༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 147 & 148*
*_BUKUKUWA SAURA SATI BIYU _*
Abinda ya rage dai yanzu bai wuce zuwan wannan muhimmiyar rana ba da aka jima ana dakon zuwanta. Ranar da za'ayi casu a cashe, shagali ne na 'ya'yan manya. Shagalin da naira zata daki raina, ranar da naira zata kare kukanta kenan, babu shakka dukkan wanda ya kwana ya tashi ya san families din da angwayen suka fito, to ba zai yi maimakin shagalin ba.
A wata ranar Lahadi ne dai angwayen su uku suka shirya wani dan takaitaccen zama a Tudun Wada. Zaman wanda Habib ya shirya kuma ya jagorance shi, ya maida hankali ne akan yadda zasu gudanar da nasu shagalin partyn bangren yara. Habib ya shawarci sauran angwayen, wato Kabir da Mustapha akan cewa tunda magabata sun hade bukukuwan, za'ayi su lokaci daya kuma rana daya, me zai hana suma suyi koyi da manyan tunda abin ya zama kamar dangi daya.
Wannan ce shawarar da Habib ya bayar wacce nan take su Kabir din suka yi na'am da ita. Habib yace,
“Masha Allah, to yanzu sai batun wajen da za'ayi taron. Wane waje kuke ganin zai fi dacewa muje?”
Kabir yace, “Eh gaskiya ne wannan, ya kamata a samu waje very comfortable with enough space. Ni a tawa shawarar me zai hana mu bawa Crystal Palace dake Farm Center aikin hada wajen da abinci da komai, ko yaya kuka gani?”
Habib yace, “Tabbas dama abinda ke raina kenan.”
Kabir ya dubi Mustapha yace, “Ba ka ce komai ba, ko kana ganin akwai wani wajen daban da ya fi can din?”
Cikin murmushi Mustapha yace, “No, ai babu wani waje da ya fi Crystal Palace, waje ne me kyau sannan suna da kyakkyawan tsari. Can din kawai za'a je.”
Sun jima suna tattauna batutuwa da dama da suka shafi hidimar bikin, daga bisani kuma suka shiga hirar bada dan takaitaccen tarihin rayuwarsu, musamman ma abinda ya shafi gwagwarmayar soyayya. Sai yanzu ne da Mustapha ya bada labarinsa, Habib ya san cewa, Mustaphan yayi soyayya da Hassanah. Abin dai nasu gwanin sha'awa tamkar 'yan uwa daki daya, daga karshe suka yiwa kansu addu'o'in fatan alkairi suka watse kowa yayi nasa waje.
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."