༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 49 & 50*
“Alhaji kenan, ka riga ka ɓata komai. Tun farko kaine me hakkin kula da 'yan matan nan har da iyayensu ma duka, amma sai ka watsar dasu ka tsane su tamkar babu wata alaƙa a tsakaninka dasu. Babu yadda banyi ba ka kula dasu, ka taimake su lokacin da suke bukatar taimakon amma sai ka toshe kunnenka. Sam baka so ayi maka zancensu, wanda ma ya yi maka zancensu shima ya shiga uku. Yaran nan suna son junansu sun dauko hanyar da zasu ƙarfafa zumunci, wanda kaine ya kamata ace tun farko kayi wannan haɗin amma sai ka sa almakashi ka datse zumuncin karfi da yaji. To ka ga al'amarin Allah yadda yake, jiya sunyi kuka yau kuma suna dariya, dan haka wannan sai ya zame maka darasi a nan gaba.”
“Tambayar ki nake ya ya za'ayi, kin zauna sai wasu surutai kike min na daban.”
“Au wannan maganar ce surutai? To ni bari na tambaye ka dan Allah, shin lokacin da ka rika tsara duk abinda kayi niyya ka nemi shawara ta a kan yadda za'ayi? Shin zance ma har kashedi kayi min kada na sake saka maka baki a lamuranka? Dan haka nima ban san yadda za'ayi da, indai wannan ne dalilinka na kira na, ka ga tafiya ta.”
Tana fada ta mike zata fita yace, “Magana nake miki shine zaki tashi.?”
“To Alhaji me kake so na fada maka? Kai baka so a fada maka gaskiya, ko mene ne ya faru laifinka ne, kaine ka shirya komai. Dan haka kai zaka warware shi, duk wanda zai fada maka gaskiya, dole ne yace kayi ba dai-dai ba. Ka wulaƙanta zumunci. Kana raye, kana da hali sosai da zaka iya inganta rayuwar yaran nan amma ka barsu suna aikin bauta, aikin wahala sun zama kamar bayi. Suna 'ya'ya mata amma su suke riƙe da kansu da iyayensu, a matsayinsu na 'ya'yan 'yar uwarka ciki ɗaya. Shi arziki da talauci duk na Allah ne, duk wanda Allah ya bawa dukiya to bashi kadai Allahn ya bawa ba, duk wasu makusantansa suna da kaso da hakki a cikin dukiyar nan. Sawa'un sun tambaya ko basu tambaya ba.”
“To naji meye shawara yanzu?”
“Ni yanzu shawara ta gare ka ita ce, shi zumunci ba dole sai sabga ko matsala ta tasowa mutum zaka je wajensa ba, lokaci zuwa lokaci zaka rika ziyartar su. Sannan ka bar yaranka suyi zumunci da 'yan uwansu, a hankali komai zai koma dai-dai, sannan kuma ka buɗe hannuwanka.”
KAMU SEDANG MEMBACA
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
Fiksi UmumCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."