༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 17 & 18*
Nan suka sake mikewa tare, Mami ta zagaya da Usainah guraren daban-daban inda aikin nata zai kasance, daga karshe ta kai ta kitchen din gidan. Kasaitaccen kitchen ne da ya hada komai na bukatar rayuwa, sannan a tsaftace yake tamkar ma ba'a amfani dashi.
Shi dai wannan bujimin gida da Usainah zata rika aiki a ciki, gida ne mallakin wani hamshakin jami'in gwamnati a fanni tsaro. Amma ya rasu babu jimawa, ya bar matsarsa ɗaya, ita ce hajiya Kaltume, 'yar asalin Yobe ce, sai 'ya'yansu guda biyu kacal mace da namiji, Mami wacce aka bayyana a baya ita ce macen, namijin kuma ana kiransa kabir, shine babba.
Mami zata kai kimanin shekara 19-20, ta girmi Usainah da shekaru kamar biyu zuwa uku. Ta gama makarantar secondary boarding school, yanzu haka dai tana zaune a gida bata cigaba ba.
Kabir ya yi karatun health har matakin masters degree yanzu haka yana jagorantar wani asibitin kudi da Abban nasu ya gina gabanin ya mutu. Wannan kenan.
Bayan barin Anty Laure daga gidan tallarta ta shiga gari, sai da dare yayi sannan taje take wa Inna bayanin yadda a kayi, bayan sun gaisa take cewa,
“Hajiyar tace duk bayan sati biyu za'a rika biyan Usainah naira dubu goma ( ₦10,000) ladan aikinta, sannan kuma duk bayan sati biyun ne zata rika zuwa ganinsu.”
Inna tayi murna sosai tare da yiwa Lauren godiya sosai.
**** **** ****
To a bangaren Habib kuwa, lokacin da Babansu Hassanah ya cika kwanaki bakwai a gida, shi da hajiyarsa suka sake zuwa kara duba shi, koda yake shi dama Habib yana zuwa kuma yana kiran Hassanah a waya kusan kullum yana tambayar jikin baban.
Suna isowa kofar gidan, ya lalubi layin Hassanah ya kira ta yace, “Ina kofar gida tare da hajiya.”
Nan da nan Hassanah ta fito tayi musu iso zuwa ciki, Baba na ganin hajiya ya mike zaune daga kwanciyar da yake tare da cewa,
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."