༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 5 & 6*
Usainah tace, “Me zamu yi kuma a can ai mun gama sayen abinda zamu saya.”
Yace, “Eh na sani amma dai kuyi hakuri ku dan dawo.”
Hassanah ta juyo, yana gaba suna binsa a baya suka iso kanatin, daga baya su Hassanah suka tsaya yace, “To ku dan jira ni a nan minti biyu.”
Cikin kantin ya koma yasa aka dauko masa carton din taliya silver da na macaroni da semon vita shima carton daya da karamin buhun shinkafar Tailan, da Maggi me star leda uku da man girki na turkey oil da dai sauran kayan cefanen girki wadanda ake sayarwa a kanti rankatakaf ya hado musu, aka yi masa total kudin kusan dubu talatin da biyar, (N35,000).
Kudin dake jikinsa basu wuce dubu sha biyar ne (N15,000) ba kawai, dan haka sai ya tambayi me kantin idan yana amfani da bank account ya fada masa number sai yayi masa transfer, hakan kuwa aka yi, me kantin ya fada masa account number ya tura masa kudin nan take.
Wajen su Hassanah ya fito yace dasu, “Ga kaya can a kanti ya ya za'ayi a kaisu gida?”
Usainah tace, “Wane kaya kuma, na mene ne kayan?”
Da yake Hassanah ta lura da duk abinda matashin suka yi da Dahiru me kanti, sai tace, “Mun gode amma…” Dakatar da ita yayi da cewa, “Shikenan ya isa ina zuwa.”
Kusa da wani dan babban titi ne, ababan hawa nata zirga-zirga, keke napep ya taro aka loda masa kayan, ya kirgo naira dubu goma (N10,000) daga cikin dubu goma biyar din dake aljihunsa ya mikawa Hassanah tare da cewa “To ga wannan kunyi cefane ko.”
Kin karba tayi tace, “Mun gode ma da wannan sayayyar da kayi mana, Allah ya saka maka da alkairi, kabar kudinka kawai.”
“Amma dai ba roka ta kuka yi ba ko, ni nayi niyya sai dai idan alheri ne bakwa so.”
Karbar kudin tayi sannan tace, “Allah ya saka da alkairi mun gode.” Me keke napep yaja suka tafi, shi kuma saurayin ya cigaba da tafiyarsa a kasa.
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."