💍 CIKAKKIYAR MACE💍
✍️ Real Rashida Bature.
PAGE4️⃣
Da hanzari na dawo falon alhajimu nasamu harya fara karyawa yana kurb'an ruwan tea ahankali.nayi sallama yabani izini nashiga na nemi gefe na zauna"yaduben yace yaya dai khubra koda matsala ne"?
nace a'a daman baba nazone domin deman alfarma,don Allah baba karkace a'a ni ko aro kaban daga baya sena biyaka kud'in .inajinki cigaba cewar bqba alhaji.daman so nakeyi ka bani filin dayake bayan mu saboda dakin kajin bazai minba innace kajin zan kara .
to inbanda abunki khubra yaushe hakan zai yiyu kina gida kaji suna wani gurin dabam ?
ai inaganin hakan kamar kasada ne .baba alhaji ba kasada bane nagama tsara yanda zanyi Wanda ko cikin dare nakeson shiga gun zan shiga batare dana wani damuwa ba nidai amin cewar ka kawai nake so .
Shiru baba alhaji yayi zuwa can yace to nidai bazan ce zan hanakiba amma bazan bakiba har senaji tsarinki tukum.gyara zama nayi nace alhaji ka yarda dani zan nemo masu tsara gini nagaya musu yanda zasu fitarmin Kai da kanka zakayi mamakin hakan dan zan futarda yanda zan iya shiga tanan base na zagaya ta wajeba sannan tawaje kuma za'a sanyamin gate amin karamin kofa saboda masu zuwa kaga base sun shigo nanba sannan zamuyi komai nida masu sayan kayana acikin sirri su sayi bunda sukeso su tafi anfanin gate kuma shine motar dazatana kawomin abincin kajin zata iya shiga har ciki ta saukemin base nabiya masu shigar min dashiba kuma shima zai zamo da sirri ba akofar gidaba .baba alhaji ya jinjina kai yace babu shakka kinyi dabara Allah yasa albarka yasa afara asa'a,amiin to Amma baba alhaji inda so samune Dan Allah ka aramin wasu kud'in don wannan bazai kaiba Amma wannan din aro zaka ban,to aikene da rigimarki kin debo abun da girma ,Amma zan duba nagani . yauwa my baba nagode Amma alhaji ka duba dawuri yau zan fara aiwatar da aiyukana nace cikin annushuwa da jin dadi don burina yakusa cika ,to naji adaibi ahankali cewar bqba alhaji,in sha Allah na miqe na nufi sashinmu na tarar har hajiya kaka tafito cikin shirinta taci kwalliya tayi ras da ita .Kai Kai Kai my kakus se Ina haka? lallai yanda zakije ba k'aramar guri bane irin wannan wanka se baza qamshi kikeyi ai seki sa mutanan gari sufara kiranki kema da qamshi gidan turare inayi ina dariya,mtss inkin gama surutun seki zo kiban abunda zanci don nagaji da jiranki ,kinmaci sa'a yau muna cikin farin ciki babu batun b'acin rai kuma ,nayi saurin shigewa bayi( toilet)domin yin wanka banjima acikiba sanin kakus na jirana nafito na shirya cikin doguwar riga na atamba me kalar baki da kore kalan yafito da hasken fata na nayi kyau acikin kayan ,na zuzzuba mana muka karya cikin farin ciki ,bayan mun gama na tattare kayan naje kitchen ta wanke kayan danayi amfani dashi na gyara gurin na fito na samu kakus nace kakus
"Albishirinki "
tace goro , to baba alhaji yabani filin bayannan ,Kai Amma Allah yamasa albarka yaushe kukayi hakan ? ta tambaya ,d'azu na tambayeshi na gaya mata kaf yanda mukayi dashi sannan kaka yanzu zan futa na je gidanzu kare na nemo janka ya gwada filin muji nawa ne zataci kud'in kewaye wajan.hakan ma nada kyau sedai ki lura da kyau don mutane yanzu tsoron Allah yamusu karanci karsu ganki ke macece suce zasu cuceki ,duk da nasan insukayi gigin cutar ki sun tsokalo makansu wuta bal bal ne .nayi dariya Ina me mikewa nashiga daki na fesa turaren mist Wanda nasaya d'ari hudu zuwana cikin garin bauchi ,na dauko hijab dina kalan kayana nafuto nace my kakus zan futa kimin addu'a allah ya daurani akan mugu ,hakane kam addu'a kam kullum acikin Miki nakeyi,kikuma tabbata kinyi addu'ar futa agida nace in sha Allah zanyi ,yauwa daman dazaran kin kirasu ki shigo ki kirani ayi komai agabana to shikenan hajjaju na .
*****************Tafiya kadan nayi ta bayan layin mu na hango su janka a kofar isiya me shago sun had'a majalisar su ,na nufi gurin su, tunkan na karaso suka mik'e Allah yatemaki qamshin duniya kina tafe qamshi nabinki takawarki lafiya yar alhaji jikan hajiya kaka, murmushi nayi Ina me d'aga musu hannu alamar na amsa gaisuwarsu ,na dubi janka nace in bazaka damuba inason kazo ka dubamun wani gurine kamin lissafin abunda zaici in zan iya sena bada aikin kamin ,amma zanso aikin cikin lokaci kalilan yana nufin zaka zuba yaranka suyi aikin babu dare ba rana .....ihuhu yar alhaji me abun mamaki harka dake akwai alkhairi cewar wani daga cikin yaran janka suna me sowa gaba d'ayansu janka ne ya daga musu hannu alamar suyi shiru yace wannan ba damuwa bane allah yasa zan iya don bazanso aikin ya kufce munba hajiya qamshi .na gyara tsayuwa nace indai kasassauta me zai hana na baka ,inda bazan bakaba ai bazan nemeka ba zaka iya biyoni muje kaga guri .fito yayi ma yaransa suka rufa mana baya nakaisu dai dai filin nace su tsaya agurin Ina zuwa .
cikin gida nashiga nqgaya ma kakus iso warmu mayafinta ta yafa kalan atamfar datake jikinta na dubeta Kai hajiyata Allah kinsan kan gayu irin ke kinyi tumach dinnan ko ,kedai allah ya gyara Miki bakinki baki ganin abu sekin tamka halan da so kikeyi nake futa kamar matan ubanki masusa riga dabqn zani daban , to akullum nakanso nayi shigar da za'a kalleni ace ay lallai naci sunana hajiya kaka wuce muje ,nabi bayanta Ina me dariya k'asa k'asa narufo mana kofarmu na bi bayanta muka futa.hajiya kaka ta duben to kimusu bayanin yanda kikeson tsarin yakasan ce,janka abunda nakeson kamin kaga daga can karshe zaka ciremin manyan holl guda biyar seka ciremin d'aki guda biyu, seka ciremin rumfa guda hud'u dab gate kaciremin d'aki guda d'aya ,zan shiga ciki saboda gurinnan rana yayi yawa duk abunda ake ciki seka gayamin muje hajjaju na ruke hannunta muka juya ta juyo tace to kudai ji tsoron Allah kuma "Yar marainiyata aiki me inganci don inbeyiba senasa an rushe sannna kusake sabo kuma bazata d'auki asaraba ,angama ranki ya dad'e cewar wani daga cikin yaran janka sannan yataba janka mutumina ta tafi fa,firgitttt janka yayi yasauke numfashi yana me cewa bazaka ganeba Sam yarinyar tayi ne wllh ga gadara kamar wata sarauniya .
cikin gida muka dawo hajiya kaka tanata me cewan nikuwa qamshi kamar filin bazai yiba nake gani ,na fito daga kitchen Ina me dauke da abun goge hannu saboda nayi amfani da ruwa na d'aura mana girkin rana , hajiya zaiyi inma beyiba Sena had'a dana gaba na se a Kara da nawa .
baki bude hajiya ta duben ey lallai kam !ai dole ki had'a tunda filin ubanki ne awani kud'in ne har zaki iya siyan na mutane?hmm hajjaju shiyasa nace ke "sam baki jaa"
abunda nakeso dake ki zuba ido kisha kallo yanda za'a futarmin da komai bisa tsarina hajiyata.assalamu alaikum ko hajiya qamshi me kwai tananan ?cewar yaron janka .
Wanene yake nemanta? cewar hajiya kaka.
Allah yaja da ran hajiya kaka megida ne yake nemanta awaje , to to kace gatanan zuwa .
inajin duk yanda sukayi na futo na nufi kitchen na sauke spaghetti dana d'aura najuye a kula sannan na koma daki na Sanya hijab na nufi kofar gida .
waton hajiya qamshi mungama gwadawa iyayin na wllh Sam filin yakasa se dai in za'a rage girman hall din.
No no no no !bazai yiyu arage komai ba ,yanda nakeso haka za'a amin tsarin don haka ku biyoni muje .
mun isa filin na dubi janka zanso ka sake gwadawa kashiga wancan filin ka d'ibi iya yanda zai isa .
Amma hajiy......na katseshi ta hanyar d'aga masa hannu ,banson jin maganar ka yanda nace haka za'amin,ka aika yaranka akiramin sallau me block yanxu .basu wani d'auki lokaci ba suka dawo tare da sallau me block,ya duqa "antashi lpia hajiya qamshi"?
lpia lw malam sallau ,janka pls gaya masa yawan block din da za'a yi amfani dashi ,sannan ka gayamin kudinsa muji.janka ya gayamasa sallau ya buga lissafi ya gayamin na dubi janka nace za'a fara aiki daga yau ,sannan duk Wanda ya tambayi me za'a yi anan ko mawa suke aiki banson abada bayanin komai kowa ya iya da bakinsa ,sannan sallau zan bada kudin block dinka yanxu Inna shiga gida,don haka kullum zaku ke aiko da block har kudinmu ya kare ,banikuma son dile yazama koda yaushe akwai ak'asa . godiya nake ranki ya dad'e ,zaka iya tafiya anjima inna koma gida seka zo ka karbi kudinka ,sannan na dawo da dubana kan janka inason kumin aiki me kyau duk da nasan aikinka Babu ha'inci amma akara dagewa ,nabar amanar komai gunka ,sannan Inna shiga zan futo maka da kudin aikin ku na yau zanyi waya saminu me siminti damasu kasa komai zuwa karfe biyu zaka sameshi anan ,seka nemi duk sauran abunda ka lissafa zan biya komai anjima na barka lafiya ,se kun shigo karban kudin.
ban zauna ba sanda na sallami kowa sanna na dawo falo Ina me cire hijab d'in jikina na zauna akan d'aya daga cikin kujerun falon wash kakus Allah nagaji ,sannu ke dai yar albarka ,bakiji akace neman halal da wuya ba b'arawo yace haram din ma ba bayaba.
07052100719

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
قصص عامةLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...