💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍️ Real Rashida Bature
PAGE1️⃣8️⃣
Rumana ne zaune agaban maihaifinta kanta akan cinyar mahaifin tana kukan shagwaba, dady kamin alkawari zakama babanshi magana Amma ka saba alkawari, wallahi dady Ina son shi sosai inbaka bani shiba zan iya rasa rayuwa ta .
Dubanta maifin nata yayi yana shafa kanta tareda cewa ,nagaya miki banison wannan damuwan dakikeyi ki kaddara tamkar kin samu yaron nan ne don munruga mun gama magana da mahaifin yaron ni yake jira na Sanya musu rana suzo su samen ,dayake ban cika zamaba sabida yawan aiyuka, to amma tunda haka ne yanzu abunda za'ayi in sunzo neman aurenkin zance subada sadaki inyaso se kawai nasanya rana .
Yauwa my dad shiyasa nake bala'in sonka nidai dady karka Sanya ranar dayawa kawai kasa musu 1 week ma ya isa .
"A'a baza'ayi hakaba inmu mun shirya su bamu saniba ko ba'a shirye sukeba ,don haka zandai basu daman su fad'i lokacin da sukeso .
To shikenan dady inkamin haka inaga nafi kowa sa'a aduniyar nan . thank you my dady ta juya tana duban maifiyarta ,momy kitayani murna dady zai cikamin burina .
Mumy tayi murmushi don aduniya tana kaunar ganin yar tilon yarsu cikin farin ciki tace inbanda abunki menene a duniyar nan zai gagaremu mu mallaka miki matukar muna da iko akan sa, oya tawo guna ,tunda ma kince kun dai dai ta kanku to me zamu jira gara a aurar dake kawai musha biki ,Kai mumy harnaji kunya tana rufe fuska .
Alhaji majeed arab ne zaune a katafaren falonsa yana kallon tashan TRT WOLD yana kallon labarai k'ofar falon aka bud'e tare da sallama amsawa yayi tareda duban me sallama yace a'a amjaad harka dawo ne daga gidan su safwan din?
Ey abba tunda ka kirani kace kana nemana nace barin dawo kawai naji Kiran .
Dafatan ban katse muku abunda kukeyiba ?daman na gaya maka ne akan Inka dawo ka shigo gida semuyi maganar amma tunda ka dawo shikenan .
abba ai daman futan bawani abun damuwa bane inyaso semuje ko bayauba ne .
"to shikenan allah yayi muku albarka.
"Amiin abba"
duban dan nasa yayi yace ba wani sabon abu bane se akan maganar dana fara gayama ranar ,gameda yarinyar wajan matemakin governor jiya yazo da kansa har office yasamen da maganar akan inda gaske kakeyi mu turo ayi maganar aurenku don bayason abun yadauki tsawon lokaci , to dayake bamuyi maganar dakaiba se nabashi hakuri da sanar masa in sha Allah a week dinnan yan uwana zasuzo neman auren to yanzu inason jin ta bakinka a Ina maganar ta kwana don banson se an gama magana daga baya wani abun ya b'ullo .
"Kai amjaad ya sunkuyar tareda cewa amma nifa abba ban taba jin inason yarinyar nan ba itace take bibiya ta , to inbanda abunka amjaad aikai sekayi murna matar da zaka aura soyayyar ta tafi naka kaga zaka samu zaman lpia agidanka ,da akan kaje ka d'auko wacce kaine kake kauna kazo ka kasa lankwasa ta don tana da tabbaccin bazaka iya rabuwa da ita ba kaga itace zata juya ka yanda takeso ,kuma ni naga wannan yarinyar tana da hankali ga girmama mutane Sam batada damuwa da fatan zaka amince da zabin dana maka .
Wani zufa ne yashiga tsastsafo masa dukda ac dake aiki a falon amma bai hana amjaad yin zufaba wani irin daci yakeji kirjinsa yakeyi ,duban mahaifin nashi yayi yace abba bani da ikon butulce ma zabinka koda kuwa yana nufin salwantar da raina ne sadai sam abba bani sonta zan karbi duk abunda ka bani hannu bibbiyu nagode da wannan zabin dakamin Allah ya tabbatar da alkhairi.
amiin Allah yamaka albarka yasa yayanka suma suji kanka Amiin abba ,zaka iya tafiya ." futowa yayi rike da kansa don gaba d'aya kan jinsa yakeyi kamar ba'a jikinsaba don yayi mashi nauyi ga wani jiri dayake dibansa haka ya daddafa bango har ya isa bangarensa ya kullo kofar.
Rashows ce.

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
General FictionLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...