💍💍CIKAKKIYAR MACE💍💍
PAGE1️⃣
Rashida bature.
ALHAMDULILLAH .
Khubra!khubra!!waini shin khubra bata gidannan ne naketa faman kiranki kina jina?
" Kai kakus wllh Allah kincika Kira kamar wata tsohuwar makauniya ".
khubra ta fad'a daga cikin d'akin taname turo d'an karamin bakinta,tashi tayi harta Kai k'ofa ta dawo tareda boye dan kudin hannunta datake kirgawa,sannan tafito falo.,
"to hajiya kaka gani nafito mezanmiki "?dattijuwan ta daga ido tana me duban khubra Wanda ta hade fuska ,kama baki tayi tana me fadin oh ni Abu! yanzu khubra akan Kiran danake Miki ne shine kike ta faman 6ata fuska Wanda nasan babu abunda kike tsinanawa acikin dakin inbanda lissafin karya d..karyafa kikace ?kubra ta katse hajiya kaka batare data karasa maganar ta ba,yanzu lissafin kudaden sarin nawane hajiya kaka zakice karya? lallai hajiya kaka kinason nadakatar da duk wata hidimar danakeyi agidannan ,inbanda abunki kakus sokikeyi nadauki kudin nakaima masu abincin kaji bankirgaba salon nabasu yayi yawa.sororo kakus tayi tana kallon kubra,yanzu kubra dubu ukun ne kiketa wannan kirgawa kusan rabin awa kina abu daya?
Hmm kakus kenan !kefa bazaki gane ba,tunda dayake bake kike sayan komaiba ai bazakisan Yaya duniyar take cikiba ,shin kinkuwa san nawane kudin mudun shinkafa yanzu kuwa? to kakus gara kifarka daga nannauyan barcin dakikeyi don yanzu watan tattaline yakama ,donni naga amfanin kirgawan danayi gashi dana sake qirgawan nasamu naira biyar ya haukan kudin
to nidai abunda zan gayamiki don Allah kaka inkinga Ina lissafi kiringa barina nagama karki rudani.Yanzuma ki gayamin Kiran mekikemin don nabar kudina afili gara naje na adanashi .,mtssss inkin gama fitsarar seki futa kibasu kwai inkuma sun gaji dajiranki suntafi to kinyima kanki don muryan isiya me shago najiy...kubra batajira kaka ta k'arasaba tafita tana mecewa agaskiya kaka kibar haka wllh yanzu daman arziki ne yazomin har gida fisabilillahi Amma seki rikeni da maganar dabazai amfaneni da komaiba .
tana futowa tsakar gidan yayi daidai dasake sallamar isiya me shago, wa'alaikassalam dan jirani ganinan zuwa cewar khubra sannan ta juya cikin dakinsu ta dauko hijab dinta dayasha guga sannan tafesheshi da turare tafito tanufi kofar gidansu,
Isiya me shago yana ganinta ya washe baki don tsakanin sa da allah shi kaunar khubra yakeyi, Allah yataimaki hajiya kubra qamshin duniya kinatafe qamshi nabinki, khubra tadan murmusa tana basarwa don arayuwa tanason qamshi ,tana kumason intasa tatawo guri asan lallai taci sunanta khubra qamshi, isiya create nawa zanbaka ? Qamshi ta fada tana me duban isiya, uku ma yayi ,ayya ammafa isiya sedai nabaka biyu da rabi don baicika ukun dakakeso ba, sedai zuwa anjima idan kajina sunyi kwai din Sena turo maka dashi cewar khubra,ah haba ai wannan ba matsala bane ,zan iya zuwama dakaina nakarba basekin aikoba qamshin duniya.To ammafa yanzu isiya kudin yakaru yakoma 950.don masu abincin sun kara kudi ,ikon Allah to allah yasa mudace akawomin haka ai ko dubu kikace zansaya allah dai yakaro yawan qamshi ameen tafurta tareda shiga gida domin kawo masa kwai.
Aikin banza haka dai za'a kare abula turare babu mashinshini cewar inna tabawa,
kekuma dawan? inna saratu ta tambaya dawa kikaga maganata tayi kama? inba wancan mekama da Karan rakenba mesuna (takand'a )hmmm kedai bari kawai tabawa samun waje tayi shiyasa bata ganin kowa damutumci ita mekudi asannu zanyi maganinta kuma haka zatata zama ita da sana'ar badai tayi gababa fitsararriya kawai inna tabawa tafada tare da wurga ma khubra harara Wanda batamasan sunayiba don hankalinta yayi nisa a jera kwai dinta se nishadinta takeyi don ita Inka ga tana nishadi to anzo sayan kayan sana'ar tane don sam bata da lokacin su inna saratu takance basuda abunyine shiyasa suke wahal dakansu atunanin wani.
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Ficción GeneralLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...