Pɑge 29 & 30

13 2 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 29 & 30*

Dariyar shima ya yi sannan yace, “Wallahi ni har kin sa bacin ran ma ya tafi da wannan maganar me kama da comedy. Nine fa Kabir dinki, K.B ko kin manta ni ne. Hajiyata ya ya zanyi abinda zai janyo mana bacin suna har aje kotu? Ya ya zan lalata 'yar wasu, muma fa muna da irinta. Ga Mami fa a gabanmu. Ni nace miki ina son Usainah, shi fa so bashi da wani ma'auni, kudi, ilimi, nasaba ko karfi duk babu ruwan so da wannan. Shi so halitta ne. Hajiya wannan shine abinda wasu mutanen suka gaza fahimta, shiyasa suke samun matsala da saɓani tsakaninsu da 'ya'yansu a duk lokacin da 'ya'yan suka fara soyayya da wadanda zuciyarsu ta kwanta. Wallahi Allah ina son Usainah da gaske kuma ita nake son na aura.”

Wannan rantsuwa da ya yi karaf a kunnuwan Usainah daidai lokacin da take shigowa falon. Ganin Usainar ya katse masa maganar ba tare da ya karasa ba. Ita kuwa Usainar ɗaki ta wuce wajen Mami.

Kabir ya cigaba da cewa, “Dama tun farkon zuwan yarinyar nan gidan nan naji ta kwanta min a rai, gaskiya bata dace da me aiki ba. Kawai dai ina ga rashin hali ne ya janyo mata, amma ki duba yanayinta.”

Hajiya dubansa take cike da mamaki, tace “Babbar magana, lallai zamani ya lalace kai tsaye Kabir kake fada min wannan zantuka. To naji, amma kaima kasan wannan al'amari zai yi wahalar tabbata. Ya ya zanyi da mutane kawayena da abokan arziki ace zaka auri 'yar aiki. Gaskiya ka sauya tunani, matsyunku ba daya bane.”

“Hmmm! Hajiya kenan, mutane fa kika ce? Ai indai zaki daka ta mutane to babu abinda zaki yi su yaba. Wadanda za suyi surutu ɗanki ya auri 'yar talaka, sune zasu yi surutun ɗanki ya lalata 'yar talaka. Babu abinda zaki yi, ki tsira daga harshen mutane. Sannan kuma maganar matsayina da nata ba ɗaya bane, ke zaki iya sauya mata matsayin, ki sauya mata rayuwarta da ta iyayenta, ki daidaita mu ni da ita. Wannan abu ne mafi sauki a wajenki. Hajiya wannan ita ce alfarmar da nake so ki min dan Allah.”

“Naji dukkannin abinda ka ce Kabir, amma gaskiya wannan al'amarin da sarƙaƙƙiya yake, to ya ya kake so nayi da Hajiya Zainab a kan maganarku da Farhan?  Kyakkyawar yarinya ce Farhan tana sonka sosai, kuma idan ka duba matsayinku daya.”

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now