chapter 10

540 60 2
                                    

💍 CIKAKKIYAR MACE💍

✍🏻Real Rashida Bature.

PAGE9️⃣
Tsaye nake agefen titi  Ina duba waya ta danaji shigowar sak'o ,Ina dubawa Ina tafiya gabbbbb naji na bugi abu me sanadin haka k'ar wayata danake lallab'a ta fad'i ak'asa tayi filla filla ,wash nace tare da dafe goshi na,na tsugunna ina tattara wayata na mik'e tare dacewa sorry batare dana dubi da waye mukayi karoba ,idonsa ya lumshe tare da datse hakoran sa bayan na gama had'a wayata na d'ago da kaina don ganin Wanda na bashi hak'uri banga alamar ya motsa ba ,ido na qura ma fuskarsa na tsawon wasu lokaci Ina tunanin inda nasan fuskar cak tunanina ya tsaya don tabbas inban mantaba wannan shine mutumin da yasa akacire mana tayar mota shine AMJAAD ,cikin rausayar da Kai nace ummmm kaga d'an k'aruna me kud'i abuhu ey lallai ba shakka wannan aiki dama ai se Kai na fad'a cikin siririyar muryata Ina me dubanshi , bud'e lumsassun idon shi yayi ya zuba ma fuska ta,sannan ya kafe d'an karamin  bakina nakuwa  murgud'a bakin Ina me sake d'aure fuska nace waishin Kai wani irin mutum ne mara tausayi to wallahi da wayata wani abu ya sameta allah dase kabiya ni don bazan d'auki asarar ko kwandala ba ,tudun gashina dayake d'aure ta cikin himar ya kamo ya hankad'ani na had'u da gefen wani shago dayake kusa damu,sannan yaringa biyoni a hankali har sanda ya cimmani ya bud'e baki kamar Wanda akamishi dole yace cikin kakkausar muryanshi me dad'i ke wata irin kucaka ce waya baki lasisin da zaki bud'e wannan wawan bakinki harki samu damar magana dani kisan ma Wanda zakiyi ma  shirmenki idan kika kuskura wad'annan masillan k'afafuwarkin suka kuskura suka k'ara tako inda nake Sena baki mamaki wawiya kawai ,tsoro ne ya kamani tamkar zanyi futsari ajikina ganin irin zare idon dayakemin gashi gab dani ya tsaya har Ina jiyo numfashin sa a fuskata a fusace ya koma mota ba tare da ya shiga yanda yayi niyan zuwa ba ,na jima a tsaye agun Ina zare ido haka na daure na nufi shagon animal Care nasayi duk maganin danake buk'ata na futo duk banda nutsuwa atare dani tunda nake ban tab'ajin namiji akusa dani haka ba don ko bak'ar magan ganun daya gayamin basu damen kamar jinsa danayi akusa dani ba ,jikina asanyaye na gama sayayya na sannan  na nufi kamfanin sa don sayan abincin kaji daman haka nakeyi senayi sayya nake zuwa nasayi abincin kaji shine na k'arshe .
nagama komai acikin kamfanin hatta kud'in duk na biya receive kawai nake jira ya rubuta min Ina zaune a d'aya daga cikin kujerun gurin ,wayar  cikin office dince ta fara ringing cikin hanzari naga manager ya d'au wayar ji nayi yace ey ga takalman a gurina daman so nakeyi mutane su ragu Sena kawoma ban zaci yanzu zaka buk'ata ba ,banji abunda Wanda ya bugo wayar yaceba nadai sakejin manager yasake cewa ba kowa kusa gashi kuma yana tare da mutane ok ok sir zan bayar yanzu akawo maka in sha Allah sorry sir .

harya mik'e ya d'auki wata laida dake kusa da tebur din ya dubi mutanan da muke zaune agun yana raba idon yaga waya dace ya aika cak idonsa ya tsaya akaina yace d'iyata zoki taimaka ki kaimin wannan sak'on wancan office d'in .d'an jimmmm nayi kamar bazan tashiba can na mik'e na iso gurinshi na karb'i aikan yace nagode d'iyata zakiga an rubuta A.M.ARAB ajikin office d'in nace to baba ,tafiya kad'anne ma na iso na tsaya agaban office d'in na kwankwasa naja gefe na tsaya zuwa can banji anyi maganaba nake kwankwasa wa still banji an amsamin ba na murd'a hannun kofar na lek'a da kaina na hango mutum zaune akan kujera gabansa tebur ne dauke da tarkacen takaddu ga labtop gabansa se aiki yakeyi waro idona nayi waje don ganin Wanda yake zaune akujeran ba wani bane illa mutumin damuka yi gware d'azu wato amjaad.
futo da kaina nayi waje tare da rufe masa kofar ,waje na samu a gefe na zauna na bud'e jakata na ciro biro da takarda Wanda nake lissafi na yagi faifa nayi rubutu na rufe sannan na tashi nakoma bakin k'ofar office d'in na sake kwankwasa wa daga ciki yace yess na mud'a nashiga har na iso gaban table din bai d'agoba saidai naji muryansa yace ajiye nan batare daya duba waye ba hakan yamun dad'i na ajiye masa laidar asaman table din garin ajiyewa na zaro kudin dana gani akan table Wanda nake da tabbaccin zasu isheni ,sannan na ajiye takardan danayi rubutu akan laidar na juya nayi fucewa ta.

horn ya danna megadi ya bud'e masa yashiga ko tsayuwa ya gyara parking baiyiba yayi shigewarsa cikin gidan a falo ya yarda suit dinsa na sama  ya nufi harya d'akinshi,mom dake gyara flour dake tsakiyar table d'in dining ta dubi d'an nata cikin kulawa a'a son lpia naganka haka ? juyowa yayi yaga tana inane don shi dayashigo Sam bai lura da akwai mutum a falon ba .

        " nothing mom "
yana me shigewa ciki ,kad'a kafad'a tayi don tasan halin yaronta inba wai shi yayi niyar fad'a ba bazai fad'aba inkuwa yace babu to ko Yaya zakayi bazai fad'aba,.
direct bathroom ya wuce don ya watsa ruwa ma jikinsa ko saiji saukin fushin dayake ji azuciyar sa don har yanzu haushin kansa yakeji da yabar yarin yarnan ta tafi haka banza bemata komai ba ,tsaki ya ja Wanda yayi yafi ak'irga kafin ya kawo gida .

        ****************

Koda na dawo gidama bani da wani walwala idan na tuna abunda yafaru duk senaji wani iri ganin zan damu kaina da tunanin da bazai fishsheniba na tattara na watsar da komai na cigaba da abubuwan gabana.

Rashows 😘

Please vote and comment guys

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now