༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 9 & 10*
Inna ta fashe da kuka, cikin kukan take jerowa Habib wasu kalaman godiya da addu'ar tsari daga dukkannin sharri na sarari da na boye.
Habib yace, “To ni zan koma Baba Allah ya sauwake, Allah ya kara lafiya, sai Allah ya kaimu goben.”
Kafin ya mike ya zaro wasu kudade 'yan dubu-dubu masu dan yawa ya aje gaban Inna sannan ya mike ya fito. Hassanah da Usainah suka yo masa rakiya har waje.
Da suka fito wajen ne yake tambayarsu wane asibiti ne aka kai shi? Hassanah tace, “Asibitin Malam Aminu Kano ne, kuma naira dubu dari takwas da hamsin suke nema.”
“Babu matsala wannan, ku shirya da wuri goben zan dawo sai a kai shi.”
Su duka biyun suka hada baki suna fadin, “Bamu san wane kalmomi zamu furta maka ba na godiya, mun gode mun gode, Allah ya saka da alkairi. Ka ceci lafiyar mahaifinmu a daidai lokacin da kowa ya juya mana baya.”
Habib ya katsesu da cewa, “Wannan ai ba komai bane, duk yiwa kaine, wanda duk ya taimaki wani Allah zai taimake shi, Allah dai ya bashi lafiya. Ni zan wuce sai goben.” Suka yi sallama ya dauki hanya a kasa, su kuma suka juya gida.
Habib babu wanda ya sani a wannan unguwa, kai hasalima bai taba shigowa cikin layin nasu ba sai wannan lokaci. Ta gefen titi kawai yakan wuce jifa-jifa. Duk zuwan nan da yayi har sau biyu, da motarsa yake zuwa amma su Hassanah basu sani ba. Zuwa na farko da yayi har suka hadu a kantin Dahiru, katin waya yake nema sai yayi parking din motar a can baya gefen titi ya tako da kafa zuwa kantin. Wannan zuwan ma hakan yayi, aje motar yayi a baya ya karaso da kafa.
To bayan Habib ya bar gidansu Hassanah, yana tafe a mota yanata tunanin halin da yaga mahaifinsu, yayi matukar tausaya masa, a hannu guda kuma yana duban inda suke rayuwa ta wahala da kunci da rashi, yayi kukan zuci sosai 😓
Bayan haka a wannan zuwan ne ya samu sukunin ganin fuskarsu sosai. Duk da kasancewarsu a cikin rayuwar ƙangi da wahala, amma sun bashi matukar sha'awa da burgewa.
VOUS LISEZ
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
Fiction généraleCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."