Pɑge 67 & 68

12 2 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 67 & 68*

Saukar Mustapha a tasha keda wuya ya zaro waya, Hassanah ya fara kira. Tana ganin lambarsa jikinta ya bata cewa ya dawo gari, domin ya sanar da ita a gida zai yi sallah.

Ɗaga wayar tayi tare da yin sallama, ya amsa bayan sun gaisa, yace, “Ki shirya min kayan shan ruwa na musamman, yau tare dake zamu sha ruwa. Yanzu haka na iso Kano.”

Gabanta ne ya yanke ya fadi, ‘Na shiga uku ya ya zanyi? Ya zan iya haɗa ido da yaya Mustapha idan ya ji abinda ake ciki?’

A ɗan ƙanƙanen lokaci tayi wannan tunanin a zuciyarta, nisawa tayi sannan tace, “Kai dan Allah! Ashe muna da manyan baƙi a garin kenan. Mutanen Delta, barka da sauka.”

Cikin murmushi yace, “Yauwa barka kadai, to ya ya kuke ya su Inna da Baba da kowa da kowa, dafatan duk kuna lafiya.”

“Lafiyarmu lau wallahi ya ya hanya, dafatan kaima ka iso lafiya.”

“Lafiya kalau alhamdulillah, sai na karaso din.”

Gaban Hassanah ya cigaba da faɗuwa haɗe da tunani, ‘Wane zance zan fada masa ya gamsu ya amince dani?’ Hakika babu abinda ya sani, Umma ma bata fada komai ba. Da ace ya san wani abu, da zai yi min magana a kai. Wayyo Allah na! Ya ya zanyi ne?

Tana cikin wannan tunani ta lalubi lambar Usainah ta kira ta, tana amsawa tace, “Yaya Mustapha ya dawo.”

“Haba da gaske kike, yaushe ya dawo?”

“Kin ga yanzun nan muka gama waya dashi saukarsa kenan ko gida bai isa ba ya kira ni.”

“Allah sarki, aiko da sallah zamu haɗu a gaisa idan na zo gida sati ɗaya zanyi kafin na dawo, zamu je har Gwammajar. Dama Kabir ya takura sai da aka nemo wata me aiki, wai baya so ina yin aikin wahala.”

“Hmm! Lallai yana ji dake sosai. Usainah meye mafita ne? Ya zanyi da yaya Mustapha, me zan fada masa?  Wallahi tunda ya sanar dani, gaba ɗaya na shiga wata irin damuwa, na rasa da wane ido zan kalle shi?”

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now