Chapter 46

435 42 0
                                        

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍🏻 Real Rashida Bature

*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION* 

'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''

Wattpad https://my.w.tt/zq9Wot0H9bb

PAGE4️⃣5️⃣

Wani irin k'ugi cikin rumana yayi tare da k'ullewa ba shiri ta garzaya toilet don rage cikin ta daya dame ta da murd'a wa.

tana zaune akan toilet tana rusa kuka,senator nazir da jamcy ,aminiyar ta da duk duniya bata da kamar ta inka d'auke iyayenta, sannan ga aminin mahaifin ta Wanda duk duniya babu Wanda ya aminta dashi ,shine mutum na farko da yafara lalata ta,tun tana 'yar 13 yrs yake lalata da ita kuma duk duniya babu mutumin da mahaifin ta ya amince dashi sama da sanata nazir .

"Kai impossible ba gaskiya bane hakan sam bazai faruba , tabbas in ya kasance gaskiya to ya tabbata nima inada cutar HIV makar yanda aka nuna maganin dasuke amfani dashi a tv,kuka ne yaci k'arfin ta tare da wani irin tsoro , mik'ewa tayi batare da tayi tsarki ba ta nufi k'ofar futa ,harta murd'a handle d'in k'ofar ta tuna batayi tsarkin kashin datayi ba ta juyo tayi sama - sama bawai don ya futa ba don damuwar dayake tattare da ita bazai bari ta gane wani irin tsarki tayi ba.

"waini son baka ga me muka gani bane ? naga Kai ko ajikin ka.

"na gani mom " ni nawa meye aciki shida yayi abu daban senine zan sa wa kaina damuwar wani , lokacin dayayi ai inda zakace yaji tsoron Allah karya aikata , to alokacin sawa zaiyi a kame masa mutum don haka banda wani abun cewa sedai nace Allah shi kyauta ya tsare mana imanin mu ya shiryemu .

"amiin shiyasa nake alfahari dakai cewar hajiya.ai GA IRIN TA NAN,sukanyi abune  tare da mantawa da Allah yana kallon su kuma yayi musu talala ne basu sani ba ,gashi Allah ya toni asirin su duniya ta ga duk abunda sukeyi.

mik'ewa nayi don tashi daga gurin da amjaad ya matseni kan dinning table na zauna don cin d'an waken da mom tamin duk sona dashi da wannan abun ya faru gaba d'aya jinayi ya futamin akai don ko mom tayi min bani ko kallah sedai nasha kunun tsamiya don shine kawai a lokacin zai iya shiga cikina, amma yanzu da yake amjaad ya gayamin komai normal duk da baimin cikakken bayani ba na gamsu da maganar sa don naga zallan iya gaskiyar shi ya fad'a min a kwayar idon sa.

yaji na bad'a sosai seda d'an waken yayi ja hannu nasa na gauraya tare da d'aukar guda d'aya nayi bisimillah nasa a bakina Ina me lumshe ido har seda na had'iye sannan na bud'e don d'aukar wani,caraf idan mu suka sark'e dana juna  ,kauda Kaina nayi na d'auki wani nakai bakina ban karasa kaiwa ba naji hannun amjaad anawa ya rik'e tamau.

"mom please zokiga a bunda khubra takeyi .

dasauri mom da hajiya suka k'araso gurin tana duban mu don ba taga  abunda yace tazo tagani ba.

"Ina abunda zan ganin son?

"Gashi nan mom agaban ta ya nuna da baki.

buge hannunshi mom tayi "miye zaka rik'e mata hannu salon abincin ya futa daga ranta ne ko me?

"mom baki ganin me tayine zakice haka? salon taja ma kanta ulcer.

"na gani itama bayin kanta bane lalura ne yasa ta cin yajin kekuma daughter ki rage sawa don gudun matsala.

"ya kamata akira likita don aduba ta ramar da tayi yayi yawa se muji inda abunda za'a iya mata inkuma ita irin nata laluran kenan shike nan mudai mu tabbatar da  lafiya suke cewar hajiya tare da barin gurin ta koma falo ta zauna.

Sororo amjaad yayi don shi Sam bai gane Ina maganar su ta nufa ba ,amma bari ya zuba musu ido har likitan yazo don ji daga gareshi .

waya rumana taketa ta bugawa ma layin jamcy gashi dai wayar tana ringing amma ba'a d'agawa ,takira yafi sau talatin hakan na nuna mata cewa tabbas da gaske ne a bunda tagani ,layin sanata nazir takira shima ba'a d'aga ba bata hakura ba tacigaba da Kiran layinsa   ko zai d'aga d'in.

a b'angaren sanata nazir in hankalin shi ya zamma dubu to gaba d'aya sun tashi,ya rasa ta Ina a kasamu wannan hotunan da aka baza a kowani social media,ga gidan tv da radio se baza labarai akeyi ga masu Kiran shi da suka addabe Shi,shi duk tsoron sa da tashin hankalinin sa irin hukuncin da megirma shugaban k'asa zai yanke masa ,shin da gaske ne tana dauke da cutar HIV?don shi Sam bai taba amfani da condom ba don bai taba kawo makansa wannan cutar ba.

d'aya daga cikin wayoyin  shi ne tayi k'ara ya dauka bai jira Wanda ya bugo wayar yayi magana ba cikin zakuwa yace "kun samomin shegiyar?

"a'a yallabai munata bunciken yanda take ne ,yanzu naje naba da number ta dai don amana tracing dinta kuma in sha Allahu za'a ganta ka kwantar da hankalinka megida .

wani uban tsaki yaja tare da buga wayar a kan kujeran da yake "na rantse inna kamaki bazan raga miki ba jamcy,ni zaki jama matsala ?zakisan ni kika tozarta bagidajiya kawai wacce bata waye ba ,ita rumanan daya ke wayayyi yane shekara nawa muna tare babu Wanda yasani harta maihaifinta daya kasance amini na bamu bari ya fuskanci muna mu'amula da juna ba se ke mtsss yaja katuwar tsaki tare da share gumin daya ke tsastsafo masa , kallon wayar da rumana take ta Kira yayi yaja tsaki don ya rasa dame zaiji ga  matan shi suma se bugo mishi waya sukeyi babu ma wacce ya d'aga kiran ta,da karar wayar ta dameshi ma janyo wayar yayi ya kashe ta gaba d'aya ya tashi yana zagaye d'akin.

wani irin kuka rumana takeyi me ban tausayi tare da wani irin nadama ne yake shigan ta ,wannan wani irin cin amana ne ?ashe wanda ka yarda dashi zai iya muna funtar ka abayan idon ka har ma ya ha'ince ka ? shin haka dama duniya ta zama ?
oh duniya abun tsoro..

RASHOWS

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now