjaad yace mama tare muke da yaryar nan ita tace mushigo don mu gaisa dake safwan ya d'ago yana kallon abokin nashi da mamakin karyan da yayi ,au tare kuke shine dan sakarci tayi wuce warta ciki kamar wacce aka biyo oh waini ko yaushe qamshi zakibar halinki nakin kula samari ne , amjaad ne ya tab'e baki to yarannnan kwa tsaya daganan kushiga daga cikin falon mana ai bakwa zauna daga wajeba a'a mama daman gaisheki zamuyi wataran zamuzo mu miki hira cewar safwan aiko baza'ayi hakaba maza ku shigo duk da bansan daga Ina kukeba ai kwad'an wuta maza ku shigo ciki mikewa sukayi suka cire takalman su sukabi bayanta daga shigansu wani sanyin ac ne da daddad'an kamshi ne yamishi marhabun kujera hajiya kaka ta nuna musu tana me zama tace bisimillah ku zauna bari akawo muku abun tab'awa bakomai mama mun gode cewar safwan da ido amjaad yabi falon da kallo duk da bawani kaya masu tsada bane a folon amma se tsarin falon ya furgeshi don kujerune masu karamin karfi se gefe tv ne plasma me girman 32 inches atsakiyar falon kuma dadduma ne shimfid'e se table akan dagacan gefe dinning table ne shima samansa an shimfid'a farin kyalle an gogeshi se d'aukar ido yakeyi akusa dashi anyi wani durowa kamar kwaba gabansa na glass an jera plate aciki da cups se wani abu shikuma an zuba spoons aciki shima a goge yake tas ko Ina ka kalla a falon fes yake ba kura , sunkuyar da Kai yayi yana taba wayar hannunshi safwan ne ya dubi kakus yace gaskiya mama kina hutawa abunki kiji sanyi me dadi kamar karna futa rana waje kuwa kamar mutum yayi yaya don zafi ,hmmm kaidai bari d'annan ana zafi kam kwana biyu da alama ruwa ya futa ko yana Shirin yimana bankwana gaskiya kam inji safwan ta juya tana kallon kitchen bata hango khubra ba tace ikon Allah kardai qamshi bata futo bane har yanzu ta barku baki bushe , khubra! khubra wai me kikeyi aciki ne dakika kasa futowa har yanzu shiru taji tasake daga murya qamshi qamshi wai baki jinane kokuma halinkinne ya motsa ?
mikewa nayi daga kwancen danake donjin Kiran kakus yayi yawa na nufo kofar Ina me cewa Kai kakus waini wani irin kirane haka fisabilillahi waishin bakisan yawan Kira nasa tsufa bane to agaskiya ni bantashi tsufa yanzuba seki bari nima naci nawa zamanin na fad'a Ina me k'arasa futowa falon dukansu ido naga sun zubamin wani kunya ne ya kamani don kayan dayake jikina wata yar top ce se gajeran wando wanda iyakacinta gwuiwata don shine ajikina daman Sena sanya dogon hijab me hanu wanda yajemun han k'asa shiyasa na futa haka kuma nayi la'akari da acikin gidane kuma ba jimawa zanyi ba, dabur cewa nayi Ina me son juyawa naji kakus tace Ina kuma zakije kizo kibasu ruwa da abun motsa baki shine zaki juya toni hajiya kaka ahaka kikeson neje d'auko musu ruwan wai ?nayi maganar Ina me bubbuga k'afana ak'asa sannna na juya ciki ikon Allah da wani munafikin ne yace ki futo haka kajimin yarinya futowa nayi da himar din dazu na wuce kitchen na d'auko musu coca cola guda biyu se dambun kakus datayi ta boye a kitchen din na jera akan ture me girma na kawo musu akan table na ajiye musu zan juya naji muryanshi yace mama bata zuba manaba zata wuce yayi maganar kamar bashi yayiba ,harara na bisu dashi Ina me tsine masa a zuciyana yi nayi kamar ban jishiba kakus tace au bazaki zuba musunba kuwa juyowa nayi Ina turo d'an karamin bakina safwan ne yane barshima abunki qamshi zan zuba mana yayi maganar yana bud'e goran coca cola yana zubawa a cup ,zan tafi tace wai Ina zakije ne ga baki kinyi shine zaki wuce
" wa "
nikam ba gurina suka zoba kedai dasukazo gunki sekiyita zuba amma karki sanyoni aciki nayi wucewa ta ciki Ina me jin takaicin dan iskannnan don har ga Allah yanzu tsoro yake bani bani kaunar wani abunda zai had'a mu .bayan wuce wata safwan ya dubi kakus yace mama amma wannan jikarki ce tace kwarai duk cikin jikokina babu kamarta domin khubra takasance marainiya mahaifiyar ta mutuniyar kirkice wajen haihuwar qamshi ta rasu shine aka mayar mata da sunan mahaifiyar ta duk kayan dakake gani acikin sashinnan kaf dinsu khubra ita tasanya mun harta abun dumama ruwan zafi ta sayamun don batason nake amfani da ruwan sanyi Sena dumi duk kuma da kudin sana'ar ta takeyin komai bata dogara da kud'in mahaifintaba babu abunda zance mata sedai namata fatan samun miji nagari Wanda zai rikemun Yar marainiyata ya tallafi maraicinta to amma taki basu fuska duk Wanda yafuto yazo da niyar zance to in sha Allah da k'afarsa zai gudu don bama zata kulashiba inkuma yaci sa'a tafuta tofa sedai shi yayi hiran don kanzil bqzatace masa ba .
Ikon Allah cewar safwan mama lokacine beyiba in yayi zakiga kamar hakan be faruba allah yasa d'annan to kuci naman karkura ya hau kai , dambun safwan ya diba yakai baki ya tauna tare da lumshe ido don dad'i hajiya kaka ta dubi amjaad tace Kai banga kana shan komaiba yace ni kaka kunun aya zansha ba wannan ba kakus tace kaci sa'a akwai kuwa barin kawo maka don wancan tunda tashiga to futowanta se anyi da gaske don yanzu haka tanacan tana lissafinta dabaya karewa donga ranar da khubra zata wuta da wannan lissafi ta shiga kitchen ta d'auko masa ta dawo karba yayi cikin girmamawa yace na gode kaka bakomai kaidai kuci dambun ba dadi abar abu haryayi sanyi ta dubi safwan tace kaima ga kunun aya na kawoma duk kusha yace to kaka mungode .shiru falon yayi amjaad se shan kunun ayar sa yakeyi ahankali don yayi mashi dadi sosai ya lumshe ido Kai kaka wannan kunun aya akwai dad'i wannan in mutum ya samu ai kullum se nasha , to me zai hana ai kullum qamshi tanayi na sayar wanta ne, kaka kice dai tana sayarda abubuwa , sosai ai bata zauna ba kaga tana sayarda kwai don shine babban kasuwancinta se take had'awa da zob'o,dataga ana neman kunun aya seta farayi dashi tana sayarda katin waya ga abincin sayarwa duk tanayi sannan tana koyarda manyan mata ,Kai Kai lallai ashe kaka kinada babbar Yar kasuwa atare dake shiyasa kaka kukejin dadinku shiyasa kaji nace maka Ina alfahari da ita don tazama jaruma don duk yaran cikin gidan gona itake ciyar dasu tana biyansu kuma albashi harta yayunta guda biyu duk a karkashin ta suke tunda su sunki kulawa da neman na kansu insunyi hankali sesu nemi nakansu.....bata Kai karshen maganrtaba taji sallamar baba me zuma amsa masa sukayi ya shigo falon tareda su ya jamal abayanshi zama yayi a kan kujera yana me dubansu amjaad tareda mamakin meya kawo yaron alhaji majeed har cikin gidansa ,zamowa daga kujera su amjaad da safwan sukayi suna me gayar da baba me zuma ya amsa cikin kulawa yace yaya alhaji ya kwan biyu bai shigo garin namuba ey wllh baya samun lokaci ne yanzu aiyuka sunyi yawa ,Allah sarki ai se ahankali baran ma su dasuke da jama'a to allah yayi taimako sukace amiin dukansu.hajiya ne ta dubi baba me zuma tace ashe kasansu yace ey wancan yaron alhaji majeed arab ne shikuma wannan abokin sa don yawanci tare suke zuwa garinnan allahu Akbar kace Ina tare da yaron mutumin kirki babu abunda zamuce masa saidai Allah yasa yagama da duniya lpia halinsa nagari yabishi ashe aikine yayi masa yawa shiyasa bamujinsa harta kayan sallan dayake mana sallah biyu kenan bai manaba Allah ya sassauta masa wannan aiki don wasu da dama sun shiga wani hali agarinnan don yasaba raba mana buhun shinkafa wannan madai daitan zakaga anbi gida gida ana rabawa tareda suga kowa mudu biyar daga baya kuma kafun sallah se azo ararraba mana zannuwa nikam da nace hala yana aikowa da kayan masu rabon ne suka ruke don ba halinsa bane rowa Allah dai ya Kara masa arzik'i da lafiya duk akace amin ,sannan ta dubi su kamal tace kukuma lpia naganku anan Ina aikinku kuka bari kukazo nan ? gyaran murya baba me zuma yayi yace abumda yake tafe dani kenan ganinki da baki kuma yasani shiga wani zancen 'yarki ce ta koresu tabasu hutun sati biyu shine sukaje suka gayamin akan nazo na bata hakuri su koma bakin aikinsu to ai tunda kaga haka wani abun suka mata don haka kurum khubra bazata koresu ba kudai kuji tsoron Allah kuyi koyi da kanwarku kowannenku ya nemu abun dogaro da kansa ku yanzu bakujin kunya ace a karkashin kanwarku kuke aiki duk da ba abun kunya bane amma ai zaisa kuji kwarin gwuiwan neman nakanku kuma dolefa sekun jure don kudi bazasu zo muku kuna kwance ba dole se kun jajurce nidai babu ruwana awannan magana bazan mata shishshigi da lamuranta ba ita tasna wahalan datashi harta kawo haka don haka seku jira duk hukuncin data yanke akanku.
Baba me zuma ne yace" yanzu Ina ita khubra take? don na leka gonar bata can akace tashigo gida tana d'a kinta, Kai jamal tashi kaje ka kwankwasa bawai ka shige mata d'aki ba ,Ina kwance don har nafara barci naji ana buga k'ofar d'akin nayi mamaki don nasan kakus bata kwankwasawa sedai ta shigo na tashi na d'auki hijab na Sanya na bud'e dakin ganin ya jamal ne yasani karasa futowa yace "kizo inji alhaji !na dubi falon sannan na karaso gurinsu na zauna a k'asa kusa da k'afafuwar alhajin mu nace "alhaji barka da rana! yace" yau khubra gani a gabanki a matsayin ubansu jamal na biyo jin ba'asin abunda sukayi ne har aka basu hutun sati biyu ,nasunkuyar da kaina cikin sanyi da kuma alamar barci a tare dani nace "alhaji ba haka bane daman samun su nayi da karyamin dokan gidan gona, kuma sun san cewan duk Wanda ya karya doka babu ruwan sana'a da kusancinmu da mutum kuma a bunda sukayi ganganci sukamin suna neman janyomin a sara ne ,dubana alhaji yayi yace wani irin asara kuma? ey asara zance domin barin kajin sukayi basu basu abincin dare ba suka barsu ba ruwa ba abinci se kuka sukeyi har zuwa k'arfe uku na dare, har nazo na basu abincin babu Wanda yasani yanzu koda sace kajin akazoyi ai har za'a kwashe duka a bufuta dasu basu saniba, suna can suna barcinsu shine naga basu shirya ma aikin ba nace suje su huta in sun shirya sesu dawo kuma kowa yazo da mahaifinsa don asake sabon karanta musu dokoki .
kada kai bqba me zuma yayi yace tanan nima Ina bayanki bazan baki hakuri ba sedai zanso ki duba lamarin tunda har suka je suka gayamin laifinsu sannan kuma suka rokeni danazo na baki hakuri to inason ki sake basu dama in akasamu akasin hakan to ni bana cikin maganar seki yanke duk abunda kikaga dama amma wannan karon Ina me neman amusu afwa shiru nayi har Kamal yace don Allah kiyi hakuri zamu kula dubansa nayi nace na hakura na janye Amma senanda kwana uku zaku dawo bakin aiki dan Allah addan yara kiyi hakuri inji jamal nace na gama magana inbe mukuba zaku iya ajiye aikin , a'a wllh yayi mun gode sukace , babà me zuma yace to angode qamshin hajiya se a dada hakuri Allah yamuku albarka mukace amiin sannan suka tashi suka futa nima komawa d'akina nayi .Rashows ce
07052100719
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Fiksi UmumLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...