Pɑge 31 & 32

10 1 0
                                    

༺ *MATAKIN NASARA* ༻
  ━━━━💞༺۵༻💞━━━━

*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*

Written by:
                *Sɑdik ɑbubukɑr*

Wɑttpɑd @sɑdikgg

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           
______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*_♠️Dedicɑted To♠️_*
              👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*

*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

*Pɑge 31 & 32*

Duk wannan sha'ani da ake babu wanda ya sani walau Hassanar balle kuma iyayenta. Sai da aka kammala komai, kwana daya a tsakani, hajiya ta shirya tare da Habib suka taho gidansu Hassanar.

Misalin karfe 11:00am na safiya suka iso, Habib ya kira Hassanah yace, “Muna kofar gida ni da hajiya.”

Nan da nan ta fito, ta isa wajen motar, kanta sunkuye ta durƙusa har ƙasa ta gaida hajiya sannan suka shiga gidan gaba ɗayansu.

Hajiya ta zauna bisa tabarmar da Hassanah ta shimfida mata. Hassanah kunya ce duk ta baibaye mata fuska, shi kuwa Habib babu ruwansa, ya ma manta da wata aba wai ita kunya. Kawai so yake yaji mafaɗar zance, ayi a gama, su Malam Ibrahim su zo a tattauna dasu. Shi a nasa haukan ma da zai yiyu da hajiyar tayi magana da kanta tunda dai gashi ta sake dawowa, kawai ta nema masa auren a wuce wajen.

Inna ta gaishe da hajiya sosai, bayan sun gaisa hajiya tace, “Ina me jiki kuma?”

“Ai me jiki tunda jiki ya samu kuma babu zama ya dan fita amma ba nisa ya yi ba. Kai Khalid maza jeka kira Babanku kace masa haijya ce ta zo.”

Khalid ya kwasa a guje ya nufi wajen da Baban nasu yake zama ana hira, da isarsa yace, “Baba wai kazo inji Inna, hajiya ce ta zo.”

Baba ya mike suka taho tare da Khalid, yana shigowa dakin ya gaida hajiya tare da kara mika godiyarsa bisa abubuwan aikairan da take musu.

Habib ya mike ya fito daga dakin Hassanah ma ta biyo bayansa, wajen mota suka komo suna tasu hirar. Murmushi da annashuwa ne ke ta bayyana a fuskar Habib, ita kuwa Hassanah murmushin ne haɗe da kunya suka cika mata fuska.

A can ɗaki kuma hajiya ce tace, “Yaran nan ne naji suna son karawa zumunci ƙarfi, shine nace bari na zo naji kan zancen kada a barsu su kadai. Gara su san cewa mun san me suke ciki.”

Baba yace, “Babu shakka ƙwarai da gaske wannan daidai ne.”

Hajiya tace, “To Habib dai maraya ne, shekaru kusan biyar kenan da rasuwar mahaifinsa, Alhaji Sa'eed Na Kowa. To amma ƙanen mahaifinsa zai zo bayan sati daya sai a tattauna game da al'amarin.”

༺ *MATAKIN NASARA* ༻ Where stories live. Discover now