Chapter 18

448 47 0
                                    

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍️ Real Rashida Bature.

PAGE 1️⃣7️⃣
Ummm jinan rabe kace sujirani na fito maza koma bakin aikinka karsu salwantar maka da aiki son kasan halin qamshi tas zata iya baka wutu don ba mutanan nan bane suka dauke ka aiki bare suta juyaka to shikenan hajiya nabarki lafiya.

Amjaad ne ya dubi safwan yace wallahi kanada matsala tunda ance babu abunnan to mezaisa mu tsaya kaida ga ganin gurinnan aikaima kasan karya ne ba wani abun arzik'i dazasuyi ni wallahi na rasa irin kwashe kwashe hajiya ace duk cikin garin bauchi babu kajin da takeso se anzo har buzaye saboda namen magana mtssss tunda ta nace sedai take aiko direban Amma nikam badani za'a ake wannan wahalarba ka gidajen gona Wanda suka amsa sunansu acikin gari amma wai duk basu mataba shiiiii gashinan tawowa please cewar safwan,rabe ya karaso ya dan rusuna alamar girmamawa yace hajiya kaka tace bari tazo tayi muku bayani dakanta to shikenan mungode fa safwan ya amsa mishi shikuwa amjaad ko kallon yanda yake baiyiba sema dad'a kau dakai yayi domin gaba d'aya takaicinsu yakeji ,mtsss kaji wata sabuwar matsalar inji amjaad safwan dai be kulashiba shima bai sake magana ba sema kwantar da kujeran motar dayayi ya kwanta tareda lumshe idonsa.

            ****
Hajiya kaka leka dakin khubra tayi taga se juyi take tana ruk'e ciki ga jikinta yayi zafi sosai tace oh ni yasu yau Ina ganin jarabawa falo ta fito batare da ta d'auki mayafi ba ta nufi gidan gona tana salati tareda hawaye don tsofi abu kadanne zaisanyasu kuka na macewa jama'a waishin kuna inane ku taimaka ku kiramin jamilu a wayoyinku kuce duk abunda yakeyi yayi maza yadawo gida khubra ra zata mutu wayyo ni Allah safwan ne yayi saurin karasawa kusa da ita yace kaka lafiya kike kuka kiyi hakuri juyowa kakus tayi tace inafa lafiya d'annan jikata zata mutu tasake fashewa dakuka subhanallah miya sameta haka tana inakuma ?daga ciwon ciki fa ta fara yanzu abu yana neman ya zama ciwo ajali ya Allah ka sassauta ma wannan marainiyar ta juyo tace zaku kiramin jamilu ko se jikana ta mutu don na fahimci daman kadan kuke jira kuci gado ta sake fashewa da kuka kaka me zai hana akaita asibiti inyaso se a dubata asan menene matsalar nima kaga abunda nakeson nayi kenan yanzu na futo akiramin ubanta duk da batason akaita asibiti amma nikam sedai ta yafen ban shirya ganin gawanta ba haka zan daure na saba maganar ta na kaita tanayi tana matsar kwalla kaka muje ku futo da ita tunda da mota muke Sena kaiku asibitin to shikenan ma tazo da sauki ta nufi cikin gidan ita dasu siyama tace suzo sukama mata ita inata jujjuyawa don cikina yanata murd'a min ga tsananin ciwon mara don marata ya rike kam na tabbata ko iya takawa bazanyi ba ga zogin dayake min muryan hajiya kaka naji sannu khubra allah yabaki lpia ki daure muje asibiti ko da abunda zasu miki kisamu lafiya ,ni Allah kaka bazan jeba sufa da anje sesu farama mutum allura nidai o'o tana maganar tana b'ata fuska don tsananin ciwon mara hakuri fa zakiyi khubra shine kawai hanyan daya rage mana nidai o'o tayi maganar tana runtse ido don ko kad'an batason yin maganar .

Safwan ne ya k'arasa motar su ya dubi amjaad Wanda yayi tamkar beji abunda yake wakana agunba haba amjaad kanajin matar nan tanacewa jikanta ba lafiya amma kayi burus abunka ai ka leko da kanka ka jajan ta mata hakan ba kyau
"inace kai kamata jajen ? shiru yamasa bai bashi amsaba yana kwancen bai kuma bude ido ba yace anmaka bayanin kajin ne kokuwa har yanzu zaman jira mukeyi mtssss wasu kaji ana maka bayanin me kajin ne akecewa ba lafiya zata mutu kake wani magana kirjinshi ne yaji tayi wani mummunan bugawa ya bud'e idonshi yana me duban safwan amma seya danne abunda yakeji a kirjinsa
don kar safwan ya fahimta 

      "wa kenan?""

wakuwa inbanda qamshi ,tsaki yaja tare da sake runtse idonsa ya koma ya kwanta shiru shiru baiga sun fitoba ya bud'e idonsa ya juya ya tsurama hanyar da zai kaika gurin kakus ido kamar maison ganin wani abun, bunde motar yayi yanufi cikin gidan kakus kanshi tsaye yashiga falon tareda siririyar sallama shiru falon ba kowa don haka ya k'arasa shiga cikin falon magana yake jiyowa tawata kofa don haka ya nufi kofar yayi dai dai da kakus takecewa iya gatan dazan Miki kenan khubra nakaiki asibiti asubamin ke aga meke damunki ki daure kiyi hakuri muje kinji jikallena o'o nifa kaka bazaniba labulen d'akin ya fude tareda daka mata tsawa kintashi kinfito kosena zo gurin na b'abb'ala Miki kafafuwa ana lallabaki kina wani manar baza zaki tashi kokuwa? d'ago kaina nayi nadubeshi naga niya kafe da idonsa me ban tsoro ƙoƙarin mikewa nakeyi Wanda ban shirya mayin hakanba don wallahi gaba d'aya tsoronsa ne ya kamani ganin fuskarsa babu alamun rahma mikewa nakesonyi amma na kasa ganin hakane yasa siyama da zahra kanne na suka matso suka kamani donna samu na mike ,tsawa ya dakamusu Wanda dukanmu sanda muka furgita kun matsa agun ko kuwa ,kekuma kiyarda na iso furin baki taso kin wuce kinfito ba kigani wani marayan kuka nasa Ina Mika ma hajiya kaka hannuna cikin muryata dabata futa sosai kaka bazan iya tafiya ba kuma ni banson naje ki gaya mashi banison zuwa nayi maganar Ina me zubo da hawaye kan fuskata yana had'uwa da gumin zufan dana had'a, kauda Kai yayi tareda sake karamar tsaki ya nufoni hanu na fara yarfewa ina mikama kaka zuwa yayi bakin gadon ya tsuguna ya ciccibeni yayi waje dani kaka da su siyama bayanmu suka biyo har wajan mota safwan ne yayi saurin bud'e bayan mota ya sanyani ya koma gaba ya shiga kaka ta dubi siyama tace ki koma ki kulamin da d'akina in ubanku ya dawo kice yaron alhaji majeed ne ya kaimu asibiti ya kiramu inyaso seya biyo bayan mu , sannan tashiga motar safwan ya tayar suka d'auki hanya tafiyar befi minti goma ba muka muka isa wata privet hospital faka motar yayi a haraban asibitin sannan ya futo ya bud'e mana kaka ne ta futo tana ruk'e da hannuna na Sanya kafa na sauko amma in daga kafa abun bayi yuwuwa don marana ya d'aure runtse ido nayi Ina ruke da hannun kaka wacce se jeromin sannu takeyi , bud'e k'ofar yanda yake yayi ya futo jinayi yace kaka dan matsa tace to tareda matsawa gefe nidai idona yana rufe jina nayi andagani cak tareda nufan cikin asibitin be direni a ko inaba se adakin doctor don haka safwan ne ya tsaya ya budemin file tareda tambayan kaka sunana da na mahaifi na da wasu tambayoyi da za'a cike file din sannan suka nufo d'akin da amjaad yashiga sun tarar dashi suna magana da doctor din da alamun sanayya atsakanin su hannu safwan ya mika ma doctor tareda cewa a doctor kabir ashe kama gari da naso kiranka senayi tunanin ko baka gari shiyasa kawai muka tawo batareda mun kiraka ba ayya wallahi inanan dis week dinnnan madam ta rukeni ban je ko inaba me yasamu kanwar tamu yayi tambayar yana me dubana ,kallon su amjaad nayi Ina turo baki doctor daya lura yace kozaku dan bamu waje ne ? yayi maganar yana dubansu amjaad , safwan ne ya nufi kofa don futa amjaad kam gyara zama yayi tareda kada fansa alamar bemasan munayiba ,kakane tace daga ciwon ciki semukaga abun yanata yin gaba dubana yayi yace sannu yan mata mekikeji yanzu ,na bud'e baki cikin murya me sanyi tareda wahalar ciwo nace ciwon ciki se marata da bani ko iya daga kafata ga zazzabi se amai duk abaunda na fad'a idonsa nakan file dina yana rubutawa sannan ya d'ago ido ya duben yace hau kan wancan gadon ya nunamin gadon dayake gefensa acikin d'akin dubansa nayi nace bazan iya tafiyaba Ina yamutsa fuska ,kaka ne ta taso zata kamàni yace barshi kaka barin kaita nadai banso kaka ki kamani zanje d'ane bakina yayi tare da daukata ya d'aura ni akan gadon da doctor yace tashi doctor yayi yasanya hand globe ya tawo bakin gadon yace nunamin dai dai yanda yake miki ciwon amarci dakuma cikin nuna mishi nayi ya Kai hannu zai daura acikina yace wai miye haka kake shirinyi ne ?kaine zaka taba ta duk asibitin babu mace ne se kaine zaka tabata yayi maganar tareda ysareshi da lumsassun idonsa juyowa doctor yayi don yasan za'ayi haka yayi mamakinma tunda ya shigo yaga shine baice komaiba bayan gaisuwa ,juyowa yayi ya isa bakin table dinsa ya d'auki waya yasanya wasu lambobi zuwacan naji yace please danzo ki dubamin wata ya ajiye wayar ba'a dauki lokaciba aka turo kofar wata matace me kiba ta dan girma ta shigo da sallama doctor kabir yace yauwa doctor zainab da allah dubamin ita juyowa tayi ta duben ta juya tadubi sauran ta ce mama barka da rana kaka tace yauwa yar nan ta gaida amjaad ga dukkan alamu sun sanshi amsa mata yayi batare da ya dubetaba ta nufo gadon danake tace meke damunki nace ciwon ciki se mara da amai ,kinajin zazzabi ne Kai na daga mata alamar ey doctor kabir duk yana jinmu don daga gun zaikejin komai seya san matsalar ga dukkan alamu sun saba hakan ga maza masu tsastsauran ra'ayi, danna marana tayi wani wahallan kara nasa tareda ruke hannunta wayyo doctor don Allah ki bari zai futa marana hannuna ta daga tareda cigaba da danna cikina kuka nasanya Ina kaka ki hanata cikina sannu khubra lpia ake nema Miki kiyi hakuri yanzu za'a gama haka tata dannamin marar tanayi Ina ruketa juyowa tayi tace ma doctor menstruation ne table gabansa ta nufa ta d'auki allura da sirinji ta hada allura tazo tace to gyara namiki ido na futar waje nafara yarfe hannu inacewa kaka nidai kar amin allura zanji sauki tazo zatamin na mirgina tace kaka wannan jikan takifa bazata tsaya amata ba ko zaki taimaka ki rikemin ita to barin riketan zauna kaka abunki karta tsaya tagani yana me watsamin wani kallo tsayuwa nayi tare da kamkame jikina daya b'ari relax jikan kaka ki saki jikinki inba hakaba alluran zai karye ajikinki to nace tareda runtse ido tana sawa na callara kuka kamar wata k'aramar yarinya harara ya watsamin Wanda bansan yanayi ba harta cire bansan ta cireba tace to gyara angama take kuma naji marar ta sake sannan tace koma kujera ki zauna , ahankali nake takowa harna iso kujeran dana tashi Wanda take kusa dana doctor magani ra rubuta min tareda cewa zaki iya ganin jinin yazo akowani lokaci ai kina lissafi ?Kai na kadaga masa don ba karamin kunya nakejiba komai agaban sa akayi sabida tsabar nacinsa hararansa nayi Ina me turo bakina muka futo muka samu safwan a reception yana jiran futowar mu dubana yayi Ina d'ingisawa hajiya kaka tana ruk'e da hannuna yace sannu khubra allah yakara sauki amiin nace Ina kwantar da kaina a kafad'ar kakus harara amjaad yayi tare da wucemu ya isa gurin motar mu bud'e mana safwan yayi muka shiga ya bar mana kofar motar ya rufe  tareda zagawa yashiga ciki muka kama hanyar komawa ,tsayuwa yayi awata babban pharmacy futa safwan yayi bai jima sosai ba ya dawo dauke da leda a hannunshi yashiga moka tafi mun iso dai dai titin bauchi club ya tsaya a hisan me gashin kifi daka biyo layinma wani daddad'an kamshi ne zaima maraba tsayuwa yayi sannan yafuta shikam dan mulkin yana kacare agaba se dannan waya kawai yakeyi suna dan hira da kakus jefi jefi har safwan ya dawo yatada motar mukayi gaba kakus tace ikon Allah jad kaji kuwa me naji yace a'a kaka sekin fad'a tace kaga ikon Allah shikuma wannan anguwa dakashigo se wani kamahi ne zai taryeka Allah me hukunci  murmusawa yayi safwan yace haladai shima anguwar yaji zuwan takwararsa qamshi ne shiyasa yatada nashi amshi aikuwa zai iya yuwuwa ahaka hira ta barke tsakanin sa da kakus harmuka iso gida da taimakon kaka na futo a motar tana rike da hannuna muka nufi cikin gida safwan yabiyo bayanmu da ledar danaga yayi sayayya ahaka muka isa falon hajiya ta zaunar dani akan daya daga cikin kujerun falon.

Rashows ce
07052100719.

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now