༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 131 & 132*
A fusace Mami ta karbe zancen da cewa, “Ai yanzun ma ya riga ya gama bata komai, babu wani abu da yayi saura. Budurwarsa ce yana sonta tana sonsa, ni na hakura na bar mata kawai.”
Shiru suka yi mintuna kamar uku, kallo daya zaka yi musu ka fahimci zaman damuwa suke, babu me farin ciki a halin yanzu. Kowa fuskarsa ta sauya. Zuwa can Mustapha ya sauke aziyar zuciya ya dubi Mami yace,
“Ina son kiyi min alkawari daya india kika yi min zan fada miki gaskiya.”
“Babu wata gaskiya da zaka fada min na ji, wallahi nayi nadamar bads zuciyata inda ba za'a rike min ita ba.”
“Hmm! Kada ki ce haka, ya kamata ki bani dama na fada miki koda ba zaki yarda ba. Baki taba samuna da wani abu makamancin wannan ba, ga 'yan uwana sun fada miki halina. Koda yake ba dole bane ki yarda da maganarsu ba, saboda haka alkawarin ma bana so kiyi min, zan fadi gaskiya ba dan ki amince ba sai dan 'yan uwana su kara fahimta ta, duk da cewa basu taba min mummunar fahimta ba.”
Hassanah ce tace, “Yaya Mustapha bai kamata kaima ka rika fadin irin wannan maganar ba, kai fa babba ne kuma namiji. Duk abin ba na zafi bane ku bi hankali a warware matsalar ina ga yafi wannan cacar bakin da kuke yi.”
Mustapha yace, “To baki ji abinda take cewa ba komai ya kare a tsakaninmu, kinga dani da ita a samu wanda zai yi nadamar bada da zuciyar tasa. Ni bance bana sonki ba amma gashi ke kina tada jijiyar wuya kina cewa kin hakura.”
Usainah ta katse shi da cewa, “Ya isa haka yaya Mustapha, wace wannan din da ta kira wayar taka?”
Mustapha yace, “Hasiya ce nurse din da tayi jinyata ce a asibiti lokacin da na kwanta.”
“To amma ta fada mana wata magana wacce bamu san da ita ba, kuma ya ya akayi ma ta samu lambarka take kira?”
“Abinda ta fada muku gaskiya ne, ita budurwata ce. Hakan baya nufin bana son Mami, labarin yana da dan tsayi kadan. Abinda nake so kiyi hakuri, Allah ya huci zuciyarki, na san zaki ji ciwo sosai a zuciyarki. Nayi miki laifi ina neman afuwarki da yafiyarki. Abinda kuma kike tunani na rashin aldalci ko kyautatawa duk ba zaki samu ko daya daga wajena ba. Mami ina sonki, zan iya rabuwa da Hasiya amma ke ba zan iya rabuwa dake ba. Ina kaunarki, ni ba zuciyata na mallaka miki ba, kaina gaba daya na mallaka miki.”
أنت تقرأ
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
قصص عامةCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."