*💫⭐SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION⭐💫*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
PAGE3️⃣3️⃣
RUMANA
ado taci bakinnan yasha jan baki se kyalli yakeyi ga kannan yasha Karin gashin kanti tana sanye da wata d'ammmiyar doguwar riga Wanda yafuto mata da shafaffen k'ijinta sekace me k'irgen dangi ga d'uwawun nan a shafe se taunar cumgum takeyi tana k'as k'as dashi yanda kasan tsohuwar kilaki ,zama tayi a d'aya daga cikin kujerun falon ta d'auki remote takai tashan one hd ta samu kuwa sun sake wak'ok'in su na bad'ala zama tagyara tana kallo ta k'ure volume d'in,karar volume d'inne ya farkar damu daga barci da mukeyi , mamaki amjaad yakeyi na wannan irin karar volume ya sauko daga kan gadon yanufi main falon don ganin meke faruwa .direct socket din ya nufa ya kashe tareda juyowa da dawani irin kallo Wanda yasata fad'uwar gaba amma dayake ta kware a duniya seta dake tareda cewa ya haka Ina kallo zakazo ka kashemin ?
kaucewa yayi yace to ko zakizo ki kunnane?
shiru tayi batare da tasake cewa komaiba sedai harare hararen datakeyi tana k'as k'as da cumgum din bakinta don duk iskancinta tana shakkarsa ,yace wannan yazama na k'arshe da zakizo ki kunnamin kid'a a gida ban hanaki kallon kid'aba amma in har zakiyi kishiga falonki shima karki sake karar shi yawuce falonki inba hakaba zan sab'a Miki matuka ,inbanda rashin tunaninki idan wani yazo ya iske ki kina wannan kalon fa me zaiyi tunani ?
ok kana nufin nikenan bazan Shana a gidan mijina ba kenan saboda wasu to wallahi Babu me hanani walawa yanda nakeso ciki kuwa harda Kai , kid'a kuwa yanzu na fara kunnawa babu me canzamin tsari ehe ta karasa maganar taname watsa mishi wani irin kallo.
Kai ya gyad'a yàce to bisimillah naga rashin kunyar taki.tashi tayi tana rangaji tanufi d'akin ta nata hura cumgum din bakinta, kwafa yayi ya nufi dakinshi .bathroom na nufa bayan futan amjaad naje na had'a ruwa me zafi nashiga ciki kafun nayi wanka nagama na futo yanzu kam naji dad'in jikina sosai bakamar yanda naji dana tashi da asuba ba , ahankali na shirya na sanya wani dogon riga don samun sakewa aciki ,na gyara d'akin na kunna burner Kamshi ya gauraye d'akin na koma falo dukda ba abunda yayi amma haka na dad'a kakkad'ewa shima na kunna turaren wuta amma ba irin Wanda na Sanya a bedroom ba wani kalan daban na Sanya , kitchen din dayake cikin falon na shiga Ina kallon yanda ya tsaru agaskiya mahaifina yayi kokari ba kadanba domin komai da akesawa wa Yar gata ansayamin bubbud'e abubuwan nakeyi don ganin menene nake dashi wanda zan iya girka mana Ina cikin haka naji an rungumoni ta baya ajiyàr zuciya na sauke yace matsoraciya ninefa yana me gogamin fuskarshi a wuyana tareda cewa me kikeyi a kitchen haka?
shiru nayi tareda saukar da kaina k'asa,baibar abunda yakeyi ba yàce muje falo ga abun breakfast can ankawo muje muci don yunwa nakeji duk kin kwakwulemin ciki jiya ,buge hannunshi nayi taredayin gaba , dariya yayi yace ai gaskiya ne duk kin sanyamin yunwa don haka a rarrasheni konayi bori,banza namishi na zauna akan kujeran falon yace wato sarauta yau akeji dashi magana ma wuyar yinta akeyi kamar yanda tafiyarma dakyar akeyita , gaskiya Yan matana kinban wuya jiya ba kad'an ba ,rasa me zance masa nayi ganin yana rainamin hakankali kawai nasanya kuka ,dariya ya fashe dashi yace oh baby kina da shagwaba yanzu miye abun kuka anan ai gaskiya ne kicefa kikasani jin yunwar kuma kice karna fad'a to naji na d'auki laifin yi hakuri ya janyoni jikinshi yana shinshinani tureshi nayi don har yanzu tsoronshi nakeji gani nakeyi kamar zai kara yine ,mikewa yayi yanufi kan dinning ya zuzzuba mana Chip's din da farfesun kaza se kunun gyada ya dawo mana dasu tsakiyar falon ya dawo guna ya durkusa ya kama gwuiwata yana karemin kallo kauda kaina nayi gefe don bazan iya kallonshi ido cikin ido ba ga wani irin kunyarshi danakeji idan na tuna abunda yafaru jiya da irin ihu da gurnanin daya ringa sakewa jiya amma yanzu kaganshi kamar bashiba ,yace amin afwa rayuwata kallonshi nayi jin sunan daya kirani dashi yace nasan nayi laifi amma ayi hakuri bazan kara saki jin zafiba ahankali zanyi , agaskiya kin shayardani zuman daban taba jin irin zak'inta ba na jinjina ma iyayenki gurin tarbiyan dasuka baki na Kare mutumciki har ya zuwa gidan aurenki kika damka ma mijinki ,hakan ba kàramin k'aramiki martaba da kima yayi agurina ba naji dad'in hakan allàh yayi maki albarka yabamu zuri'a d'ayyiba nasan ba lallai bane yanzu ki yarda da abunda zance ,amma kisani ni amjaad na dad'e Ina kaunarki tun ganinki na farko danayi a company na kina rike da wayarki kina danna wa to tun lokacin kike azabtar da ruhina kin hanani sakat danaji ke hajiya tanema min aurenki wallahi har rawa sanda nayi ni,inaso ki watsar da komai mu gina sabuwar rayuwar aure me tsafta ni mutumne me son a ringa kula dani ,ake shagwaba ni don haka seki zage don naga alamar abun ze juya amemakon ni a shagwabanin inaga nine zan shagwaba wata yana me kashemin ido d'aya ,bakina turo mai ,banyi auneba naji bakinshi akan nawa sanda yagama tsotse man bakin dana shafa sannan ya sakeni yana me duba kayanshi yace kinga harzaki b'atamin kaya kin fara yamutsamin nace ka yamutsa abunka dai , table din tsakiyar falon ya janyo ya zauna kusa dani har munajin numfashin juna ya d'ibi Chip's din ya sanyamin abaki banso haka na tauna inajinsa kamar magani don Sam banijin dad'in bakina haka yata turamin yana bani kunun ,banwani ci dayaba nace na koshi bai takuraniba ya barni yace shima Sena bashi ,haka na daure na ringa bashi yaci sosai shikam tareda Shan kunun sannnan yace ya koshi na tattara gurin nakai kitchen na wankewa na wanke kafun na futo na sameshi ya mike ya kamo hannuna yace muje kisamu ki wuta don haryanzu akwai gajiya atare dake ban mishi musuba don kwanciyar nake buk'ata muka nufi cikin bedroom ya zaunar dani abakin gado ya gyaramin fillow tareda kwantar dani ya namin tausa Ina lumshe ido har barci yayi gaba dani,ya gyaramin mayafin ya rufeni ya mannamin kiss a goshina ,ya kashemin wutar d'akin tare da jamin koba ya futa cikin gidansu ya nufa don gaida iyayenshi .

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
BeletrieLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...