💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
PAGE2️⃣9️⃣
Bayan na gama had'a mana komai ne na koma falo gun su kakus na zauna muka cigaba da kallon dad'in kowa a tashar Arewa24 Wanda nasamu su kakus suna kalla,kakus se kwasar dariya sukeyi ta duben tace khubra tashi ki kiramin siyama ,nace to kakus,cikin gida naje na Kira siyama muka dawo tare .
"zama siyama tayi kusa da kakus ta gaida kawayen kakus sannan tace hajiya kaka gani . yauwa siyama so nakeyi kije ku shirya duk wani abunda kukasan zakuyi amfani dashi acan saboda banison mu makara suzo d'aukar mu bamu shiryaba su tsaya jiranmu don haka ki sanar ma duk Wanda zaije seya zama cikin shiri don ana sallar magriba zamu tafi.
To hajiya barinje na shirya Sena gaya musu duk su shirya su zahra ma duk sunyi wanka abunsu lokacin tafiya kawai suke jira .
" Daf za'a Kira sallah magriba direban amjaad ya iso mota biyu ,bayan sunyi parking masallacin kusa da gidanmu suka nufa sukayi sallah bayan sun idar, rabe ne yashigo yake sanar mana isowar direban amjaad , kakus ne tace to shiga cikin gida ka gayama duk Wanda zaije ya futo ga mota a waje ,bayan ta gama ta nufo d'akina take sanar min nace Kakus na gama komai barin futo mana da kayanmu tace to barin je na kashe kayan kallon ta shiga d'akin ta ta gayama kawayen ta suma duk suka futo muka nufi haraban gidan gona don a gurin sukayi parking ,dukan mu yaran gidan muka shiga mota d'aya ,dayan kuma muka barma kakus ita da muta nan ta da Inna saratu da Inna zulai ,bayan mun futo ne rabe ya futa a motar ya Sanya key ya rufe gidan gonar muka nausa kan titi.
bawani dogon tafiya mukayi ba muka iso cikin g r a,wani tangamemen gate naga mun nufa muka tsaya abakin gun zuwa can aka bude mana mun d'anyi tafiya muka sake samun wani gate din na biyu sedai shi tsakanin sa da na biyu ba nisa muka nufi gurin aka bude mana muka shiga haraban gidan Wanda yaji fulawowi ga wasu jibga jibgan motoci agurin furfutowa mukayi, direban amjaad yayi mana jagora har sanshin hajiya mun iske falon su biyu ne aciki waje duk muka nema muka zauna kakus da aminan ta suka hau saman kujera gaishe ta mukayi cikin nutsuwa tana amsawa da fara'a a fuskanta tare da godiya na zuwan damaukayi ,dubana tayi tace diyata barin Sanya akaiku wancan dakin zakufi sakewa acan tana Kai aya sekuwa ga sateera tashigo falon fuska d'aure ta kumbura baki ,ta gaida yan falon sannan ta nufi cikin d'akin kakus ,kamar kuma wacce tayi wani mantuwa ta juyo da sauri tana kurama gurin danake ido baki bud'e tace laaaaaa anty kufcy daman zakizo bikin bros?
kai amma nayi farin ciki wallahi dakika hakura kikazo tana fad'a tana katasowa kusa dani ta rungumeni hajiya tace d'agata karki k'arasa ta maza d'aukesu kutafi wancan d'akin, dukanmu yan matan muka mike mukayi d'akin da hajiya ta nuna ma sateera,d'akin se qamshi ne yake tashi aciki duk da bawani shirgi bane aciki gado ne se mirror da wardrobe a gefe ya Italy se kyalli sukeyi se wata kofa daga gefe ga dukkan alamu toilet ne wajan ,ajiye kayan mu mukayi daga gefen gado sateera tace dafatan d'akin yayi muku ? murmushi nayi mata nace sekace Wanda zamu jima aciki ,tace to yanzu ga bathroom anan seku fara yin wanka naga lokaci yakusa nima barinje d'akina na d'auko kayana don tare zamu shirya daku ,barin fara Kiran me Make up tazo nan tafara yima Wanda suka yi wankan kafu mun gama namu Kai na girgiza mata ta futa na dubi su Zahra nace to muyi wankan semu jira me make up din sukace to tareda ajiye nasu kayan siyama ita tafara shiga wanka.make up akamana simple bawani me yawaba amma duk da haka nafito nayi matukar kyau sateera se santin kwalliya ta sukeyi ita dasu siyama ,jakan kayana na janyo na cirosu zan sa , sateera tace waw anty kufcy kayanmu iri d'aya daman bros ya gayamin haka na zaci wasa yakemin sedai kalan ne ya ban bata nawa silver ne da red silver yafi yawa red din kuma adon zaren ne ya zama red tana me war ware itama nata kayan , gyalen ta war ware duka tace no wonder tunda aka kawo nake tunani me zaisa bros ya karbomin babban mayafi al halin yafini girma ashe canza mana sukayi ,ta d'auki silver mayafina ta sanyamin nata red ,tace gwada anty kufcy mugani .

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Fiksi UmumLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...