Chapter 21

433 49 0
                                    

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍️ real Rashida Bature

PAGE2️⃣0️⃣

Man yakamata ka gayamin abunda yake damunka tun jiya bayan kabar gurina dana kiraka naji muryanka ba yanda nasanka dashiba nama tambayar kaki gayamin yanzu ga yanayinka ya nuna akwai abunda yake damunka ,baka yarda dani bane ko me?
inhar ka daukeni amini kuma abokin shawaranka ka sanar dani.

" Numfashi amjaad yaja sannan ya dubi safwan yace sanar dakai bashi zaisa abba ya janye abunda yayi niyaba don haka nakega bawani anfanin na tsaya nata nanata abunda bazai hanuba.

"Kaidai ka gayamin maybe dalilin futarwan dakayi kasamu sassauci acikin zuciyar ka .

"Hakane amma kasani gobe su abba zasuje gidan su rumana neman aurena agun mahaifinta Wanda auren bazai d'auki lokaci ba za'ayi.

       "What?"
wata rumanan kake nufi man?

Rumanan dai daka sani amjaad yabashi amsa .

Amma kuwa su abba sun tsaya sunyi bincike sosai ne dazasu had'aka da Wannan ballagazar ?

"Kafad'a amjaad ya daga sannan yace, da abba tagayamin hankalina ya tashi,amma da na nutsu nasamo mafita wallahi abun ni sauki akasamomin don haka suje su daura amma kuma su sani kwandalata bazatayi ciwon kaiba ,ya kad'a kansa tare da cewa badai ta nace se na aure taba hmmm  .

"Ban gane me kake nufiba amjaad?

"darinyan gefen baki amjaad yayi yace duk abunda zan gayama bazaka gane ba don haka mubar zancen kaidai kawai ka zuba ido , yayi maganar tareda murmushi .

"Well ai shikenan bari mu fara shirye shirye don munkusa angwancewa yayi maganar tareda zolaya ,harara amjaad yabi safwan dashi tareda cigaba da aikinsa yanayi suna taba hira .

Ina direban yake ne wai? zaka futo ka kaini ne ko kaima kabi layin yan rashin girmamani ,?
dagudu direban hajiya ya futo, yaname gyara mazargin wandonsa,  afwan hajiya ki gafarceni naje kama ruwane tuba nake ,yauwa Ina maganar damukayi dakai kwanki ?

"Wanne kenan hajiya?

Wanda nace ka nemomin gurin da ake saida kaji lafiyayyu marasa maganin bature .

haka akayi hajiya , to maza shiga ka kaini gurin ni zansayo da kaina .

       "ayi haka hajiya ?"

dadai kindan Kara hakuri koni da kaina Sena tafi na siyo miki .

"zaka shiga ka kaini kose na futa na nemi adai daita natafi"?


     "a'a baza'ayi hakaba"

kashiga ko zaka tsaya magana?
" hajiya kiyi hakuri ki koma tunda nace miki yau daman zan siyo miki in rana tayi sanyi amjaad yayi maganar kamar Wanda zaiyi kuka don aduniya yana matukar kaunar kakan shi , hajiya bata saurareshiba tayi shigewarta cikin mota direba ya zaga ya shiga ganin haka shima ya bud'e k'ofar gaba ya zauna tareda fidda waya yakira safwan ringing biyu tayi ya daga ka sameni a gidan gonar yarinyar nan abunda ya fad'a kenan ya kashe wayar .

"horn akayi abakin get din gidan gonar lokacin muna tsaka da karatun mu ,don haka bamu maida hankali ga gurinba ,rabe ne dayake kusa da get din ya bud'e k'aramar kofa ya leka, can ya bud'e get din motarsu ta shigo haraban gun gefe suka samu sukayi parking ,rabe ya k'arasa gurinsu don ya ganesu, yace barkanku da yammaci yauwa cewar direban hajiya rabe yace sedai kunzo oga Adda khubra tana bada karatu se zuwa anjima zasu tashi in badamuwa zan iya baku abunda kukeso .

"no barshi ta gama cewar amjaad, to shikenan sannan ya risina ya gaida hajiya ta amsa tace kaga yaro zoka sallame mu kaji mukeso lafiyayyu se akace akace anan zansamu, ey hajiya muna dashi sedai me bayarwance  gata can tana koyarda karatu ido hajiya tabi gurinda ya nuna mata sannan ta dubi matan da ake koyar ma karatun tareda kashe kunne don ita tunda tashigo bataji sautin qira'aba balle tace karatun qur'ani ake koyarwa ,hannu ta daga masa tace jeka tareda maida hankalinta gunda ake koyarda karatun.

"Zaune nake akan kujerana da yazama mallakina indai agun karatu ne Babu me zama a irin kujeran da nake Kai ,.

dubansu nayi naga duk d'alibaina sunzo don haka na bude taron da addu'a sannan nace yau zamuyi karatun mu ne akan tsafta .

Yar uwa in har kinaso kizama CIKAKKIYAR MACE dolene se kin kiyaye tsaftar jikin ki dana muhallinki ,abu na farko kizamo me kiyaye yawo babu takalmi domin in har kinayi to kuwa babuke babu rabuwa da sanyi don yasamu hanyar shiganki kenan, zakuga kamar ba wani abu bane hakan to wallahi yanada matukar amfani sannan kiyi kokari ki koyama yaranki Sanya takalmi akafarsu tun suna kanana ,abu nagaba (zama ) mata dayawa sukanyi zama koyaya to kisani zamama iri iri ne akwai na CIKAKKIYAR MACE Wanda ta san me takeyi ,ki nutsu kisan a Ina kike zama awani gun yakamata ki zauna ,yar uwa yi kokari ki hana kanki zama ak'asa batare da kinsanya abu akan gunba kafin ki zauna ,ki nisanci ajiye kafarki akan tiles batareda takalmi ba ,in kin zauna kiyi kokari kiga kin hade cinyarki batare da kinbar yanda iska zai shigeki ba inkuwa kin mike kafarki ne to yi kokari ki daura kafarki daya kan d'aya,kisani bafa ke kad'ai da kika girma ne zakice zaima aikiba a'a hatta yara kanana kiyi kokarin koyamusu don inkin koyama yar ki tun tana karama da ikon Allah ahaka zata taso tana me kiyaye jikinta ,wannan kenan .

"Zamu shiga fannin jiki ,yar uwa kisani a jikinki akwai gurinda dole sekin lura dashi kin bashi kulawa na musanman inba hakaba zaki samu matsala keda oga ,guraren kuwa bawasu gu bane illa ki lura da bayan kunnan ki,bayan wuyan ki ,hammatan ki,matse matsin cinyanki,anaso akoda yaushe kiringa wankesu, shi bayan kunne ko kina zaune zaki iya neman cotton Buds, ki goggoge sannan ki zama me wanka ak'alla kiyi ko sau biyu ne arana sannan shi matse matsin cinyanki kiringa samun sabulu kina wankewa duk shiga alolarki ta farilla inkina haka da izinin allah bazakina tashin wari ba.

"Sannan Yar uwa akula da gyaran muhalli wllh ki sani duk gayunki in baki gyara yanda kikeba wllh duk banza ne , wasunmu da dama zakaga basu komai suna zaune zaman danna waya ko zaman tad'i da matan makwafta wallahi gidanta yanda kikasan juji haka yake, Babu gyara ba komai haka miji zai dawo yatarar da ita  yanda yabarta haka zai tarar da ita ,kuma don bata da kunya tace wai bai isa ya Kara aure ba imagin hmmm to wllh inzaki farfado daga dogon suman k'azantar dakikayi garaki farfado, bafa wai don karyayi Miki kishiyaba ne zaki gyara  a'a ,yau ko an miki zakiso ta tarar dake babu abunda kika gaza afanin gidanki inma da tashigo da rawan kanta don kin gazane mijinki ya aurota to seta tarar da sabanin tuninta .
ko baki da miji yar uwa yi kokarin ganin kin gyarama iyayenki gidanku zaki samu lada sannan zaki horu Wanda ko gidanki kikaje bazai zamemiki sabon abuba,sannan akoda yaushe baki da tunanin waye zai zo ,kar azo aga yanda kuke kiji kunya ,wallahi komai talaucinku matukar zaki gyara abunda Allah ya hore muku zakiji dad'in bud'e ido ki kalli gidanki kiji dad'i, duk da bakudashi allah yasa mudace.

Anan zan tsaya don haka kowacce tayi kokari taga ta gyara domin jin dad'in rayuwan mu data iyalanmu don duk abunda mukeyi shifa yaranmu zasuyi don haka iyaye kuyi kokarin ganin kun d'auramu aturban daya dace Allah yatsare mu hannu da hannaye yabamu ikon gyarawa .

mashà Allah , allah yama rayuwarki albarka yabaki miji nagari hakika iyayenki sunyi dacen samun nagartacciyar yarinya allah ya Sanya ma dukkan lamarinki albarka cewar hajiyan amjaad taname dafa kaina ,fuskata ta d'ago tana karemun kallo tareda dad'in tabarakallah mashà Allah,zanso ganin iyayenki ,

sannu hajiya barka da zuwa cewar inna saratu datake zaune agefe gun d'aukar lecture nice maihifiyarta kallon mamiki mutanan gun sukayi Wanda yasan halinta da yanda suka d'auki tsanar duniya suka dauramin .

Nima kallon nata nayi cikeda mamaki ko yaushe ne tazama mahaifiya ta oho?

Rashows ce😘

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now