💍 CIKAKKIYAR MACE💍
✍️ Real Rashida Bature.
PAGE6️⃣.
tafiya nakeyi a nutse na nufi gurin wani d'an union dake nuna alamar sune jagororin tashan sallama namishi nace don allah malam inason d'aukar shatar irin wannan k'aramar motar ne wato (hijet) kinsamu"cewar d'an union din , Ina kayan naki suke ?kuma wani waje za'a kaimiki?"kuma wani irine kayan? sanda na d'an d'auki lokaci kafin na dubeshi da lumsassun ido na nace garin buzaye za'a kaimin ,abincin kajine suna cikin can kamfanin (AMJAAD.)
To to to angama hajiya jirani na Kira Wanda yake kan layi kinsan abun layine magana yama Wanda yake kan layin akan ansamu fasinja Amma na garin buzaye mutumin yace shi bazai je garinba ,ya tambayi me binsa alayin shima yace nacikin gari yake so sanda yayi ma mutum biyar magana sukaki zuwa, mutum na shida ne yace zaije duk Ina jinsu dayake Ina ta gefene na basu baya , yafito da motar ya iso gurina dan union ya bani littafi na cike address dakomai sannan direban ya mika mishi kudi na zagayo nashiga ,inajin mutanan da sukaki zuwa suna magana da d'an union d'in Kai musa daman haka yarinyar takeda kyau shine baka gaya mana ba ,Allah nikam ko kyauta tace muje zan d'auketa ni iya kallon tama ya wadatar min kowa yana fad'ar ta bakinsa dubansu d'an union yayi yayi tsaki yayi wucewarsa yace kanku akeji sukan sunyi gaba sedai ku tari gaba yanzukam.
shiga da motar mukayi har gurin da naga an tanadar don ajiye moto ci nace ya tsaya agun na fito na ce masa zomuje ciki sena nuna ma manager kai inyaso se ya had'aka da masu zubamin kayan nikuma zan tsaya daga ciki Ina qirgawa kaima seka na qirgamin harsu gama lodawa .
muka shiga gurin manager na masa magana nace na samo mota ,yace kash ai mu hajiya nan harda motar mu muke kaima mutum kaya har gida inyaso seya biya kudin kaiwan mun hutar da me saya nemo mota ,no no banson naku ai naji kud'in kaiwan yana da yawa ne shiyasa nayi tafiyata na nemo dai-dai ni gashinan nasamo asanya min kayan dare yana yi se ahad'a da duk kayan dakaga nashigo dashi , to babu damuwa hakanma tunda kin rigada kin nemo ai bazan ce ya komaba ban sake maganaba ya kira yaransa yagaya musu yawan kayana yace suje tare da me motar ya nuna musu motar sesu loda min ,hakan kuwa akayi suka zubamin komai nawa amotar sanna direban motar ya biyosu ya duben yace hajiya kayan sun cika Kai na d'aga masa na dubi manager nace nabarka lpia Ina me juyawa shima direba ya biyo bayana .
har mun fara rivers da motar mu na tuna ban karb'i receive ba nace wait direba don Allah ka kar6amin receive agun manager mana seya baka harda number sa danace zan kar6a domin in Ina bukata sedai kawai nayi waya akawomin ,inyaso kaga kaima semu qulla alaqa dakai sekana zuwa kana kar6amin kawai.
yace hakane hajiya dana gode kinga daman kuwa jiya jiya wata hajiya taban motar nake ja Sena ke Kai mata balance duk sati ,na dubeshi nace to shikenan jeka ka dawo semu fahimci juna ,tare muka fito na tsaya jikin motar ta bayanta ina dannan yar wayata maxfone wanda nasaya dubu uku game na kamo na maciji na mai da hankali na akan wayar senaji an danna horn akusa dani ban d'ago kainaba naci gaba da abunda nakeyi aka sake danna wa still ban kula wajan ba ,kabi kanta nace maka ka tsaya kana 6atama mutane lokaci ,wai Kai bazaka daina irin haka ba koda nabi kanta dole ai se najira me motar ya d'aga ,mtsss abunda kawai d'aya matashin yasake yi kenan sannan cikin 6acin rai ya dubi me tuka motar yace safwan wai wani d'an kasadar ne ya ajiye wannan abun agun danake ajeye mota ? wanda aka kira da safwan d'in yace sedai muyi browsing don naga tare muke dakai ai,tsakin yakumayi yana me ciza lab'ban sa salamu alaikum hajiya ga receive ga number dago kaina nayi yayi dai dai da d'agowan masi faffen cikin motar nan wani bugu yaji kirjinsa tayi tare da kadawan da cikinsa tayi ya kafeni da ido nikuwa murmushi nayi na kar6i number Ina cewa yauwa nagode fa ,sannan na futa a game din Ina me kwashe number dake takardan zuwa waya ta ,sallama naji anyi daga gefe na amsa batare da na d'ago kainaba naji mutumin dayake sallamar yana cewa da allah in bazaku damuba zan ajiye mota aciki ne pls na d'ago kaina na dubeshi sannan nakai ga kallon motar da murfin ta yake bud'e alamar shine yafuta aciki yabarta ahaka ,na bud'e d'an qaramin bakina da muryata me sanyi nace ok ban minti kad'an nagama abunda nakeyi .
ya juya yana me mamakin gadara na da karfin hali irintawa lallai yarin yarnan bak'uwace batasan gun ajiye motar wayeba shiyasa tayi har ya isa gun motar su yana maganar zuci ,ya dubi abokin nasa dayacika yayi fam yace man wai mubata mintoti ta gama abunda takeyi .....fittttt yafuta amotar yayi dai-dai nima na gama abunda zanyi awayata na dubi yanda suke yakuwa gallamin wata uwar harara
tare da karasowa gurina ya hankad'ani gefe ya zuya azuciye mamaki ne ya kamani Amma ganin banson nayi dare yasani juya bayana don na shiga motar har na kama murfin zan bud'e zuciya ta ciyoni na juyo a fusace nace
" kai d'an tsurutt "
d'aga ma security bakin gate hannu naga yayi cikin sauri security ya iso ya rusuna mishi yamishi maganar da bansan me yaceba na juya kaina gefe nakuma k'i shiga motar Ina tsaye direba kam yana ciki yana jiran nashiga mu tafi ,duk'awa wannan gayen naga yayi yana magana ma Wanda yake zaune a mazaunin direban can senaga ya kashe motar ya fito suka nufi cikin ma'ikatar,na bud'e baki nace solo6iyo kawai be iya komaiba se d'acin rai,be kulaniba sedai daganin sa zakasan k'iris yake jira. kama murfin motar nayi zan shiga kenan senaga wannan security d'azun shida wasu maza su biyar sun nufo motar mu dazuwa suka fara kunce tayoyin motar direba dayaji ana tab'a masa mota ya lek'o dakansa ta window yana ganin b'arnar da ake masa cikin sauri ya fito yana name cewa lafiya zakuzo kunamin ta'adi ?babu Wanda ya kulashi ,cikin tashin hankali direban ya sake duban mutanan wai baku jinane kunata min asara amma ana muku magana kunki ku bari ,wanine daga cikin mutanan ya dubeshi yace ai wannan me sauki oga yabada aiki amaka domin duk Wanda tsautsayi yasa yayi parking a gurin ajiyan motar oga to cikin biyu za'ayi d'aya ko a cire tayoyin kokuma acire engine motar ,kuma karkace in ancire barmaka za'ayi a'a wannan tazama ganima domin namune mu masu cirewa .
na dubesu cikin kunar rai nace wai kunata oga oga !waye ogan kuma shi waye da har yake da wannan ikon d'aukar alhakin bayin Allah haka?au bakima sanshiba? cewar wani daga cikin su ,banza namishi yace me wancen motar shine ogan wannan kamfanin ,kuma shi yabamu umurni yin hakan,raina yagama b'aci ga mai mota se rok'onsu yakeyi su taimaka masa su bari zai futarda motar daga gun, wllh allah ba mota na bane kuji tausayina banida ko sisi ku tai makeni dan Allah,amma ko kulashi basuyiba suka gama cire wa sukaje suka samo wata mota mai irin k'ugiya medaukar container tazo tajanye motar me kayana tafutar mana waje me mota se rok'onsu yakeyi yana hawaye amma Sam sunki kulashi suka juya suka koma ciki.na dubi me motar yaban tausayi matuqa nace yanzu in za'a gyara motar nan kana ganin zatakai nawa?ya duben wllh hajiya ban saniba domin ban tab'a jan motar ba tsau tsayi yakaini ga karb'an motar matar nan gashi matar wllh batasan tsautsayi ba ,nace masa kashare hawayenka ka je tashar ku ka tambayi yanda ake saida tayar sannan seka zo muje, "hajiya me zakiyi agurin?"
Kai dai jeka kawai ka zo ,jiki na rawa ya nufi tasharsu can bai d'auki lokaci ba segashi ya dawo cikin sauri hajiya sunce tanan bayama ana siyarwa,ok muje gurin mugani ,mun isa gurin masu sayarda taya nace yagaya musu irin tayar da za'a Sanya ma motarshi ya gaya musu ,akayi lissafi na biyasu kudinsu na ce don Allah ko sunada Wanda yake Sanya tayar kwararre ?sukace akwai suka had'a mu da me sawa mukaje mesawa yafara aikinsa me mota kuwa al'jabine ya kamashi tare kuma da zullumin tayaya zai biyani kudin ,aka gama Sanya mana tayan na dubi me gyaran nace pls mud'an je daga can mana ,mukayi gaba na dubeshi nace aiki zakamin naga kanada saurin aiki zamu shiga can ma'aikatar duk motar dakaga na tab'a da hannuna to itace motar da zakamin aiki akanta zan biyaka yace angama, na dubi direba nace ka Sanya motar daga can tabar kan hanya barin karbo abu na dawo ,mukayi cikin company allah ya taimakemu k'afa ta d'auke na tsaya daga sarari shikuma ya dukufa aikinsa nan danan yayi ya gama muka futa ,na biyashi hakkinsa namasa godiya sannan nashiga mota nacema direban motar kayana dan Allah inason kaje kajamin hankalin security hanaklinsa yabar kan get ,muka nufi get din ni nayi cikin company shikuma ya tsaya agun security suna hira can security ya dubi abokin hiransa yace da Allah tunda kana nan kafun ta futo kad'an rikemin na zaga bayi mana ,yace babu komai seka futo ,da cigewarsa direban ya tawo yanda nake tsaye ya gayamin yace barinje na duba laida ta waje domin mu rufe wancan cameran nace kaga ni hankalina ma beje gurinva Ina tsaye harya dawo ya karaso guna yace nagama na nuna masa abun da zai kwashemin muka futo cikin sauri mukayi tafiyar mu .
07052100719.
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Fiksi UmumLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...
