༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 143 & 144*
Bayan kamar sa'a daya, Mustapha ya kira amaren nasa yana musu albishir da wannan abin alkairin da ya same su. Hasiya ya fara kira, tana dagawa yace,
“Albishirinki ”
Cikin murmushi me sauti tace, “Goro, me kuma muka samu haka?”
Cikin yanayin dariya Mustapha yace, “Wata na gani naji ina sonta har ma an daura mana aure tare, yanzu haka ma gani a gabanta, ita ce uwargida tunda ta rigaku shigowa.”
Hasiya ta kwashe da dariya sannan tace, “Kai amma lallai wannan ta cika 'yar sa'a, muna taya ta murna da wannan babban matsayi da ta samu na uwargida. Fatanmu dai kada ta hanaka saurarenmu.”
“Eh to watakila dai ba za tayi kishi da ku ba, idan ina gida babu ruwanta dani zata bar muku ni kuyi duk yadda kuke so. Amma fa da zarar zan fita kasuwa ko wata unguwar, to tare da ita zamu fita. Wannan shine sharadin da ta gindaya min, ban sani ba ko zaku amince da hakan?”
“Hmm! Toh 🤔🤔🤔 ikon Allah kenan, wannan wace irin uwargida ce babu ruwanta da mai gida a lokacin da yake gidan, sai dai idan za'a fita a fita tare da ita, ta zama shanshani mai kafar yawo kenan. Amma kam dai bata more ba, indai wannan ne sharadinta mun amince.”
Dariya yayi tare da cewa, “Hmm! Dad ne ya saya mana mota just an hour ago.”
A kwance Hasiya take suna wayar jin haka yasa ta mike zumbur tare da cewa,
"Wow! Congratulations, wace iri ce? Dad mun gode maka! Please ka zo yau da yamma ni zan fara hawa kafin Mami ta hau, wai yanzu kana ina ma me kake yi ka zo kawai dan Allah."
"Hmm! Ki kwantar da hankalinki yau da wuri zan bar kasuwa zan zo, ke zaki fara shiga."“To shike nan ina jiranka fah dan Allah pls.”
Suna gama wayar ta mike ta nufi wajen Ayya tana fada mata cewa,
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."