chapter 9

700 77 2
                                        

💍 CIKAKKIYAR MACE💍

   ✍️Real Rashida Bature.
                      ...

                      
PAGE8️⃣
Amjaad ne tafe cikin takunsa na izza da isa ya nufo motar sa domin yatashi daga aikin yau sekuma na gobe in Allah yakai yawan rai .
futo da dukkan idon sa yayi waje tare da tsayawa cak a inda yake ya dau tsawon minti biyar yana al ajabin motar sa yana jinjina karfin halin duk Wanda yayi masa wannan b'arnar .iska ya fesar me d'umi ransa yayi mugun baci wayar sa ya ciro a aljiwu ya kanga akunnensa can naji yace

"sakko k'asa kasamen"

iya abunda ya fad'a kenan ya katse Kiran . ba'a dauki lokaciba naga wannan mutumin wato safwan wanda ya tuko motar ya futo ya nufo gurin gayen da yayi wayar, amjaad lpia wannan Kiran gaggawan ,mtsss tsaki gayen da aka kira da amjaad yayi ya bud'e baki dakyar yace wllh kacika matsala se zuba kakeyi kamar aku,matsawa yayi tare da nuna motar sa da hannu futo da ido shima yayi waje yana me duban abokin nashi ban ganeba motar takace akama haka? kokuwa kaikace amayar maka haka? mtsss tsaki yakuma ja sannan ya dubeshi kamar zaiyi magana sekuma ya fasa domin wani tukuki yakejin zuciyar sa tanayi ,yama rasa me zaice waye zai cire masa tayoyin mota ?yanisa yace to kodai security bai fahimci wata motar nace suyima aiki bane ?lallai inya tabbata hakane kuwa tabbas Sena koresa a aiki dama duk Wanda yayi aikin duk acikin zuciyar sa yake wannan tunanin rai bace yanufi gurin security kafin ya karasa security ya tawo dasauri don yaga tawo warsa ya rusuna yana me cewa barka da fitowa ranka shi dade wani abun kake bukata?shiru amjaad yayi yana ciza hakoransa ya nisa ammm nikam wata mota nace ayima aiki ne? yayi tambayar ahankali kamar bashi ba,ranka shi dade motar wannan dire banne Wanda yake tare da yarinya farar nan masu akayi ma aiki , lumsassun idon sa ya zuba ma security na tsawon wasu lokaci kafin yace follow me,suka isa gun motar har lokacin dayan abokin nasa yana gurin matsawa yayi gefe security yaga motar atake yazube guiwowinsa akasa yana me rantsuwa wllh Allah sir agabana akayi aikinnan kuma ma motar su aka ciccire tayoyin aka futa da motar waje,bayan futar sune da kamar awa daya da rabi sekuma naga ta dawo ita da wani tace kaga na dawo nayi mantuwa ne suka shige wllh allah bansan aika aikan da zatayi kenan ba ,kuma Ina tsaye suka zo suka futa batare da taya ko wani abu ba ta futa ,yadubi d'ayan abokin yace don allah oga safwan ka d'ad'a fahimtar da oga Allah bansan waya aikataba yana maganar kamar zai kurma ihu ga zufa ya had'a tako Ina .hanu dayan abokin da aka kira da safwan d'in ya d'aga yace zaka iya tafiya ,bayan ya wuce ne ya dubi abokin nasa yana me kada kai yace Masha Allah nagode ma duk Wanda ya aikata haka  
   
          "dara taci gida"

kasa ama wasu sekuma yajuye akanka ka had'u da dai dai kai ni wllh dazanga Wanda yayi haka har kyauta zanyimasa nasha gayama kadin ga sassauta ma zuciyar ka hakan babu kyau amma kaki .kawar da Kai yayi sannan yanufi qbokin nasa ya fusge key din motar sa yace seka nemi me gyarawa seka shiga yana maganar yana tafiya . kad'a Kai kawai safwan yayi yajuya ciki don ya karasa aikinsa .

tafe yake yana tunanin waye zai iya masa haka , lallai inya kama kowaye tabbas bazaiyi masa ta dadi ba ahaka har ya iso unguwar su dake cikin g.r.a ya tsaya a dai dai wani tangamemen gate horn yayi aka wangale masa gate din farko yana shiga aka bude na biyu se gurin ajiye motoci ya kashe motar sannan ya tattaro wayarsa da takardunsa ya nufi d'ayan  gate din Wanda zai sadaka da haraban gidan ga wasu fulawoyi masu ban sha'awa da qamshi, kofar wani sashe ya tsaya ya danna wani abu take kofar ta bud'e yashiga cikin katon falo Wanda yaji kujeru na alfar ma ga dadduman dayake shimfide akasan tiles din falon da kudinsa yakai miliyan d'aya,ga katuwar plasma se aiki takeyi ga ga ga mekaratu na barmaka sauran ka karasa domin haduwakam gidan ya hadu,sama ya haye ya bud'e wani kofa tare da sallama ya nufi ciki wata mata na hango fara sol zaune a bakin gado tana gyara daurin kanta ya nufeta tareda ware hannunsa ya rungumeta oyoyo sweet mom Allah nagaji yau yayi maganar cikin shagwaba murmushi tayi itama tana me cewa oyoyo son neman halal da wuya sannu Allah yama albarka,maza jeka watsa ruwa kazo ga abincinka can yana jiranka to mom ya sunbace ta ya mike ya sauko kasa ya bud'e wani kofa tare da sallama yashiga waw abunda na fad'a kenan don d'akin ya tsaru iya tsaruwa falon yaji wasu royal chairs masu kalar sararin samaniya da lallausar dadduma shimfide se tv dake makale a bango ,se fridge acan gefen falon se tashin qamshi me sanyi d'akin yakeyi ga sannyi ac daya hadu yabada wani ni'im taccen dadi , bedroom ya nufa shima ba baya ba wajen had'u wa don gadonsa ma abun kallo ne abakin wani tebur me dauke da laptop ya ajiye wayoyinsa ya cire suit din jikinsa ya jefa a laundry basket sannan ya shiga bathroom ya jima aciki kafin ya futo ,yana me tsane jikinsa da towel ,ya nufi gaban mirror ya feshe jikinsa da turaruka masu matukar qamshi ya mulka cream dinsa gaba d'aya dakin ya gaureye da qamshi sannan ya Sanya farar jallabiya me gajeran hannu yasanya gajeran wando taciki ya futo domin cin abinci afalon ya tarar da wannan matar da yakira da mom ya nufeta yana mecewa mom yaya naji gidan yayi shiru banji yar rigimarki ba ,ta harare shi Kai kaga rigima nikam auta na ba rigimammiya bace ,suna maganar kuwa sega wata kyayyawar yarin da bazata wuce shekara shabiyu ba ta futo tawata kofa laa ya amjaad yaushe ka dawo ?Ina oyoyo Ina ?Ina  cinnakan danace maka inaso ka siyo min? U see ai naga ya miki mom wannan problem ce ,ya dubi yarinyar garama kima mutane shiru da wannan dogon tambayar taki don ko d'aya ban sayoba .....qi bai kaiga gama maganar ba ta callara Karan da ya sanya shi yin shirun dole yana me toshe kunnan sa tare da kad'a kafad'a alamar ko a jikinsa,yanufi table don yaci abincin sa ,mom ta dubeshi amma dai kasan baka kyauta ba kasan bazaka siyo mata ba seka samata rai kace zaka kawo mata ta juya gurin yarinyar ta kamo hannunta ta zaunar akan kujera yi shiru abunki my satiira ga ice cream can ki dauka ki rabu dashi,nidai
              "cinnaka "
zaki sayomin mom Allah bakiji dadin sa bane ,qawata data kawomin tace daga buzaye yayanta yakawo mata tsaraba da zai dawo daga abuja ,shinefa nima nace yayana nima zai sayomin basai na karbi nataba , tarinqa matsamin har na karba shine yamin dadi sosai nazo nabama bros labari yace zai sayomin amma kinga ya sab'a alkawari ta sake fashewa da kuka ,mom ta jawota jikinta tana rarrashinta tareda aika ma amjaad dake cin abinci harara murmushi yayi don ya tabo "Yar lelen mom ,yacigaba da cin abin cinsa ahankali yace to ai ni banje abuja ba seki jira randa naje abuja Sena tsaya nima na sayo miki inkuma kinsan gunda ake sayarwa anan kibari innaga ma semu tafi cewar amjaad,no bros nidai sai dai muje can yanda friend d'ina ta gayamin acanne kawai zamu samu wani kallo ya watso mata ta sake b'are baki don tasan ma'anar kallon mom tace haba satiira kinsan kuwa inane  buzaye bafa nan kusa bane wani gari ne daban maza share hawayenki zansashi takanas ya shirya a karshen satinnan yaje ya sayo miki tunda shiya d'auki alkawari wa kansa ,da gaske mom da gaske habibty kinga Monday sekema kije dashi skull ki nuna ma kawarki kema yayanki na sonki yaje har garin buzaye ya siyo miki tsalle tayi tana duban wan nata thanks bros taje ta manna masa kiss sannan ta dawo suka cigababa da kallonta kamar ba ita bace me rusa wannan kukan .

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now