💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
*💫⭐SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION💫⭐*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
*mata masu fama da sanyi akwai yaji Wanda a abinci kawai zakici dashi ,zai wanko miki duk wani datti da sanyin da take Sanya Miki ciwon mara ko yake samiki jin zafi a gabanki kamar kinsanya barkono ,sannan akwai tsimin sanyin duk me bukata seta nemi wannan number ,07052100719*
*Ina godiya da kulawarku masoya sannan Ina alfahari daku nagode da addu'oin ku gareni thank you so much*
PAGE4️⃣0️⃣
Wani irin sarawa kanshi yayi ,tareda girgiza kanshi ,mom ne ta dubeshi don ganin yanayinsa ya canza alaokaci d'aya,ga zaburan dayayi .Son lafiyarka kuwa ?
Dafe kanshi yayi tareda tsurama khubra ido .
mom ne ta zo kusa dashi ta kama hannunshi ta zaunar dashi,son kanutsu ka gayamin meke faruwa ?duk ka tashi hankalin mu.
d'ago idonshi dasuka rune yayi yana cizon bakinshi ya kasa cewa komai .
nikam gaba d'aya nashiga tashin hankali ganin yanda lokaci d'aya amjaad ya burkice se zufa kawai yakeyi .
ruwa mom tace na miko mishi a fridge,jikina a sanyaye naje na d'auko me d'an sanyi nakawo na bud'e bakin goran na tsiyaya a cup na mika mishi ,bai karba ba ,mom ne ta karb'a ta kafa mishi cup din yayi abakinshi ,take ya bud'e bakin ya shanye ,cup din mom ta mikomin nasake zuba ruwan aciki na mika mata ,shima tas ya shanye sannan ya dubi mom kamar zaiyi magana sekuma ya girgiza kanshi tareda datse hakoranshi .
shafa bayanshi mom tayi tace relax son kabi komai ahankali,ka nutsu kamin bayani.
"yaushe khubra tazo nan yau mom ?
wani abunne son?mom ta bukaci Karin bayani.
no mom yaushe tazo nan yau?
"Tazo nan da safe misalin takwas inaga koda minti biyar ne ko goma tun lokacin kuma bata sake futa ko inaba .
Kai ya kad'a tareda dunkule hannunshi ,wallahi mom bazan yafe maduk Wanda yamin abunba,duk Wanda na kama yanada hannu acikin wannan abun bazan kyaleshiba,zanyi mqsa hukunci me tsanani,
kamin bayani ka tasani gaba kana surutan daban ganeba ,wai meyake faruwa ne kam?
wayar ya mika mata,karba mom tayi tana dubawa,zare ido naga mom tayi ,ta d'ago Kanta tana kallona sannan ta ce innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. wannan wane irin abune haka mara kyan gani ,??
gaba nane naji ya fad'i ganin yanayin mom itama ,take naji hankalina ya tashi ,shin wani abu akace nayi harya sanyasu awannan tashin hankalin?
Ina zaune agun amma daka duben zakagane Ina cikin tashin hankali,tasowa nayi daga gurin danake zaune na k'arasa kusa da mom ,wayar dake hannunta na karba don ganin abunda ya tashi hankalin su.ido na futar waje nima ,don ganin hoto na dana wani namiji ,hoton farko yana rike da hannuna ,Sena biyu ya rankwafo alamar zaiyi kissing dina ,Sena uku kuma ya rungumoni,Sena gaba kuma Ina kwance ajikinshi muna murmushi,wani irin sarawa kaina yayi tare da faduwar gaba me k'arfin gaske,dafe cikina nayi wanda naji ya murd'a min,kamoni mom tayi tace kwantar da hankalinki karkiji ma kanki ciwo ,hawaye ne ya zubomin tare da kuka me karfi daya kubcemin, inayi Ina rike da cikina ,
Mom bata hanani ba nayi kaku na sosai ,tareda tsinema duk wanda yamin wannan sharrin,duban amjaad nayi tareda karasawa kusa dashi na durkusa a ganashi gwuiwata suna k'asa nace trust me amjaad, wallahi tallahi bani bace ,karka yarda da abunda suka turoma sharri ne sukemin ...Ina kuka Ina maganar don nashiga rud'ani,Kai ya d'aga min don bazai iya cewa komaiba,ganin kukan danakeyi ne mom ta mik'ar dani tsaye tace is ok daughter karki ja ma kanki wani ciwo ,zansa ayi bincike don ganin an gano gaskiyar lamarin , inma wani ne yayi hakan duk zamu gano .
kauda kanshi amjaad yayi yace mom ai gaskiya kam abayyane take ......wani irin razana nayi don jin abunda yace ,take nasake shiga wani hali,kukana ya karu.
![](https://img.wattpad.com/cover/251018272-288-k745218.jpg)
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Fiksi UmumLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...