Pɑge 113 & 114

9 3 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 113 & 114*

Murmushi Habib yayi tare da kashe wayar ya fito daga mota ya shiga gidan. Kai tsaye falo ya nufa da sallama ya shjga. Mami ce ta amsa masa da cewa,

“Wa'alaikums salam warahamatullah ta'alah wabarakatuh, barka da zuwa.”

“Barkanki dai”

Ya fad tare da zama bisa kujera two seater. Nan a kayi gaishe-gaishe, Usainah tace, “Yallabai Habib ya shagalin sallah, ina hajiyarmu da fatan tana lafiya.”

“Hmm! Lafiyarta kalau, amma fishi take daku tunda kunki zama ku yini tare da ita.”

Dariya suka yi gaba dayansu, Mami tace dora da cewa, “Gaskiya hajiya ba zata yi fishi damu ba, watakila dai me maganar ne yake fishi damu saboda mun hana shi zuwa wajen farin cikinsa.”

“Hmm! Kema dai Mami na fuskanci guda ce wajen iya tsaro zance.”

Hassanah ce ta fadi wannan maganar, shi kuwa Habib murmushi yake saki. Kimanin kamar mintuna biyar suna ta hira cikin wasa da dariya, Usainah ta mike ta nufi kitchen ta kawo masa abincin nan da suka hada masa, sannan ita da Mami suka fice daga falon suka bar Hassanah da Habib kadai.

Hassanah ta mike daga kan kujerar da take zaune ta koma wacce Habib ya zauna. Kusa dashi sosai ta zauna sai da jikinta ya taba nasa, kamshin turaren jikinta ya rika dukan hancinsa, haka ita ma ta rika shakar kamshin nasa turaren.

Kallonta kawai ya rika yi, ya tsura mata idanuwan nan nasa ko kiftawa baya yi. Kyau ya ga ta kara yi sosai, tayi kiba kadan ta kuma kara haske, tayi dumurmur da ita kamar ya dauke ta ya tafi da ita.

Kallon ta ga yayi yawa, domin har idonsa ya fara sauyawa ya fara rikidewa zuwa launin jaja-jaja. Cikin wani salon murmushi me kara kashe jiki hade da motsa bukatu daban-daban, tace, “Ya ya dai malam lafiya? Me kake kallo haka ne?”

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now