Chapter 32

651 46 1
                                        

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍🏻Real Rashida Bature

PAGE3️⃣1️⃣

Baba me zuma ne zaune gaban kakus ya zuba tagumi ya rasa yanda zaiyi da ita ta sakko daga fushin datakeyi.
dubanta yakumayi yace hajiya kiyi hakuri ki gafarceni kinsan duk abunda zanyi bazanyi shi don naga na b'ata miki raiba ,wannan ma da nasan ranki zai b'aci da hakan wallahi da bance ayiba ,ni aganina hakan shine dai dai .

kwallar fuskarta ta share tace a duniyar nan dai damuke ciki a yanzu ban tab'a ganin anyi hakaba daga zuwa biki sekace na bar musu amarya ko gyaran jiki banyi mataba to wallahi ko mijin ne yazo da kanshi yace ya riketa senaje na d'auko abuna na gyarata ciki da bai ,mazan yanzu kayi gyaran ma yaya aka k'are da rashin mutumci su bare kaje tsigai tsiyo to bari kaji a satin farko wani zai kad'o miki yarki me hankali ne zaice a gyarata marashi kuwa da sakinta zata dawo , don haka wallahi yanzu ba se anjima ba zanyi waya aje a d'auko min jikata bazan iya wannan abun kunyar ba.

Ki fahimceni hajiya ni bani son nazama me magana biyu ne a d'aukeni karamin mutum gani ga uban yaron ga mijin mukayi magana nace tunda suna gidan base an dawo da ita ba abarta kawai tazo da zuwanta .

Innalillahi jamilu jamilu awani gari kataba ganin anyi haka ?

To bari kaji ka dad'e ba'a maidakai k'aramin mutumba nizaka muna furta ,mun gama magana dakai shine zaka  zaga kace su riketa sabida jikata yar tsana ce , bama wannan ba shi yaron daka tasashi agaba ka gaya mishi inace cewa mukayi a bunne abun sedai yaga ankawo masa ita yanda kakanshi tace ?
to shikenan naji yanzu katashi kaje ka kawomin kud'in dana gayama za'ayi mata gyaran jiki .

Allah ya huci zuciyar ki hajiya kiyi hakuri,to yana iya ai hakuri yazama dole

mikewa yayi tana ganin futarshi ta janyo wayarta ta lalubi keypad dinta don kowani suna anyi mata alama da keypad din yanda zata gane don haka batasha wuya ba wajan gane number malama zuwairiyya bugu biyu ta dauka ta gaida hajiya cikin girmamawa.

hajiya ta Kora ma malama zuwairiyya bayanin abunda takeso ayi ma jikarta sannan ta shaida mata nanda anjima zata gansu ,sukayi sallama ta kashe wayar ta mike ta lek'a gidan gona ta Kira rabe tace yi maza kaje kayi shiri ka rakani wani gurin ,komawa yayi gidan gona ya karasa abunda yakeyi kafin ya dawo ya shirya falo ta zauna tana jiran shigowan babab me zuma,tana zaune kuwa se gashi, guri ya samu ya zauna tareda mik'a mata  kudin karba tayi tace dafatan yanda nace ka kawone? yace hakanne hajiya tace to mashà Allah,Amma jamilu meyasa ka yanke hukunci batare da ka nemi shawara taba ?

gyara zama baba me zuma yayi yace hajiya Ina me dad'a baki hakuri akan abunda na zartar batare da saninki ba,a jiya lokacin da kuka bar gidannan zakuje can gurin bikin nima nabi bayanku nida malam sahabi ganin duk Wanda yakamata ace sun hallari bikin amarya a abiki kuncika to me zai hana kawai tashige diyanin base anta koma bayaba ,Sena tashi naje gidan malam sahabi namishi bayani yace to in  hakane me zai hana nabiku can din se na nemi shawararki acan da isarmu muka tarar har kun riga kun tafi muna kokarin futa daga gidan se ga alhaji majeed arab yayi mana iso bayan an gaggaisa ne nake cewa so nakeyi na tambayi shi amjaad in har ya shirya to base andawo da ita khubra ba zuwa gobe in sha Allah zansa akawo kayanta ayi mata jere , alhaji majeed arab yaji dad'in hakan kwarai da gaske yarinka mana godiya yace bari mujira shi amjaad din su dawo daga gurin dinner aji daga bakinshi duk da bayi da matsalar gurin sakata .

zuwa can bayan kun dawo yazo sallama ma mahaifin shi zai wuce gidanshi ya tarar damu mahaifin shi yayi masa bayani dayake yaron arzik'i ne irin mahaifin shi karkiga irin godiya dayake mana muka musu sallama muka dawo to lokacin dare yayi ban zaci zaku dawo a ranar ba Sena dawo akan gobe zanyi sammako naje gidan na iskeki semu tattauna maganar to kinji yanda abun yake hajiya.

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now