chapter 8

531 62 1
                                        

💍 CIKAKKIYAR MACE💍

✍️Real Rashida Bature.
                      
PAGE.7️⃣
Se gab da magriba na isa gida na iske su janka suna majalisar su suna zaune nafito a motar nashiga ciki na bude get din nace ma me motar yashigo da motar kayan sannan na nufi majalisar su janka na musu sallama duk suka amsa janka ya duben

"hajiya qamshi nataso ta samu ne?"

"kusan haka "kaya nakeson a saukemun daga mota.juyawa yayi  yama yaransa magana muka nufi gidan gona suka saukemun gaba d'aya kayan na mika musu dubu daya nace asha ruwa amma Sam janka yak'i karba yace haba qamshi wannan gudun mawar mu kenan, Sena gaba zamu karba nayi godiya sannan suka tafi .
Nadubi me mota nace baka gayamin sunanka ba Yaya na ?
yayi dariya yana me cewa haba hajiya nine yayankin ?
nace au da so kakeyi nace nice yayar ka ?nasan dagani kayi shekara talatin koma kafi, nikuwa kwata kwata shekara 19 ne dani In hakane kuwa kaga ba laifi bane don nace maka yaya na ,yace kumafa hakane hajiya

      " sunana isma'il"

Ina nan cikin garin
  
          "biciki"

la yaya na  kace makwaf ta ma muke dakai ,ai mutum da k'afa ma zai karasa garinku Kai amma naji dad'i Ina maganar kamar ammin dole don Sam banson dogon magana ,yace hakane hajiya ,nace to yanzu ungo wannan kudin aikinka ga wayata ka sanyamin number ka in za'a dauko min kaya Sena kiraka ya karb'i wayar batare da ya karb'i kudinba yasanya min number sa yaban nayi save sannan na sake Mika mishi kudin yace a'a hajiya bazan karb'a ba ni yanzu duk kud'ad'en dakika kashe na sayan tayar motar ne damuwana don wllh bansan ta Ina zan faraba .
nayi murmushi nace karka damu kuma bani bukatar ko sisin ka , wannan kuma kudin aikinka ne yazama dole ka karba na sake mika mishi,nace  ka karba lokacin sallah yayi zanshiga ciki ,ya rusuna ya amsa yana min godiya nace no ba komai Sena kiraka allah ya tsare.

assalamu alaikum my kakus na dawo sallah na tarar ta fara,Sena shige d'aki na nima na daura alwala na tada sallah ban fito falo ba har saida nayi sallar isha'i sannan na futo na shige kitchen na zubo sauran abincin danayi na walima daman na rage mana na dare aciki nazuba na dauko zo6o na dawo falo ,yayi dai dai da futowar hajiya kaka ,nace sannu da gida hajiya yauwa khubra andawo ?ey nadawo na tarar kina sallah to Masha Allah kinkuwa samu duk abunda kikaje sayan ? duk nasamu amma senaga har yanzu masu kawo kajin basu iso ba Ina duban kakus,ito myb wani abun ne ya tsayar dasu allah dai yakawo mana su lpia nace amiin .nacigaba da cin abincin har nagama na Kai kitchen na wanke na goge gurin na dawo muka cigaba da hira da kakus.
se wajan k'arfe tara na dare sannan masu kaji suka kirani nayi masu kwatancen dai dai yanda zasu tsaya,rabe ne yashigo da gudunsa Adda adda gamasu kaji sun iso !se haki yakeyi alaman ya sha gudu to d'an nema baki abun magana sannu da kawo rahoto cewar kakus ai daga yau gantali ta kare maduk Wanda yake gidannan garama kusani yimaza kaje kagaya musu gamunan futowa .

lale marhabun ya kaji maraba maraba da kajin hajiya qamshi sannuku sannuku abunda hajiya kakus keta nana tawa kenan ,masu motar kaji dai tsayawa kawai sukayi suna ganin ikon Allah, sannuku da hanya abunda nace musu kenan sannan na bud'e gate nace bisimillah kushiga daga ciki sunshiga da motar na dubi rabe nace mushiga kaima ,muka shiga suka bude motar nace amma dai se na nemo masu tayaku ko?daya daga cikin su yace habawa hajiya wannan ai aikin mune bamu minti goma kiga ikon Allah,anbaku har ishirinma inji kakus.a kofa na tsaya Ina kirga kajin aiki sukeyi cikin kula da sanin aikinsu da ikon Allah kuwa cikin lokaci k'an k'ani suka gama da manya guda dubu biyar se na nuna musu gurin da zasu Sanya kananun sabbin fafa wato day old sukuma guda dubu biyu ,suka gama na biyasu kudin aikinsu mukayi sallama suka tafi ,Adda khubra dan Allah ki daukeni aiki badin halina ba kinji adda ,nayi kamar ban jiba naci gaba da had'a ma kajina maganin su aruwan shansu ,bayan na gama na dauka nafara shiga musu dashi ya biyoni Adda khubra zan tayaki d'aukar nima ,u make sure kasanya takalmi gasu can dana siyo najuya naci gaba da aikina,da hanzari ya Sanya  ya fara tayani muka gama shigar musu da ruwan sannan muka zuzzuba musu abincin rabe se murna yakeyi yau na barshi ya tayani aikin kaji , hajiya kaka ta tottofe dakin da kajin suke  da addu'a sannan na kulle ko Ina na kunna musu room hitter dai dai yanda bazai musu illa ba  na bar musu haske sannan muka koma cikin gida kakus se addu'a take faman jero musu .

😘

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now