💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻Real Rashida Bature
PAGE1️⃣0️⃣
Wannan page nakine *@MUM H.A.H*
Duk Wanda ya dubi fuskar àlhàji babà me zuma zai fahimci yana cikin b'acin rai fuska ba fara'a yashigo gidan ciki ciki yayi sallama shima don yazama dole ne da baziayi ba, inba kana kusa bama bazakaji sallamar tashi ba bai amsa sannu da dawowar da matansa da yara dasuke masa atsakar gidan ba ya nufi falon sa harya kai bakin k'ofar yajuyo yace saratu inkin k'arasa abunda kikeyi ki kiramin sauran kuzo dukanku .Inna saratu shiru tayi tana me nazarin mijin nasu don tunda ya shigo take ganin kamar yana cikin damuwa don haka seta tsame hannunta daga tsince shinkafar datakeyi ta dubi maryan 'yarta tace yi maza ki gayama tabawa tazo malam yanason magana damu tazo d'akinsa daman itada Inna zulai ne awajan suka mike suka nufi d'akin mijin nasu ,sun tarar yana zaune akan kujera se kad'a k'afarsa yakeyi bai ce musu komaiba har Inna tabawa tashigo ta nemi guri ta zauna tare da cewa sannu da dawowa malam bai amsa mataba itama kamar yanda yayi ma sauran matan ,d'akin ya d'auki shiru tsawon nawasu mintuna ,kafun ya dubesu yafara magana cikin kwantar da murya yanda zasu fahimci maganar harta shigesu ,yanzu ku fisabilillahi kun kyauta min kenan konace kun kyauta ma kanku ? yayi shiru yana me binsu da ido kamar yanda suma shid'in suke kallo kuma suke sauraro ,yaci gaba da cewa tsakani da Allah ace agidana ake koyarda abubuwan k'aruwa amma ni matan gidana basu k'arunba sedai azo anamin godiya irin gudun mawar da d'iyata take bayarwa wa matan waje har mazajensu suji dad'in abun suzo suna min godiya alhalin ga Wanda sukafi bukatar agyara munsu nan Inna tabawa ne tayi carab tace wai shin malam wani magana kakeyine don nikam Sam ban fahimci yanda ka dosaba ,dubanta yayi yace ai kuwa yazama dole ki fahimci yanda maganata ta dosa to barin futo Miki a mutum sak ,yanzu Ina zaune a gurin zaman mu da muke d'anyi jifa jifa akan dakalin malam audi sega malam tanko yamun sallama na amsa yanemu guri ya zauna sannan ya duben yace Masha Allah daman gidanka zani na duba ko kana gida Sena hangoka anan to hakan ma yayi ,na dubeshi nace to allah yasa lpia dai yace wallahi lpia lw se alheri wato alhaji baba me zuma karkaji wani irin dad'in danake ciki kwanan nan,kuma ba kowa bace take sani wannan farin cikin se abar k'auna ta....baki bud'e baba me zuma ya dubi abokin nashi don jin kalamin dayayi wai abar k'aunarsa, ey dole ka kallen wato abar kaunata ta kasance tana jiyar dani dad'in dana rasashi tun bayan amarcina da ita ,barin baka abun abud'e don ka fahimta ,ayanzu dakake ganina idan abar kauna ta ta tsotseni tas ta lasheni tako ina idan na fara aiki zan iya kwana biyu kafun abuna ta kwanta sannan ga gyaran da abar kauna ta tayi tako ina wato tsakani da Allah Ina cikin shauki don haka kagannin nan bani wasa wajen tura yara makaranta don da kainama nake kaisu nakuma shaida ma malamin karya kuskura ya barsu su fito harse antashi nikuwa Sena lallab'a na dawo gurin abar kauna ta na d'ibi romon democrad'iya ,ga tattalin danake samu wallahi ko me take so jikina na rawa zanje nayi mata nifa har dakan yaji nake mata agaban kowa kuwa ba ruwana tattalin abuna nakeyi don nasan me nakeji nima daga gareta .baki bud'e baba me zuma yake kallon abokin nashi yace to lallai ka yi babban morewa Allah yasa acigaba amma me nene fa'idar gayamin wannan labarin?wato abunda nake nufi anan shine kaf wannan bayani dana maka ba agun kowa tasamu ilimin hakan ba se agurin d'iyarka wato hadizatul khubra kaidai wallahi kayi dacen diya Allah yayi mata albarka yakaro mata ilimin gyara mana matanmu da tunasar dasu abunda suka manta don agaskiya ba karamin temako takeyima kaf yan garinnan ba ,wllh da abar kauna ta tagayamin cewan wasu abubuwan yawanci a makaranta diyar namu ta koya narasa dame zan sakama yarinyar nan se na ba jabir dubu biyu nace aje sayo mana kwai don itama taji dad'i sannan naga yazama dole nazo nayi maka godiya don inda baka sata a makarantar koyon ba ai bazata samu ilimin hakan ba . kad'a Kai alhajinmu yayi yace bakomai ai duk yi ma kaine kuma ai kaima d'iyata d'iyar kace ahaka sukaci gaba da hira amma zuciyar babà me zuma gaba d'aya tayi gida don yasamu yadawo,zuwa can yama abokin nashi sallama ya nufo gidan yatarar da su .
dubansa inna saratu tayi a Kai kaice to don yaji dadi seme don kuma jijiyarsa tana kwana biyu a miqe se akayi yaya ai dama tsayuwa kayi ya samma abunda yasa ita jijiyar tashi take jimawa ko kaima ka moren ta fada tana me kauda Kai gefe ,ya dubeta ai dalilin dayasa na iso gidan kenan sannna inason kowaccenku ta bud'e kunnuwanta taji wallahi shine allah duk wacce tabari aka yi karatu agidannan bata hallacci gurin karatunnnan ba senayi matukar sab'a mata don naga ku bazakuyima kanku fad'aba nayi maganar nayi fad'an kunki ku gyara to sekuje makaranta inma baku iya bane sekuje akoya muku ,ace kaf gari suna jin dad'in su ni da karatun yake cikin gidana ace senine koma baya to wllh bazan d'auki wannan ba nagama magana Wanda take jin ita ta isa to taki zuwa d'aukar darasin mugani kowacce tabani guri wai kana nufin gurin yarinyar cikin mu zamu gurfana agabanta ta koya mana yanda zamu zamuyi mu'amular sure ? ey lallai yau nake ganin karuwanci agidannan cewar Inna taba dubanta yayi yace ban haifi karuwaba kuma in Sha Allah bazan haifaba kuma kik'i zuwa karatun kiga me zan miki Allah yaba ma merabon ganin fushina sa'a ,shiru sukayi suna mebinsa da kallo zuwa can kowa ta mike suka fara futa se Inna tabawa ne tace cabbdijan zanga mai kaini wllh tayi maganar nata me k'arasa futa a falon harara yabi bayanta dashi tareda sake tsaki mtssss.*****************
D'aukar takardan daya gani a samar laidar yayi donshi sam jiya bai duba laidar ba bare hankalinsa yakai kan takar dan ,budewa yayi a hankali don yaga takardan miye don shi Sam be ajiye takardaba agun ga abunda yakani .
*D'AN K'ARUNA DAKA TEMAKI KANKA KARAGE JINKAI SANNANN KAKE LURA DA DUK WANDA ZAI SHIGO DON NAGA BAKA IYA KOMAIBA SE JI DA KAI ANYA KAI JARUMI NE KUWA? DAGANIMA NASAN BABU ABUNDA KA IYA SE GIRMAN KAI KODAYAKE MA BA WANNNA BA INKA K'IRGA KUD'INKA ZAKAGA BA D'AURI BIYU TO BA WANI NE YA D'UAKAR MAKABA NICE NAN YARINYAR DAKASA YARANKA AZZALUMAI SUKA CIRE MANA TAYAR MOTAR MU SUKA TAFI DASHI WAI KAI AGANINKA KACI BULUS INKUWA HAKA KA D'AUKA KAYI KUSKURE DON NI BANI ASARA DON BA SARATU BACE TA HAIFEN KUMA BA MAHAUKACIYA BACE TA RAINAN DON HAKA YAU KAYI BIYAN BASHIN DOLE DON ZAN CIRE KUDIN TAYA NACIRE KUD'IN DANA BIYA AKA SANYA MANA DANA LADAN NEMO ME SAWA DA KUMA RIBANA DON HAKAN MA KASUWANCI NE ,SANNAN ZAN CIRE KUDIN MAGANIN TURENI DAKAYI HAR KAINA YAYI CIWO IN KUDIN TAYI SAURA ZAN BAMA ALMJIRAI SADAKA DON DAGANI BAKA SADAKA LOL SOLOB'IYON HAJIYA.
Wani irin dank'a yayi ma takardan tareda bige laidar takalmin dayakekan table din duk suka watse dukan kan table din yayi yana me tauna hakoransa cikin sauri ya k'arasa gaban table d'inshi ya danna wani abu can sega abokinsa kuma yaronsa ya shigo cikin hanzari ya dubi aminin nasa amjaad lpia kuwa ?meya sameka ?yana me karasawa kusadashi bai iyace masa komaiba don bazai iya ba ga jijiyoyin kansa duk sun fito zuba masa ido safwan yayi ya nufi bridge din dake cikin office d'in ya dauko ruwa me sanyi kad'an ya tsiyaya ya bashi kamar bazai karba hakadai ya daure ya karban ya kwankwad'e ya sake mik'a mishi ya Kara masa shima ya shenye ya zauna akan kujeransa batare da ya dubi safwan ba yace ko waye ubanta inason anemomin ita yau base gobe ba ,cikin rashin fahimtar wa abokin nashi yake magana yace ka nutsu kamin bayani waye kake magana akanta ? takardan ya nuna masa Wanda yake yashe a qasa ido safwan yabi hannunsa dashi harya sauka akan takardan isa gurin takardan yayi ya dauka ya warware ya karanta ido yafutar waje yana jinjina kokarin yarinyar don ya ganeta tsaf lallai akwai rigima duk rananr da suka had'u da abokin nashi yafad'a azuciyar sa,sannan ya dubi abokinsa yazu amjaad kan wannan rubun kake haka fisabilillahi wani kallon banza yabi safwan dashi sannan yace zaka iya tafiya kakuma tabbatar annemomin ita Sena shayar da ita mamaki zatasan ni takira da ragon namiji ko a gidan ubanta ta taga nayi ragontan oho duk setamin bayani stupid girl Sena murqushe yarinyar nan ya buga table din gabansan kallon sa kawai safwan yayi yace yanxu kasamu dai dai kai nikuma inhar naga wannan big girl din har kyauta Sena mata don ta cancanci a bata kyauta d'aukar biro amjaad yayi ya wurgo ma safwan wanda ya goce be sameshiba ya juya yana dariya yayi tafiyarsa office d'inshi amjaad kuwa maballin rigansa na sama ya bude don jiyayi rigar ta mak'ureshi .
Agaskiya comment yayi kad'an in bakujin dad'in buk din gara kawai na dakata ,inkuwa kunason cigabasa to naga sharhi inayine dominku masoya nagode.
Karku manta da vote and comment.
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
General FictionLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...