💍 CIKAKKIYAR MACE💍
✍️ Real Rashida Bature.
PAGE3️⃣
yau tun k'arfe uku na farka nayi istihara kamar yanda na sama rainazanyi najima Ina sallah har asuba tayi nayi nafula wato salatul fajr.
nazauna inata lazumi har aka kira assalatu na mike nayi sallah asuba, najima inakai kukana ma Allah buyi gagara misali,bayan na idar nayi azkar din safiya don bani wasa da azkar domin shine takobin mumini,
dana shafa addu'a na mike na ninke abun sallan na daga karkashin katifa nadauko wannan kudin da kakus takarbomin agun alhajin mu ,na mayar da katifar na zauna akai sanna na kunce kullin dana mata sekuwa ga tulin kudi sun bayya ,
ido na zaro don tunda nazo duniya bantab'a ganin kud'i masu yawa hakaba,baki bud'e na gyara zama sannan na mik'e dasauri naje na kullo kofata nadawo na zauna na zazzage kud'in akan gadon nafara rabasu Kashi kashi nacire yan dubu daban yan d'ari biyar daban,sannan nafara aikin k'irgasu dalla dalla don banison asamu matsala ,bani nagama kirga kud'in nanba har saida naga rana ta b'ullo ta jikin labulen window na,sannan na sarara musu ahakanma so nakeyi wai nasake k'irgawa nagani kar wani ya mak'ale ajikin d'an uwansa .cikin hanzari nafuto na nufi kitchen dake cikin falon mu ,na kunna gas Wanda nasiyo mana d'an karami na daura ruwan bak'in tea namishi hadin komai sanna nafuta don bama kaji abinci da ruwa se kuka sukeyi saboda yau ban basu dawuriba.
bayan nagama bama kaji ruwa da abinci na dibo kwai din dasukamin naje na adanashi acikin gurin da na ware domin adana d'anyar kwai kamar store haka gurin yake
na nemi laida bak'a na kulla kwai aciki na nufi cikin gidan mu wato sashin matan alhaji mu .da Inna zulai amaryan alhajimu muka fara had'uwa a tsakar gidan na duk'a Ina mai gayar da ita .
"hajiya innata ashe kin tashi "?
natashi khubra ,
"Antashi lafiya innar mu Yaya karfin jikin?"
lpia lw khubra jiki yayi sauki sosai ,yaya hajiya ta tashi dafatan komai lpia.
nayi murmushi nace komai lpia inna ,inasu zahra suka barki kike tsaye anan ke kadai?
zahra suna ciki nima abu nafuto zan dauka kika ganni anan ,ayya to allah yakara miki lpia ,amiin tace min ,na mik'a mata laidar hannuna inna ga kwai ba yawa asoyama su Zahra sannan inna acigaba damana addu'a ga sana'ar nan , murmushi inna zulai tayi tana mecewa inbanda abunki khubra yaya za'ayi ki debo kayan jauran ki haka ai semu karya jarin dakin bari har sekin dad'a bunqasa tukunna seki bamu alakoron.
nayi dari nace kai innarmu yanzu kwai guda goma ne dayawa ? ai addu'ar ku na cigaba da bun qasar kasuwanci muke nema da bakin ku me albarka, to shikenan khubra mungode Allah yasa nangaba abud'e mana k'aton gidan gona Allah kuma ya kauda idon makiya arzik'i yata bunqasa ,amiin Inna ta myb hajjin bad'in bad'ad'a dake za'aje irin wannan addu'a haka,nafada Ina dariya "kajimin yarinya "wato bama na bad'in nan ba har sekin karamin da bad'ad'a ko,to inna banda abunki har yau she na bunkasar da zan miki alkawarin zan biya Miki kujeran makka shekara me zuwa ,kinsan ban karya ,hakane kuma fa cewar inna to godiya nake dawannan kyauta .nanufi dakin Inna saratu nayi sallama yaranta suka amsamin nashiga cikin falon nasamu guri na zauna,nagaida ya Kamal dana same su a falon ,sanna na gaida ya jamal, nikuma sauran yaran d'aya bayan d'aya suke gaisheni domin na girme musu ,duk rashin jituwar da mukeyi da matan alhajina bai hana mu yaran gidan mu girmama junaba .innace tafito daga cikin dakinta a'a Yaya nakejin kamar muryan "yar gadara"adakinnan tana me k'arasa futowa falon,nabasar kamar banjitaba ,ta nemi gun zama akan rub'abb'un kujerunta ,sanda ta yi kusan minti uku da zama sannan na dubeta Ina mecewa inna barka da safi dafatan antashi lpia lafiya lw ai na d'auka maganarma bazaki iya bane kinwani hakimce akujera sekace fulani agidan sarki nayi murmushi wanda yazamemin jiki inbason magana,na mike Ina me zuwa kusa da kafarta na ajiye laidar dake hannu na,inna ga kwai a soya masu rabe amma sadaka ne ,kowa daya naki biyu yakama guda goma kenan namata murmshi na mike zan futa..keee dakata zoki d'auki tsiyarki har nice zaki kalla don bakida kunya kicemin sadaka kika bamu dayake ance miki mu mabara tane ko ?bance komaiba na juyo zan d'auki laidar caraff rabe ya d'auke dan Allah Adda khubra kiyi hakuri ki barmana wllh mukam munaso inyaso semu had'a dana innar tunda kinga mu takwas ne ad'akinnan mungode Adda, na shafa kansa nace cewa zakayi allah shikarb'a don sadaka nabaku d'an k'anina nayi masa murmushi najuya na futa .
Ina jiyo muryo yinsu suna murna .
nashiga b'angaren inna tabawa da sallama na iske surayya abakin murhu tana wura wuta Adda khubra Ina kwana?na galla mata harara tayi sauri rike baki yi hakuri Adda antashi lpia,nace lafiya lw duk randa kika sake cemin ina kwana Sena zubar miki da rub'abb'un hakoranki kaf,na nufi falon inna tabawa nayi sallama tareda d'aga labulen nashiga cikin falon ,Ina Sanya k'afata aciki ji nayi tankar nasanya a cikin yashi haka na daure na shiga nasameta baje itada sauran yaranta na nemi kujera na zauna duk yaran suka hada baki Adda khubra antashi lpia lpia lw dafatan kuntashi lpia ? na amsa musu sannan na dubi inna tabawa ,Inna antashi lpia lw tace min atakaice don duk cikin matan alhajimu tafi nuna min tsana ,don haka nima na mike Ina me ajiye mata laida agabanta Inna ga kwai asoya ma kanne na sadaka naki guda biyune aciki sukuma kowa guda guda nayi fucewata yaranne ma naji suna Adda allah ya amfana .Ina komawa na sauke ruwan tea din najuye a flas, na fasa kwai na yanka albasa na Sanya danyar tumatur nad'an bubbuga tafarnuwa kad'an bame yawaba nasanya maggi Sena futo haraban sashenmu na tsinko zogale kadan na dauraye shi da naga ruwan jiki ya tsane Sena zuba ahadin kwan na barbad'a Curry kad'an sannan na daura pan din akan gass na kunna na soya mana na jera namu akan tebur din dayake falon na jera na alhajinmu akan d'an ma dai dai cin ture na nufi sashinsa na tsaya abakin falon nayi sallama daga ciki ya amsamin yana me bani izinin shiga,nashiga na ajiye turen hannuna akan tebur na durkusa alhaji antashi lpia? lpia lw khubra Yaya kika tashi keda hajiyar taki,?nayi murmushi duk muntashi lpia nabashi amsa ,to mashà Allah yau wani abun dad'in nasamu haka "Yar hajiya?kai alhaji kwai nefa da ruwan shayi na bashi amsa Ina me dad'a gyara zama aikuwa nagode sosai allah yabaki masu miki kema, yajikqn mahaifiyar ki nace amiin alhaji .mukayi shiru nadan wasu lokaci sannan ya dubeni akwai abun da kike sone ?na girgiza kaina nace a'a godiya zanyi daman jiya hajiya kaka tabani kud'in dakace zaka banni to shine nazo godiya.oh kice shine kikazo toshiyar baki da kwai dai yana maganar yana dariya ,nima dariyan nayi a'a alhaji nidai godiya nazoyi zalla Ina me dariyan nima alhaji nagode sosai allah yakara rufa asiri yasa kafi haka Allah kuma yajikan mahaifa yabamu ikon jin qanku.amiin khubra shiyasa nake me alfahari dake saboda kwazonki dakuma sanin yakamatan ki da hangen nesa , duk da nasan halinki zan dada rokonki daki nutsu ki bada himma ga kasuwancinki tunda angama karatun sakandiren sekuma muta addu'a har Allah yafuto da mijin aure se kiyi,nagode sosai alhaji.
amma baba alhaji ashe kana dakudi haka ?oh khubra kincika bin kwaf inadashi daidai gwargwado ,nuna wane bansonyi don nasan halin matana kema don na auna hankalinki ne, a kaji guda ashirin kin gyarama hajiya kaka sashinta kin sanya mata tayals adakinta kin saya muku gass na girki kin gyara daki daya daga cikin d'akunan dayake cikin falon kinmayar dashi kicin ga abun tafasa ruwan zafi kinsanya mata a bayin ta kin dauke nauyin da ya zama nine yakamata ace namata don neman albarka gashi Sam baki barinta da yunwa, kafin matana su tashi su girka ke harkin gama kinbata taci kikuma kula da ita ,aikuwa kin cancanci na baki sama da miliyan d'aya ,bakuma don nafi sonki bane na baki duk Wanda naga sun ya maida hankali ga sana'ar kowanne zan bashi jari ,amma Sam inbanda gantali babu abunda suka Sanya agaba har kananun abun na damuna .
wannan kud'in da kikaga nabaki kud'in filina ne dayake garin dungal shine na sayar wancan satin akan zan dad'a a kasuwancina na shanu, to ganin danayi kin mai da hankali ga kiwon kajin kuma Allah yasa ma abun albarka shine nace barin baki mugani ko za'a dace, don naga nauyin yayi miki yawa gashi har naji hajiya kaka tace ta saukemin abincin gidana se naki ,shine naga kajin sun kasa ma wannan d'awainiyar ,dafatar bazaki bani kunyaba zakiyi abunda ya dace.in sha Allah zan maida hankali naga nayi abunda kud'in bazai lalace ba sedai alhaji Ina neman addu'a ka domin ganin haske ma lamari.
addu'a kullum acikin yimuku mukeyi sedai zamu dad'a akan Wanda mukeyi allah yamuku albarka gaba d'ayanku nace amin nayi masa sallama nadawo sashin kakus.😘 07052100719
YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
General FictionLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...