Pɑge 71 & 72

15 2 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 71 & 72*

Sai asuba Mustapha ya farka, gama sallar Umma keda wuya ta ga ya motsa har ya bude idonsa, kalle-kalle yake kawai amma ba magana. Yunƙurawa ya yi zai tashi zaune Umma ta matsa kusa dashi ta kama shi ya jingina tace, “Sannu Mustapha.”

“Sannu yaya Mustapha” Nabila ma ta fada yayin da ta shigo bayan ta ɗauro alwala zata yi sallah.

Kallonsu kawai Mustapha yake ya gaza buɗe baki ya yi magana. Zaune yake dai yana ta duban inda suke, yana duban Umma. Sai da gari ya ida wayewa, wata nurse wacce ta kula dashi, ta zo ta duba jikinsa. Bayan sun gaisa da Umma ta dubi Mustaphan tace, “Masha Allah, sannu ya jikin naka?”

Kallonta kawai ya yi da ido babu magana, Umma ce tace, “Tun ɗazu ya tashi amma yaƙi magana sai dai kallon kawai.”

Nurse tace, “Babu damuwa zai yi magana insha Allah.”

Ta rubuta wasu magunguna da allurai ta miƙawa Umma takardar tare da cewa, “A samo waɗannan yanzu.”

Ta mike ta koma ofis dinsu, shayi ta haɗowa Mustapha tace, “Mama ga wannan a bashi yana sha, ka sha wannan shayin kaji kafin a sake yi maka allura da kuma maganin da zaka sha.”

Umma tace, “An gode Allah ya saka da alkairi.”

“Babu komai Mama ki bashi ya sha a hankali.”

Nurse ta fada, har ta juya zata tafi sai tace, “Ba'a tafi sayen maganin ba?”

Umma tace, “Eh wallahi muna jiran Abban nasu ya zo tukunna.”

“Okay, bani katin mu gani.”

Nurse din ta karɓi katin ta nufi shagon Pharmacy na asibitin ta sayo magungunan da alluran. Bayan mintuna kamar talatin (30 minutes) ta dawo. Lokacin Mustapha ya mike Umma ta kama shi ta yaje toilet ya wanke idonsa. Sannan ta bashi shayin ya dan sha

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Où les histoires vivent. Découvrez maintenant