Pɑge 43 & 44

12 2 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 43 & 44*

Usainah tace, “Ki je kawai ni ina nan, ai maganar hajiya gaskiya ce. Shan zaki idan ya yi yawa yana haifar da illa ga lafiyar jiki.”

Mami tace, “Au kema kin zama me wa'azin ne ko kuma likita ce? To ya yi kyau sai a yiwa wanda za'a yiwa wa'azin. Ni kunga tafiya ta.”

Mikewa tayi ta deɓi ledojinta ta nufi daki. Hajiya ta dubi Usainah tace, “Kema jeki kinji, ba hanaku sha nayi ba, amma dai a riƙa shan kaɗan.”

Usainah ta mike ta nufi dakin, tana shiga Mami ta kalleta a yatsine tace,

“Me kuma ya kawo ki keda bakya shan zaƙi? Kuma da kin san haka zaki yi da baki bari na sayo kayan da yawa ba. Ni saboda ke sayo. Idan kuwa dan kinji hajiya ta faɗi wannan maganar ne, to wallahi idan zaki biyewa hajiya sai ta hanaki cin komai a duniya. Ita ba lafiya ce da ita ba, shiyasa take ganin kamar kowa ma haka yake.”

“To ai kema ba lafiyar ce dake ba, gara hajiya ita larura ce daga Allah, amma ka fa? Me lafiya ba zai taɓa aikata abinda kike aikatawa ba.”

“Hmmm! Usainah wulakanci kike min yau, na ga neman rigima kike tun ɗazu, maganar da ranki ya miki daɗi kike faɗa min kai tsaye.”

“Yo ke ɗin me kika gama faɗawa hajiya yanzu, a kan tana faɗa miki gaskiya. Ko ba abinda kika gadama ba kika faɗa mata? Sai kace yanzu zaki ce ina faɗa miki magana, kin manta gidan radio nake faɗa miki.”

Mami tayi dariya sosai sannan tace, “Naji komai zaki faɗa min, ki faɗa lokacin ki ne. Yanzu dai ga kayan nan ki ɗauka ni bana son komai ke na sayawa.”

“Hmmm! Ni ina zan kai wannan kayan zaƙin haka? Kashe ni kike so kiyi kenan. To indai kema ba zaki sha ba, nima bana so.”

“To shikenan zan sha zo mu raba.”

Nan dai suka sha wasu chocolates suka aje sauran. Suka cigaba da hira, Mami kokari take ta ga ta kaudawa Usainah wancan ɓacin ran da ta saka mata.

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now