Pɑge 119 & 120

9 2 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 119 & 120*

“Eh hakan yayi babu matsala, Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya.”

“Amin ya Allah, ya ya su Nabila da fatan suna lafiya.”

Sun dan jima ba laifi suna hira a wayar sannan suka yi sallama. Hasiya farin da murna suka kara daduwa a ranta, ta tabbata da zarar Mustapha ya je ya gaida Abban nata to magana ta kare sannan kuma barinta na ayi bikin da wuri zai cika. Saboda Abban nata zai bata goyon baya sosai, kaifi daya ne idan zai yi to zai yi idan kuma ba zai yi ba ko amsawa ba zai fara ba.

Da yammacin wannan rana kuma Mami ce ta kira Mustapha bayan sun gaisa tace,

“Gobe nake ka zo Bompai gaida su hajiya.”

Gabansa ne ya yanke ya fadi, nan da nan yayi wani tunani kamar haka;

‘Wai meke faruwa ne komai za'ayi sai su ce rana daya, kamar hadin baki, yanzu na amsawa Hasiya gobe zanzo yanzu kuma ita ma gashi tace gobe’.

Wannan dan tunanin yayi, daga baya kuma sai ya saki murmushi me dan sauti tare da cewa,

“Ranki ya dade gobe-goben nan babu wani shiri, ba za'a bari ba sai zuwa jibi?”

“Gobe fa babu aiki weekend ne shiyasa nace ka zo, kuma fa kasan kwana biyu ban ganka ba tunda muka dawo daga hutun sallah. Kawai ka zo goben na riga na fadawa hajiya gobe zaka zo ne da sai mu bari sai jibin.”

“Hmm! Ranki ya dade kenan, shikenan zan zo zo amma kamar da wane lokaci ya kamata na zo?”

“Ni dai nafi son ka zo da kafin karfe goma sha-daya na safe 11:00am indai ba wani uzuri bane da kai.”

“Bani da wani uzuri, insha Allah zan zo.”

“Yauwa idan ka zo Bompai, layin dutsen Bompai zaka shigo, ka tsaya dai-dai dutsen ka kira ni.”

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now