༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 15 & 16*
Sannu a hankali 'yan uwa da abokan arziki na kusa dana nesa suka rika tururuwar zuwa dubiya da fatan alkairi ga Baba.
Alhaji Idi wan Inna bai je asibiti ya duba shi ba, haka ma yanzu da suka komo gida bai zo ba, sai dai matarsa da ragowar 'ya'yansa da suka rika zuwa a kai-a kai, su ɗin ma bada san ransa ya.
Shi ba komai bane yasa baya son zumunci, saboda kada ya kashe kudinsa ƙarda ne, Alhaji ƙankamo kenan. Hannun jarirai ne dashi. A tunaninsa yadda suke cikin ƙunci, matukar ya rika hulɗa dasu har ya bari 'ya'yansa suna mu'amala dasu Hassanah to dole ne su rika kawo masa bukatunsu.
Hatta da 'ya'yansa ɗin ma ba wata sakewa suke samu ba, ko babban ɗansa wato Mustapha dake karatu a Sokoto ba da san ransa yake kashe masa kudin makarantar ba. Sai da wani abokin kasuwancinsa ya shawarcesa, cewa, idan bai bari yaransa sunyi karatun zamani ba, to babu shakka yana ji yana gani za'a rika damfararsa, wannan ne dalilin da yasa ya kai 'ya'yan nasa makarantar boko.
Idan kaga an ɓanɓari wanann mutumin wani abu, to mace ce, macen ma kuma ta banza, ita kam ko nawa take so zai iya bata cikin ɓari da rawar jiki. Abin takaici ma ba manyan mata masu zaman kansu yake kulawa ba kaɗai, har da 'yan mata ƙanana, a takaice dai wannan mutum ɗan tasha ne tattacce.
To sai dai albasa ba tayi halin ruwa ba, Allah ya kuɓutar da dukkannin 'ya'yansa daga gadon wannan miyagun halayen nasa.
*** *** ***
*_BAYAN SATI DAYA_*
Bayan sati ɗaya da sallamar su Inna daga asibiti, Anty Laure ta sake dawowa duba marar lafiyar, sannan kuma su tattauna dangane da fara zuwa aikin Usainah. Bayan sun gaisa, ta yiwa Babansu Usainar sannu. A lokacin ne ma yaji labarin samowa Usaina aikin, fatan alkairi haɗe da godiya ya yiwa Anty Lauren.
Nan Anty Lauren tace da Inna, “Yanayin aikin shine a can gidan zata zauna, bayan sati biyu zata rika zuwa ganin gida.”
Daga Innar har Usainah basu ji daɗin tsarin aikin ba, ita Inna fargabar yau take, ɗan yau bashi da tabbas, ka haife shi ne amma baka haifi halinsa ba. Koda ace ita Usainar ta tsare mutuncinta, to idan kuma ya kasance akwai samari a gidan fa?
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."