Chapter 37

483 51 0
                                        

*💫⭐SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION💫⭐* 

'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''

*💍CIKAKKIYAR MACE💍*

✍🏻 Real Rashida Bature

PAGE3️⃣6️⃣
wani irin kallo amjaad yayi mata ,cikin b'acin rai ta bud'e baki zatayi magana ,sekuma tayi shiru ta juya tayi d'akinta .

wayarta ta d'auka tareda danna Kira ma number jamcy ,bugu biyu ta d'aga,rai bace rumana tace wallahi zanyi b'arna agidannan ,Allah nakusa aika yarinyar nan lahira ,zankashe ta fa!!!tayi maganar cikin karfi .

relax kawata mubi komai asannu ,ni dadina dake gajen hakuri,bakibin komai ahankali,ke kinfison sha yanzu magani yanzu ,kinkuma fi kowa sanin taurin kan mijinki .mtsss rumana taja wani dogon tsaki tareda cewa waya gayamiki yanzu dashi nake magana ?

ok inba dashi kikeyiba keda waye ? jamcy ta bukata .

dawa kuwa zakijini inba da wannan aljanar ba me suffan jinnu ,dafari kamar zabiya , tofa yanzu wannan kamannin duk ita khubra ne dasu?

tsaki rumana takumayi tace matsalata dake kenan , sorry kawas yanzu gayamin meya hadaki da ita don musamo mafita ?
kaf rumana ta kwashe yanda mukayi da ita ta zayyana ma jamcy ,shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace, agaskiya rumana kina bani mamaki gaki dai kece babba amma yarinyar nan seta kwace girman ,taya tafiki wayo da sanin kan namiji ,kina gani azahiri itakeda miji ,kekuma kece da hauka ,ki duba kigani tasan tayi miki lakwas agaban shi yanda duk inda yaje yanacan yana tausaya mata tareda tunaninta don yasan myb ke kinan kin daga mata hankali yanda bini bini zai ringa kiranta yanajin yaya take awani hali take ,don haka zama beganmu ba zan shigo anjima don sanin minene madafa ,ajiyan zuciya rumana ta sauke tareda cewa sekinshigo ta kashe wayar tareda cillawa gefe tamkar shiyayi mata laifin.

"cikin takunsa na isa ya nufi d'akin shi bai jimaba ya futo yanufi mota yanda yabar safwan yana jiranshi , jingina yayi da jikin motar tareda ciro wayarshi a aljiwu yana dannawa.

futowa safwan yayi daga cikin motar yace yaya dai man?

"mtssss tsaki amjaad yaja yana me gyara tsayuwar shi batare da yayi magana ba,sanda ya d'auki lokaci kafun yace mushiga part d'in hajiya inaga acan zamu samu abinci .

dubanshi safwan yayi yace matan ka basuyi bane ?

tafiya yafarayi tare da cewa inka gama surutun seka shigo ciki .

zaune nake acikin bedroom dina Ina nazarin sabon salon da rumana ta b'ullo dashi,nisawa nayi tareda jan numfashi,mikewa nayi na nafi gurin wardrobe d'ina na d'auko wani lace black se zaren jikinshi red riga da skirt ne dinki yafita sosai don kwararren telane yayi min   yana daga kicin kayan da amjaad yayimin akan na hidiman bikinshi ,gaban mirror na dawo bayan nagama Sanya kayan , light make up nayima fuskata na d'aura dan kwalin nayi d'aurin ture kaga tsiya Wanda yanzu yazama d'aurin zamani ,take fuskata tafito nayi cas kamar ka saceni kagudu gawani irin fari dana karayi na samun hutu da sauyin guri da zama guri d'aya,ga cima mekyau , had'e da mayuka masu inganci , jikina ya murje nayi bul bul dani ,sake kallon kaina nayi a madubi naga komai yaji zam zam nayi wani irin murmushi wanda ni kad'ai ne nasan ma'anar hakan.
main falo nanufa cikin tafiyata kamar wacce akama dole ga sassan jikina suna kad'awa.

      "kwas! kwas!!

sautin da takalmina suke bayar wa kenan , duk da plat shoe's ne amma yana bada amon sauti me janyo hankalin kishiya ,yanzuma hakane don idon rumana yana kan k'ofar sashina,tunda taga dosowa na taja wani dogon tsaki tareda hard'e k'afa tana danna wayarta, akai kaice tace aikin banza da bamusan asalin mutum bane seyace ubansa shugaban  k'asane , direct kan dinning na nufa don ajiye plate din hannuna ,ajiyewa nayi tareda dawowa na zauna akan d'aya daga cikin kujerun falon,zamana yayi dai dai da dawowar amjaad gidan ,bakinshi d'auke da sallama ,amsawa nayi tareda mik'ewa na isa gurinshi,hannu ya bud'e min ,nashiga jikinsa atare muka sauke ajiyar zuciya cikin salo nace sannu da dawowa hubby,bai amsamin ba se shinshina min wuya dayakeyi, na janye jikina iname karban jakar dayake rataye a kafad'ar sa ,na juya na nufi sama ,akan side lamp drowa na ajiye mishi, tareda shiga bathroom na had'a mishi ruwan wanka ,nafito na iskeshi abakin gado yana cire takalman shi ,karasawa nayi na tattare takalman na kawar dasu na ajiye agurin daya kamata, nace ruwanka yana jiranka , d'ago kaiyayi kamar zaiyi magana sekuma yacigaba da balle maballin rigansa ,mikewa yayi tareda kamoni yace yau Sam banijin dad'in jikina don haka a taimakamin atayani wankan,ganin yanayinshi ne yasani yin hanyar bathroom din batareda nace komaiba ,sanda yagama jagulani sannan mukayi wankan muka fito daure da towel ajikina, manshi na shafa agurin shafa man ma seda yagama latsani ,Ina kaucewa amma shi sam naga alama so yakeyi yayi babbar harka ,ganin danayi dagaske fa abukace yake yasani saduda, don ta wannan fannin amjaad Sam bayida hakuri , haka nabiye mishi muka biya buk'atar junanmu kafun muka sake wankar tsarki ,na fito na iske amjaad harya  Sanya kayanshi yace baby yunwa nakeji a taimakamin da abinci kar yunwa yamin illah, juyowa nayi nace sorry baby barin busar da kaina semuje falo ko nan zankawoma ? kafad'a ya d'aga yace nifa bazan iya jiranki harse kin gamaba don haka kizo muje kiban inyaso seki dawo kicigaba da gyara kankin , ganin danayi da gaske fa yakeyi yasani ajiye hand dryer din na sake gashin a bayana nace to muje inyaso Sena dawo na k'arasa.

tunda muka fara saukowa rumana ta tsaremu da idonta har mukazo muka wuceta , direct kan dinning mukaje na zuba mishi sinasir da miyar ganye ,tareda juice din kwakwa Wanda yaketa tashin qamshi,.

kaina naji an damka ,don haka yasani juyowa da sauri Ina kallon rumana Wanda tsabar masifan dayake cinta har fuskarta yayi ja ,idonta sunyi kananun masifa tace uban me kukayi ad'akin dahar kika jiko kankin?

wani takaici ne ya lullubeni ,cikin zafun nama na buge hannunta ,Ina me nunata da yatsa nace wannan haukankin  yazama na k'arshe da zakiyi gigin Sanya wannan banzar hannunkin ajikina ,wani damka tasake kawo wa gashina tace wallahi sekun gayamin abunda kukayi har kika jika kanki ,ban bari hannunta ya kawo jikinaba na goce, amjaad wandake zaune tamkar bayi gurin ya d'ago kanshi yana mata wannan kallon shi daya zame mishi jiki yace haukanki harya Kai haka ashe bansaniba ,kanshi ta dawo da masifar kamar wance dama take jirance dashi ,tace kace hakan mana tsohon munafiki,tunda ka gama  tsare yar cikinka a d'aki ka sauke mata nauyinka ai dole kafito kana muzurai ma mutane , to wallahi baka isaba ,sabida kamaidani wawiya ka shanyani anan Kai kaje kana baje karfinka akan yarinya karama kai ko kunya bakaji ?
to wallahi zakaga hauka yau ,inhar ya tabbata kwanciya kayi da ita .

dubanta yayi yace wai ke me kike nufi ne dani?

banza tamishi tana kad'a jikinta .tsaki naja tareda mik'ewa nafara sauka daga step din dinning ban kaiga karasawaba rumana tayiyo kaina zata sake kamomin gashin kaina na kauce ji kikeyi tiiiiim! ta goce daga steps din na tsallaketa nayi tafiyata , amjaad tsaki yaja yace kin had'a kanki da wahala .....

Pls kuyi hakuri da wannan ba yawa nayi ne kawai don karkujini shiru Ina hidma ne sis dina ta haihu amma alhamdulillah anyi suna lpia angama taro nagode sosai da kulawanku damasu kirana damasu yimin magana ta PC damasu yimin magana ta group nagode da kaunar ku gareni Allah ya shirya mana zuriya.

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now