💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍️ Real Rashida Bature.
PAGE2️⃣7️⃣
*WANNAN PAGE DIN NAKINE JAMILA MAINASARA INA MIKA GODIYATA GA KULAWARKI NAGODE SOSAI ALLAH YABAR ZUMUNCI*
Dubana yayi yana karemun kallo idonshi ya tsaya akan d'an karamin bakina kafad'a ya daga alamar nina sani , sannan yace ni dai nagaya miki bazaiyiyu kici min kud'i a bulus ba,
"Juya idona nayi tare da kallon littafin gabana don bazan iya kallonshiba yanamin wani irin kwarjini ,cikin sanyin muryata kamar wacce banison yin maganar nace Kai kaga bulus nikam ko yanzu aka watse a taro ai namaka aikinka tunda bukata tabiya .
"injiwaye bukatar ta biya?
"injini mana tunda nayi abunda akeso.
"waya gayamiki kinyi abunda akeson?
ko ba'a fad'a da bakiba alamu ya nuna .
"look karfa ki zak'e dayawa kiga kamar kokinyi abun kirkine ranar ,abunda yakawoni kenan gunki yau don naga kamar bazaki iyaba ,inbazaki iyaba tunwuri kigaya mana mu nemi kwararriya don banson azo ana mana kwana -kwana kina ganewa ko ?
"kallon shi nayi nawasu lokaci kafun na sauke idona daga kallonshi nace
"fine "na janye kuje ku samu babbar matan da ta kwaren ,kuma kudinka dai bazan bayarba,don naci kud'in aikin dana muku ranan.
"ido ya kankance yace ke harkin isa to bari kiji yanda kika fara haka zaki karasa in zaki zage ki dage gara kiyi don babu Wanda yace kice zaki iya sedaga baya kiwanizo kice kinfasa ,mawa zakima wasa da hankali.
"shiru nayi ban kulashiba na fara tattara takardun dasuke kan table din,zan mik'e ya min wani irin kallon da yasa ni dole na koma na zauna Ina me zunb'uro bakina gaba .
"wato ke ba'a isa amiki gyaraba sekiyi fushi ko?
haka aka gayamiki ake rayuwa?
kauda kaina nayi gefe ,ba magana nake mikiba kinyi banza dani .
toni me kakeso nace maka ,kace in ajiye ma aiki inbazan iyaba nace zan ajiye kace ban isaba , to ni bansan yaya kakeso nayi makaba .
"yanzu maganar danayi yasa kikayi fushi kenan?
"amma kamar yar jejeniyar da mukayi banda kin amsa magana ko?
"nifa baby ba fushi nayi ba kawai nayi shiru ne .
"to ki bud'e baki kimin magana yanda nake miki don kece kika sanya wannan dokan bani ba, kuma kinsan na tsani nayi magana ayi banza dani .
ashe ba dadi kenan, Kai zakiyi ma wani amma Kai bakason ama, na fad'a azuciya na ."yanzu me kika yanke akai ,zaki gyara ko ahaka kikeson Kita tafiya babu gyara ?
"shiru nayi banda niyar bashi amsa ,Sena tuna da maganar shi ta d'azu nace to.
"to me"?
"to zanyi , murmushi naga yayi .
" araina nace mugu don ka bani wahala ma ai dole ka tillastani kace nice zanyima aiki, bayan ga Yan mata dayawa agari ,kawar da batun zuciya ta nayi nace amma muje zuwa nida Kai ne."dubanshi nayi naga wayarshi yake dannawa na dubi abubuwan da rabe ya kawo mishi ko tabawa beyiba ,cup na dauka tareda tsiyaya mishi kunun ayan a cup din ,na bude mashi samosa na dubeshi nace my soulmate kasha karyayi zafi ,kallona yayi tareda kallon cup din dana tsiyaya mashi ,yace ai na barine naga hankalinki ankawo abu kinbari nina zuba dakaina ne ko?
"no baby ba haka bane,kaine ka rikitani da kalamanka nakasa tuna komai ,.
"hmmmm da kuma nayi shiru sekika tuna kenan ko?
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Ficción GeneralLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...