Pɑge 97 & 98

12 1 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 89 & 90*

Mami tayi dariya tace, “Kema Hassanah akwai ki da tsokana, amma kiyi tambayarki ai malamarmu ce. Babu mamaki a cikin bayanin da zata miki na kara samun wani ilimin.”

Usaina tace, “Kanku ake ji, ni bari kuga nayi abinda yafi min wannan zantukan naku.”

Wayarta ta dauka ta lalubo lambar Kabir, kafin ta kai ga danna kira tuni nashi kiran ya shigo, murmushi tayi tare da cewa,

“Kun ga dan halak yanzu nake shirin kiransa, gashi ya kira ni.”

Ta fada sannan ta daga kiran da cewa, “Yanzun nan nake shirin kiranka, nace ko fishi kake damu saboda mun tafi shine kaki ka kirani.”

Dariya Kabir ya yi tare da cewa, “An gaisheki sarkin korafi, babu wani fishi da nayi. Hira muke tayi da hajiya shiyasa kika ga ban kiraki ba, sai yanzu zan kwanta shine nace bari na bawa zuciyata abincinta yadda zanji dadin bacci.”

“Hmm! Ka jika da wani dadin baki, da can kuma da kake baccin ba tare da kana bawa zuciyar taka abincin ba, baka jin dadin baccin kenan?”

“Wa ya fada miki bana bata abinci? Ai tunda na tunda zuciyata ta fara ganinki, to daga ranar ta daina kwana da yunwa. Kallon fuskarki abinci ne ga zuciyata, sautin muryarki abincin zuciyata ne, shaƙar ƙamshin jikinki da salon tafiyarki duk abincin zuciyata ne.”

“Lallai ka iya tsara zance me dadi. Ya ya gidan ya hajiya da fatan kowa lafiya?”

“Lafiya lau kowa yake sai dai ni abu daya na damuna.”

Usainah tayi murmushi tare da cewa, “Na san meke damunka doctor na, kayi hakuri zan dawo. Wannan lokaci ne na yin ziyara da gaishe-gaishen 'yan uwa da abokan arziki. Idan na dawo kuma shikenan fa, sai babbar sallah daga ita fa shikenan zamu kasance tare har karshen rayuwarmu.”

“Hmm! Kema kin iya kalaman kwantar hankali da saka nutsuwa cikin zuciya, shikenan Allah ya tabbatar mana da alkairi. Ya ya su Inna da Baba da fatan suna lafiya?”

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon