*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
PAGE3️⃣4️⃣
haba k'awata kinutsu muyi magana mana,yanzu miye kikeso ayi akan hakan jamcy ta tambayi kawarta rumana ?
nifa wallahi baniso ace gayen nan ya kusanceta ne don ba karamin tashin hankali zan shigaba idan wani abu ya shiga tsakaninsu ,don hakane ma banison kusancinta dashi ,gata shegiyar yarinya yanda kikasan ita tayi kanta ,daganinta idonta abud'e yake wallahi,amma duk ba wannan ba asannu zan saita ta yanda nakeso ,nidai burina yadawo d'akina yau d'innan don wallahi bazan iya hakuri har na tsawan kwankin daya lissafo ba.haba rumana miye kikeyi haka ne sekace wacce bataje makaranta ba ,wannafa haka yake a shari'ance don haka dolene kiyi hakuri ki kauda idonki daga garesu kibama banza ajiyansu ,akwai wani had'in dana samo miki kinga kafun yadawo gareki kingama had'a kanki yanda zaki samo kanshi .
àjiyar zuciya rumana ta sauke tace to shikenan zan jira zuwanki amma wallahi don gyaran dazanyi ne amma dabadun hakaba dase dai yau mu had'u dukanmu uku adaki d'aya in jaraban yakeji dashi seya had'a mu duka yaci amma bazan kyalesu yaje yana iskanci da itaba yanzunma ba wai barinsu zanyi su wala ba kedai sekinzo kawai.baba me zuma ne zaune shida Inna zulai a falon shi ya tasata agaba yana mata bayani , agaskiya zulai yakamata ace kun waye shekarun mufa dad'a ja sukeyi ,amma ace fisabilillahi duk zamanmu dake bazaki ringa mayarmin da martaniba sedai ki kwanta min kamar ruwa nine zanyi kid'ana nakumayi rawa na,bakisan bada gudumawar mata yana dad'a zaburar da miji ba, to in baki sanibane yau barin sanar dake don naga ke bakisan zuru ba ,yakamata ace kisanya ido ga duk wani numfashi na a shimfid'a kilura da Ina zaki tab'a numfashina ya canza to inkika tab'a kikaji canzuwana seki rike a kwakwalwarki duk randa muke tare a shimfid'a sekiyi amfani da abunda kikasan zaisa nafuta a hayyacina don harga Allah yanzu na farfado daga zalintana da kukeyi, nima yanzu so nakeyi amayar dani d'an lele a shimfid'a, a tarairayeni a mulmula ni kamar nakiya .
Kai Inna zulai ta gyad'a tareda cewa wallahi ni malam kunya nakeji......bata karasaba baba me zuma ya katseta yace na rabaki dacewa malam d'in nan nemo suna me zafi Wanda inkin furta zanjini a gajimare Ina yawo seki damk'oni da zafafan aikin ki .
rufe ido inna zulai tayi tace to shikenan ranka shidad'e takawarka lafiya wani irin washe baki baba me zuma yayi yace shiyasa nake matukar kaunar ki saboda saurin d'aukar gyaranki Allah yayi miki albarka matata abar alfahari na ya rungumo abarshi daganan salon ya canza na janyo musu k'ofa don karnayi mugun gani, oh su baba me zuma ba'a tsufa .Kwance tashi babu wuya awajan Allah yau ne zan futa daga girkina na sakar ma rumana miji ,gaba d'aya hinin yau jina nakeyi wata iri jikina ba karfi kamar Wanda zan shekara batare dashiba ,shima duk yayi sukuku duk da bai furtaba amma daga yanayin magananshi zaka fahimta,don futarshi office munyi wata dashi yafi sau biyar zuwa yanzu, abincin rana na shirya mishi me rai da lafiya na jerasu akan dinning naje na tsalo wanka na mulke jikina da mai da turarukan danasan yafi kauna,riga na d'auko daga cikin kananun kayan da junayna takawomin ranar wai naci amarci ban taba sawaba se yanzu na bude jakan data wakomin aciki,na duba duk Babu na arzik'i se wata riga itama da kad'an ta wuce cinya ,tayimin kyau kam na gyara gashina na d'aure ta gefe yabada style me kyau nafito tamkar wata Cristi, butter mint na jefa a bakina na koma falona na zauna tareda kunna Africa tv3 ina kallon tafsir ,Karan bude k'ofar falon ne ya sanyani juyowa don ganin wanene duk da nasan shine kawai yake bude k'ofar falon batare da ya kwankwasa ba ,tsayiwa yayi tareda ware hannunshi alamar na tawo ,yinayi kamar van gabe nufinshiba nace bisimillah my oga, mak'e kafad'a yayi yace o'o kamar wani yaro,dariya nayi nace haka kadawo yanzu kuma?Kai ya d'aga min yace nidai in baki zoba bazan shigoba ,ganin bayida niya ne ,yana neman ya janyomin attention din matar gidan a akanmu yasani nufanshi cikin takun dayake girgizamin jiki daman ga abubuwan tabarakallah mashà Allah,ido ya kuramin har na k'arasa na shiga jikinshi Ina me sauke numfashi shima numfashin ya sauke tareda hade hannunshi ya matseni a jikinshi tsam ,hannunshi na ruke muka nufi cikin bedroom,jakan dayake hannuna na ajiye mishi a yanda yake ajiyewa tunda ya dawo d'akina , takalmi shi cover shoes na cire na taimaka mishi yacire kayan jikinshi nace ruwa na ciki ka daure kayi seka futo Ina jiranka a falo ,kallon k'asa k'asa yakemin yace da dai kin daure kin cikate ladarki ,nace a'a nikam nayi nawa kaidai kaje kayi Ina jiranka ,kamoni yayi tareda mik'ewa yana nufar hanyan bathroom din dani nace pls hayateey zanyi mura Inna sake wanka yanzu kadaiyi zan tayaka anjima , really kaina na d'aga mishi sannan ya shige nikuma na nufi wardrobe na zab'o mishi kayan shan iska Wanda bazai takurashi ba ,na feshe su da turarenshi na ajiye mishi a bakin gado na koma falo Ina jiranshi .
bayan mun gama cin abinci ne muna zaune muna kallo Ina jingine a jikinshi don abincin ya f'ada min ,muna kallon yana shafani don kamar al'adarshi ne haka matukar zan zauna kusa dashi zaita shafani har na saba yanzukam , bud'e k'ofar falon akayi da k'arfi batare da sallamaba ,dukanmu k'ofar muka kalla ba wata bane illa rumana don haka na kauda kaina Ina mejin takaicin irin wannan jakantar, ka shigo wa mutum d'aki ba tareda ne man iso ba ko tunanin a wani hali zata iskemu ita batayi ,dubanta yayi yace lafiya zaki fad'o ma mutane d'aki babu sallama ?
kaika San wannan ni ba abunda ya kawoni ba kenan ,tashi zakayi ka wuce mutafi ai lokacin ta ya futa na girkin don haka banson shiga hakk'i,dubanta yayi yace da rana fato fatonne zakizo ki cemin na tashi mutafi , to ban tashinba zoki jani ,wai dan Allah rumana meyasa kike da gajen hakuri ne ?inkinyi hakurima anjima ne zan dawo gareki fa har zuwa gobe ,kwata kwata awa nawane ya rage na dawo da zakizo ke gaki isasshiya kinzo kisanyani agaba ko ?
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Fiction généraleLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...