Pɑge 121 & 122

12 1 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 121 & 122*

Mikewa Mustapha yayi tare da mikawa Kabir hannu suka yi musabaha, sannan na zauna kusa dashi. Kabir ya dube shi yace, “Ya aiki ya jama'a?”

Mustapah ya amsa da cewa, “Alhamdulillah! Ya hakuri da rigimar Usiainah?”

Dariya Kabir yayi yace, “Usainah gidan rigima kenan, ga rikici ga tsokana. Ka ganta nan dai sai fama muke.”

Cikin murmushi Usainah tace, “Kai yaya Mustapha ni ce ma me rigima, to na gode.”

Mustapha da Kabir sun dan taba hira tsakaninsu kafin Kabir din ya tashi ya bar falon. Usainah ma mikewa tayi ta tafi kawowa Mustaphan abinci, yayin Mami kuwa ta matsa kusa dashi. Ido ta tsura masa tana sakin murmushi tace,

“Ina sonka ina kaunarka, na mallaka maka birnin zuciyata, ka shiga kayi duk abinda kake so a ciki. You're my first love and you should be my last insha Allah. Har aljanna ni ce matarka.”

Makamancin kallon da take masa, irinsa shima ya rika yi mata hade da murmushin yana cewa,

“Ranki ya dade na gode sosai da wannan babbar kyauta da kika zabe ni a cikin maza badan nafi su kyau ba ko iya magana kika bani ba. Nayi alkawarin zan kula da wannan kasaitaccen birni wanda zai zama dausayi ga raina. Nima ina rokon Allah ya amsa addu'arki ya hadamu a aljannar.”

Lumshe idanu Mami tayi ta jinginar da kanta a kan kafadarsa, Mustapha ya dan zame kadan zai yi magana tayi saurin cewa,

“Meye haka kuma, so kake na fadi shine zaka janye jikinka? Idan ban jingina da kai ba, to da wa zan jingina? Kai ne madogarata, kai ne kuma garkuwata. Ka saki jikinka mun riga mun zama daya.”

Murmushi yayi har da sauti sannan yace, “Hakane ranki ya dade amma dai kin san...”

Dakatar dashi ta sake yi da cewa, “Eh na san komai ba sai ka fada ba. Kai kanka ka san zuciya da abinda take muradi ko, to ni matarka ce halak malak. Lokaci kawai muke jira a tara jama'a suyi sheda shikenan. Dan haka ina fatan ba wani dogon lokaci za'a saka ba, idan ma zai yiyu tare da nasu Usainah za'a hada ko ya ya ka gani?”

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now