Chapter 43

458 41 0
                                    

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍🏻 Real Rashida Bature.

*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION* 

'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'

I think you'd like this story: "CIKAKKIYAR MACE" be RASHOWS on Wattpad https://my.w.tt/zq9Wot0H9bb




PAGE4️⃣2️⃣

Kafin mom tayi yink'urin rike khubra, amjaad ne cikin zafin nama kafin came me harya iso gurin ya riketa .

kan kujera ya kwantar da ita ,fuskarta ya shafa tareda kura mata ido,baby karfa kisa ma kanki damuwa akan wannan abun.

son dolene fa abun ya tayar mata da hankali,domin kuwa wannan ba karamar abu bane ,inda bamusan halinta ba Kai kana ganin duk da sharri aka mata in wani mijin tasamu zai yarda ne ?shiyasa akecewa yana da kyau ma'aurata su nutsu suyi ma junansu kyakykyawan fahimta Wanda ko agaba za'azo ace wance ko wane yayi abu kaza ,to zai tsaya ko zata tsaya tayi dubi da irin halin mijinta ko matarsa seyaga hakan dame ya dace .

kaga kamar yanda Kai ka shaidi matarka ,don Allah kucigaba da hakuri da junanku ,sannna kucigaba da kyautata zamanku , Allah yayi muku albarka,yakareku daga dukkan me sharri , yakad'e futuna,ya Toni asirin duk Wanda yayi wannan had'in.

ido na bud'e sannan haryanxu idona baibar zuban hawayeba,mom ni asanina babu Wanda namishi wani abu balle nace ramako yayimin ,mom inma mutum zai rama seyayimin irin wannan gingimemen sharrin,k'azafin zinafa akamin da aure akaina, fisabilillahi Yaya sukeso nayi,tun Ina gida banyi zinaba se yanzu danasan yin hakan babban laifine yin zina da aure wa'iyazubillah,wasu hawaye masu zafine suka sake zubomin.

sharemin amjaad yayi,baby banison wannan damuwan dakikeyi,ninan na d'aukar miki alkawari nanda 2 days in sha Allahu za'a gano duk Wanda yayi wannan aikin,ki kwantar da hankalinki,kaina gyad'a mishi tareda share hawayen fuskata.

direct Choco photos yanufa sama ya wuce office d'in manager,jikin manager na mazari don ganin amjaad dayayi a office d'in sa,don yasan waye amjaad yakuma san mahaifin amjaad sannan uwa uba yana auran Yar matemakin governor,kujera ya gyara mashi tareda gaidashi ,ah ranka ya dad'e aida ka kiranima nazo da kaina hàr gidà, Allah yasa aiki zanyi?inkuwa takasance hakane dakuwa nafi kowa morewa.kallonshi amjaad yayi na seconds ,sannan yaja numfashi aiki nakeson kamin amma ga rin Wanda zakumin ko zaku iya ,wayar sa ya ajiye akan table din gaban manager , d'aukar wayar yayi ya kurama hoton ido , sannan ya ajiye ta akan table din, agaskiya yallabai bamu irin wannan pic din ,sedai waje d'aya ne sukeyin irinshi a duk garin bauchi, nanne kawai za'a muku.
ok zanso kaban address din gurin .
rubuta mishi yayi tareda mishi godiya nazuwa studio dinsu dafatan nan gaba yallabai za'a bamu aiki.
Kai kawai ya d'aga mishi sannan yafuta .

direct studio din rashows photographer yanufa ,tundaga k'asa ake gaidashi amma bai amsa ma kowaba ,yadubi wani yaron shagon don duk ma'ikatar gurin suna sanye da riga me dauke da sunan gurin ,inane office d'in manager, yallabai barinma jagora nakaika,gaba yaron studio yayi amjaad nabiye dashi a baya , manager na tsaka da aiki yaga shigowan amjaad office d'in sa ,baki ya washe ,ah lallai yau inada manyan bak'i a gidannan sannu da zuwa rankashi dad'e barka da yammaci,yauwa,bayan manager yamasa iso ne ya zauna,sannan amjaad ya ajiye wayar shi akan table din gabansu ,so nakeyi amin irin wannan aikin,but antabbatar min ananne kawai za'a iyamin irinshi.tabbas duk inda zakaje agarin bauchi tofa dole kadawo nan ma'ikatar matukar aiki irin wannan kakeso ,ya kareshe maganar murmushi d'auke a saman fuskar shi na ganin sune manya a yin hoto agarin bauchi.

baki amjaad ya tab'e sannan ya kad'a Kai, so wayene me aikin ko Kai kakeyi da kanka?

no yallabai,wani hazakakken yarona keyin aikin shiyasa nakeji dashi domin ya kware ta wannan fannin .

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now