༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 47 & 48*
Usainah ta mike ta kira Inna, Kabir ya ɗan risina tare da cewa, “To Inna ni zan tafi sai anjima da yamma zan dawo na dauke su.”
Ya sa hannu cikin aljihu ya dauko wasu kuɗaɗe ya aje gaban Inna tare da cewa, “Ga wannan a sayi ruwa.”
“Aah! Har da wata ɗawainiyar kuma daban, to Allah ya saka da alkairi, ka gaida hajiya, a sauka lafiya.”
“Amin.” Ya fada tare da mikewa, Usainah da Mami har ma da Hassanah suka rako shi waje, ya shiga mota ya yi tafiyarsa. Su kuma suka koma ciki, Hassanah ta kama wankinta tana sauri ta ƙarasa a sha hira ita da su Usainah.
Mami da Usainah kuwa falo suka koma, Usainah ta dubi Mami tace, “Wai kema ba zaki ci abincin bane ko ya ya?”
“Ke jarababbiya ni bance haka ba, ki kira Hassanah mana sai mu ci tare ko?”
“Ke kin ga idan zaki ci ki ci, koda bata ci abinci ba, yadda take wankin nan ba zata tsaya ba sai ta gama, ita haka take. Dan haka ki sa hannu mu ci kawai.”
Nan dai suka ci abincin su biyu, suna yi suna ta faɗan cacar bakin da suka saba. Mami ta saki jiki sosai babu wani nuna baƙunta, abinci ta ci sosai, suka cika cikinsu taf!
Bayan sun gama suka buɗe shafin sabuwar hira, abubuwa da yawa Mami take son yin tambaya a kai amma tana jin tsoron tsiwar Usainah. Duk da haka sai da tace,
“Dama kamar ku daya da Hassanah? Aiko da zamu haɗu da ita a wani wajen zuwa zan yi na rungume ta nace ke ce.”
“Hmmm! Allah ko, da ta yi miki ihu tace zaki ɗauke ta.”
“Haba dai sai kace ke, ai da ganinta ta fiki hakuri da kirki.”
“Eh ɗin naji ta fini, ta je tayi ta fina ɗin sai me kuma.”
“Allah ya baki hakuri baiwar Allah, ni ba da fada nake nufi ba. Ita ɗin dai mutuniyar kirki ce, shiyasa nake yabon ta, na san da ita yaya Kabir ya fara gani da ko kallo baki ishe shi ba.” Cikin sigar zolaya Mami take faɗin wannan maganar.
VOUS LISEZ
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
Fiction généraleCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."