💍 CIKAKKIYAR MACE💍
✍️ Real Rashida Bature.
PAGE5️⃣.
Alhamdulillah yau takama sati uku da bada aikin ginin gidan gona na kuma alhamdulillah komai ya kammala har fentin gurin anyi ansa su interlock aharaban gurin komai yazama ready .kai alhamdulillah hajiya qamshi Allah yasanya miki albarka agurinnan yanzu kam ya zama dole na daure ko bani so zan Sanya ma sunanki hajiya afarko don nafara jiyo qamshin tafiya d'akin allah bada jimawa ba jirginmu zai tashi zuwa qasa me tsarki ,Allah ka tabbatar mana da wannan nufi kan na mutu cewar hajika kaka,oh my kakus in sha Allah bazaki mutu yanzu ba se na kaiki makka da yardan allah.
kakus ta rungume ni tana me share hawayen idonta allah yanufa hajiya khubra Allah yasa abude a sa'a, amiin my kakus.
muka dudduba guri kam yayi kyau sosai sedai ace mashà Allah kawai.
bayan mun dawo cikin gida na dubi kakus, hajiya inason anjima zan fita naje cikin garin bauchi domin sayan abincin kaji tunda komai ya kammala daman abincin ne na jinkirta , to amma d'azu me kawomin kaji daga garin jos yace se zuwa k'arfe biyar na yamma zasu iso, don haka bamuda lokacin batawa tunda na gama girkin walimar bude gidan kajin inaga kawai muyi nanda awa d'aya don naga yaran gidannan sunfini hanzari kaf dinsu sun shirya sekace zasu biki ,abuma nace musu se k'arfe hudu amma su tunkafin sallar azahar har sun shirya .
to ke yanzu miye damuwarki?nifa hajiya damuwata kar nazauna yin walima har masu kawo kaji su iso banje na sayo abincin kajin ba bansayo maganin suba , sannan bansan me zance ma baba alhaji ba tunda nace masa ya kira abokinsa da matarsa walimar.
yanzu ke don wad'annan k'ananun abunne kike damun kanki ?to maza tashi ki kwashi kayan ciye ciyen ki shiga dasu gidan gonar sannan ki jera komai inkin gama kizo ki gayamin .hakan kuwa akayi naje na gyara fararen kujerun danayi a rumfar farko domin zaman masu sayan kwai ,na zuzzuba fried rice a plate, nasanya wani plate din na rufe Sena dauko pure water na Sanya awani plate din tare da zo6o na ajiye akusa da plate din abincin haka nayi ma kowa ,dayake nasan yawan mutanan dana gayyata .
na koma cikin gida nashiga bayi (toilet)nayi wanka na jima aciki Ina dirje jikina da sabulun give ,nafuto na mulke jikina da humra sannan na nufi d'an durowan danake ajiye kayana ,na ciro sabuwar atamfa ta dana d'inka domin wannan rana,na dawo bakin gadona na zauna na mulke jikina da maina wato me gurguwa don Ina matuqar son man ,nadauki body spray na mist na feshe jikina kafin na Sanya kayan doguwar riga akamin d'inkin zamani sannan nacema telar yamin igiya ajikin kayan yakuma yimin aljihu ,na murza farar powder a fuska ta na sanya kwalli se man baki kad'ai na sanya Amma dayake fara ce ni se nayi kyau sosai,na nemon himar madai daci kalan kayana wato red kala na fesa turare ajiki na Sanya na dauki waya ta Kiran kamfanin maxfone M28+ ,nafuto falo ban iske hajiya kaka afalon ba don haka na nufi cikin dakinta nanma batanan .
cikin gidan na nufa duk ban gansuba sena dawo sashinmu na rufe mana kofar d'akin sannan na rufe kofar sashin ta ciki yanda nawaje bazai iya shigowa cikin gidanba ,na nufi gidan gona ta don Inada tabbaccin gurin suka tafi tunda banga kowa agidanba .
aikuwa maganata ta tabbata domin kaf Wanda na gayyata sun hallara gurin nasan wannan ba aikin kowa bane se na hajiya kaka,na karaso nima na samu guri na zauna a d'aya daga cikin kujerun gurin,.hajiya kaka itace ta mike ta bud'e mana taro da addu'a sannan ta daura da cewa ba komai bane yataramu anan sedan mu taya jikata abu tunkawo na murnar gama gidan gona datayi ,kukuma sauran jikokina ina me roqon allah daya Sanya muku kwazo da kuzarin miqewa domin ku dogara da abun kanku bana iyayenku ba , ubangiji Allah yasanya albarka ma wannan guri yasa nan gaba agina gomansa Kai kuma jamilu daka bada gudun mawa angode Allah yakarama budin alkhairi yasa ka gama lafiya,masu baqin ciki kuma allah yamana maganiku ya kauda idon ku ga cigaban jikana ,munafukan 6oye muna muku jinjinan bangirma . murmushi nayi don nasan da wanda kakus takeyi.
Baba alhaji ne ya mike yana mecewa nayi matuqar farin cikin ganin wannan rana,sannan Ina me godiya ga Allah daya bani aron rai harnaga gidan gona da "Yar dana haifa da kaina ta gina ubangiji Allah ya sanya albarka ma wannan gida ya tsare duk wani mummunan abun da zai dosa sa ,shawarata anan itace khubra ki nitsu ki bada himma ga wannan abu ,sannan ki sauke haqqi ga duk Wanda yake qarqashin ki harta su kajin somin suma amana ne Allah yabaki don haka ki kula sosai Allah yamuku albarka gaba d'ayanku ,sannan kukuma inda mai ra'ayin yin aiki anan gidan gonar zaku iya zuwa neman aikin agurin me gidan gonar inkun dace to ,don itace keda komai a hannunta .hajiya kaka ne ta sake miqewa ta dubi manyan qawayen ta hajiya zainabu da hajiya karima yaunefa ranar da zaku nunamin cewan kuna tare dani ,don haka zanso ku fito ku kwarara ma jikata addu'a,take kuwa suka mike atare suna washe baki jin qawar tasu tabasu suna hajiyoyi suka fara kwararo addu'a daga bisani suka zauna ,daga bisani kakus ta gabatar da aminin alhajinmu malam kallamu kaima yakamata ka tofa albarkacin bakinka .
ya mike shima ya sanya albarka , hajiya kaka ta dubi su inna to matan alhaji ko dame abun cewa acikin ku ?
Inna zulai ne ta mike tayi addu'a itama sannan ta zauna sukuwa su inna saratu fuska cunkushe sukace Allah sanya alkhairi , to amiin indagaske ne cewar hajiya kaka,sannan ta dubi yayu na kamal da jamal "to yayun kwabo kukuma bazaku nuna naku farin cikin bane ko me"? Allah sanya alheri sukace atare suna me zum6uro baki gaba.daga bisani ta gabatar ma kowa abincin dayake gabansa akaci akasha ,sannan aka zazzaga cikin gurin hajiya kaka se bayanin komai take musu nidai se kallon su nakeyi kawai Ina murmushi.
na dubi kakus najata gefe , hajiya kaka nikam zan barki anan ki kula min da komai zanje cikin bauchi don kar kajin su iso ban da abun basu gara na adana komai kafin su iso .to shikenan kiyi addu'a daman ,sannan ki kula da kanki allah ya tsaremin ke a duk inda kike kidawo dawuri nace in Sha Allah kaka ga key din sashinkin don na kulle ne kar ashiga inyaso sekisa su zahra su tattara nangun karsu barshi haka duk datti.daman ai wannan dole ne tunda suka ci suka 6ata to yazama dole su gyara ke dai yi maza kije kisamu ki dawo dawuri.07052100719.
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
General FictionLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...