*💫⭐SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION💫⭐*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature~wannan page din takice~ *ta annabi* ~ina godiya ga kulawarki~
PAGE3️⃣8️⃣
bayan na ajiye keys d'in da amjaad ya damk'amin na motocina ,himar na d'auko kalan kayan jikina sedai bashi da girma sosai ,rufe k'ofar falon nayi tareda nufan cikin gida, falon hajiya nafara shiga tareda yin sallama ,ban iske kowa afalon ba don haka direct kitchen d'inta na nufa ,iyami me girkinta na samu tana gyara kitchen d'in,cikin mutum tawa ta gaisheni duk da ta girmemin hakan bashi yasa ta jira sena gaishetaba ,ni hakan ma kunya yake bani ,dubanta nayi nace hajiya fa?tace tana d'aki ta d'an kwanta don tasha magani me karfi ne ,ok to barinje sashin mom kafin ta farka senazo na dubata ,shiga cikin kitchen d'in nayi na dudduba abunda nake nema danaga ban gani bane na futo .
sashin mom nashiga d'auke da sallama abakina don shiga guri da sallama yariga da ya bini ne inzan shiga guri senayi sallama nan,kallon falon na tsayayi kamar yaune ganina na farko ,babu kowa aciki se tv dayake aiki shi kad'ai ,don haka kitchen na nufa na fara duba abunda nake nema ,akayi sa'a kuwa kaf abunda nake nema akwai don haka na fuffuto dashi na zuba akan kitchen cabinet din gun ,Ina ƙoƙarin wanke hannuna ne naji motsi a kofar shigowa kitchen din na juya don ganin waye .
a'a daughter kece a kitchen ?
"mom antashi lpia?
na durkusa Ina gaisheta tareda cewa nashigo banganki a falo bane nayi tunanin ko kin koma barci ne ,kuma banson naje na tada ke ,shine na shigo nan neman rabi me girkinki na tarar itama bata nan .Ey nina aiketa ,nima motsi naji yasani karasowa kitchen d'in don nasan baici ace har ta dawo daga aiken dana mata ba .
kaina a sunkuye muke maganar don Ina matukar girmama mom inajin nauyinta sosai.
daughter ko kinason wani abunne naga kin fito da kaya waje?
kaina dad'a sunkuyarwa nace mom yunwa nakeji sosai kamar zan fad'i don har jiri nake gani ,amma inna girka abu bayamin dad'i ne ,kuma abunda nakeson ci babu a kitchen d'inmu shine nazo nema anan ko zan samu se rabi ta tayani mugirka .
k'arasowa mom tayi ta kamani tare da cewa subhanallahi,kuma son yasani shine don rashin hankali yabarki haka?
memakon yazo ya gayamin inyaso koni da kaina Sena girka miki,ta kama hannuna muka nufi falo ta zaunar dani ,itama ta zauna tace karki biye ma son inkinason abu kizo ki gayamin ni zan miki dakaina ,inma bazaki iya zuwaba maza kirani a waya banison wannan gangancin kun ,yanzu gayamin me kikeso kici nafara girka miki kafun rabi ta dawo don bazai yiyu ki zauna da yunwa ba .
baki na bud'e dakyar don jirin danakeji ,kwana biyun nan haka nake wuni da jiri ,nace mom dankalin hausa zanci da mai da yaji ,se d'anwake da mai da yaji ,se taliyar murji da manja da yaji se Lipton.
murmushi mom tayi Wanda ban gane ma'anar hakanba tace to kekuma salon dayazo dashi kenan , to mashà Allah yanzu kuwa zakici duk wannan abun dakika lissafo,anyi sa'a kuwa duk munadashi ,barin d'aura miki kwanta abinki ,mom barinzo na tayaki tunda dayawa ,no daughter yi zaman ki ,in kuma kwanciya zakiyi ki tafi sama d'akina Kona sateera ki kwanta acan kafin na dafa miki,kaina na girgiza nace barin zauna anan ma nagode mom.
nidai bansan ya akayiba se farkawa nayi naga mom zaune akusa dani sateera ma tana gefe .
mom tace daughter kin tashi ?
kaina gyad'a mata batareda nayi magana ba,tace sateera kamata kuje d'akin ki ta wanke bakinta ku sauko taci abincinta .
komai dana b'ukata mom ta girkamin jikina har rawa yakeyi ganin abincin danake ta kwadayi samu tsawan kwana biyar ban samu ci ba ,wani yawu ne na had'iye muk'utttt ina gyara bakina donjin wani yawu daya tarumin ,sateera ne ta sa dariya tareda cewa matar bros Ina zakikai wannan abincin haka?
ko sauraranta banyiba nafara zuba yaji akan d'an waken, bisimillah nayi nafara ci ina lumshe idona don dad'in dayamin ,tas na cinye d'anwaken ,don d'an dai dai mom tamin , plate din taliyar na janyo shima na bud'eshi da yaji na fara ci seda naci rabi kafun na kawar gefe na janyo dankalin hausa na fara dangwalan mai Sena dangwali yaji naci,baki sateera ta bud'e tareda tsareni da ido tace matar bros anya kuwa lpia kike?keda baki wani cin abinci amma kiduba kiga irin lodin dakikeyi yau, gaskiya mom akira doctor kar abincin yafasa mata ciki.
dak'uwa mom tayi mata tace kinci gidanku,ai lafiya ke kawo ci ,kema fa da bakinki kince da bataci , to yanzu alhamdulillah ta samu lafiya tadawo cin abunta seki barmin daughter taci tunda dai da akwai abincin.
but mom !abincin kamar yayi yawa ga azababban yaji datakeci ko tunanin ulcer batayi ,hannuna na tsame daga dankalin na janyo cup din Lipton dina danake kurba ahankali na k'arasa sauran daya yarege aciki na ajiye cup din tareda cewa alhamdulillah,seda na gama na d'ago kainà Ina duban sateera nace kikace me?
mom ne tace rabu da shiriritan sateera maza tashi ki wanko hannunki da bakinki kizo ki zauna ki huta , ahankali na mike nanufi kitchen na wanko hannun kamar yanda mom tace , falon na dawo na zauna akan kujera najigina bayana ajikin fillow kujeran ina maida numfashi kamar wacce nayi tsere ,ni wannan abu yana damuna a yan kwanakin nan ,sannu mom tamin tana me gyara min dan kwalin kaina , sateera ta fashe da dariya tareda cewa ai dole anty kufcy kiyi numfashi irin wannan abinci dakika narka ma cikinki,innice ma Allah bazan iya tashiba ,harara mom tayi mata tareda cewa Allah yashiryeki da wannan surutunkin ,maza tashi ki kara mata karfin ac ko zataji dad'in jikinta .
ido na lumshe don wani irin barcine yake lalub'ana me k'arfin gaske,na bude idon nace mom barci nakeji ,tace kuma !! da dai kin daure ki zauna zuwa anjima abincin ya fad'a Miki sekiyi barcin,kaina na d'aga mata,tareda sake rufe idona .
lura datayi nayi barci nane agun yasa ta d'an girgiza ni tace tashi ki shiga d'akina ki kwanta ,mikewa nayi sateera tace matar bros muje d'akina kiyi barcin,bank'iba don acan zanfi sakewa ,tare mukaje d'akin da ita na kwanta ta gyaramin bargo tareda kashemin wutar d'akin ,ta kunna ac sannan ta jamin k'ofa tafita ,nan dana barci me nauyi yayi gaba dani..

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Narrativa generaleLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...