Pɑge 3 & 4

15 3 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️


______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 3 & 4*

Bayan Inna ta dawo gida tunani yaƙi barin zuciyarta, take sanar dasu Hassanah irin cin zarafin da yayi mata, suma ransu ba ƙaramin ɓaci yayi ba. Nan suka yanke shawarar zagayawa neman taimakon masu kuɗin unguwar tasu.

Duk da cewa an sani a sanadiyyar aikin wahalar wankin kayan mutanen unguwar ne, ya gamu da wannan cuta, musamman ma masu kudin amma dududu abinda suka haɗa masa bai kai naira dubu hamsin ba.

Daga me bada naira dubu biyu (N2,000) sai me bada dubu biyar (N5,000), mafi girma shine wanda ya bada dubu goma (N10,000) yana ganin yayi gagarumin kokari.

Kusan sati biyu yana kwance a asibitin babu wata kulawa sannan kuma ba'a samun kudin da za'ayi masa aikin ba, dan haka sai aka sallame su suka komo gida. Kashi da fitsari komai a inda yake a nan yake yi, Inna ke gyara masa idan ya ɓata jikinsa.

Wannan shine musabbabin da ya tilastawa Hassanah da Usainah shiga wancan aikin na kamfanoni, bawai dan su samu kudin da za'a yiwa mahaifinsu magani ba, sai dan su samu abin sakawa bakin salati da rufawa kai asiri.

Yau su samu aikin gobe su rasa, yau suna wannan kamfani gobe suna wancan, haka suke yawo a kan hanya kullun kamar kuɗi. Yanzu haka sun shafe kusan watanni takwas suna wannan aikin bautar.

*******************

Hassanah da Usainah 'yan mata ne kyawawa ne masu diri da sura me matukar kyau, farare ne sosai, sai dai wahala tasa sun ɗanyi duhu kaɗan, suna da doguwar fuska, hanci siriri da baki ƙarami madaidaici, ga kuma 👁👁 idanu tubarkallah! Kamanninsu ɗaya sai dai Hassanah ta ɗan fi kiba kaɗan, wannan ita ce sifa ɗaya tak! da take banbance su.

Babu namijin da zai haɗa ido dasu face yayi kwaɗayin samun ɗaya daga cikinsu a matsayin matarsa. Yara ne masu nutsuwa da kamun kai, suna da kunya sosai, zancen banza ko shigar banza ba ɗabi'arsu bace, ba ma su da isasshiyar suturar da zasu yi irin wannan shigar fitsarar.

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now