༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 93 & 94*
Gaba Habib ya wuce Usainah da Mami na binsa a baya sai Hassanah daga karshen baya, falo suka isa kai tsaye babu kowa a ciki sai television tana ta aiki.
Falo ne ƙayataccen wanda tsayawa bayyana yadda aka shimfiɗa naira a cikinsa ɓata lokaci ne.
Cikin murmushi yace, “Yau dai Allah ya kawo ku ɗan karamin gidan namu. Bisimillah ku zauna na kira hajiyar ko?”
Zaman suka yi kan wata doguwar kujera, Usainah daga dama, Mami a hagu sai ita kuma Hassanah a tsakiya. Ita ta zaɓi hakan saboda kunyar da take ji.
Ɗan lokaci kadan sai ga Habib tare da hajiyarsa sun taho suna magana, sai dariya yake. Suna ƙarasowa Hassanah ta sunkuyar da kanta kasa tare da ƙara mannewa jikin Mami.
Cikin sakin fuska da fara'a hajiya tace, “Ah ah kai madalla ashe baƙin namu da yawa, marabanku sannunku da zuwa.”
Usainah da Mami suma kunyar ce ta ɗan kama su, sai dai tasu bata kai ta Hassanah ba. Murmushi suke saukewa a fuskokinsu.
Hajiya da Habib suka zauna a kan kujera guda daya, Habib sai washe baki yake yana dariya yayin da su Hassanah suka zame daga kan kujera suka haɗa baki a tare suka gaida hajiya cikin tsantsar ladabi sannan suka koma kan kujera suka zauna.
Hajiya tace, “Ya ya mutanenbgidan kowa da kowa, ya sallah da fatan anyi sallah lafiya.”
Cikin sigar jin kunya Usainah tace, “Lafiya lau wallahi, Inna da Baba sun ce a gaishe ki.”
“To madalla ina amsawa da kyau, duk suna nan lafiya ko?”
“Wallahi lafiya ƙalau alhamdulillah.”
Hajiya ta dubi Habib tace, “Abbana leƙa wajensu Mero kace su kawo musu abinci.”
Ta fada tare da mikewa ta koma, shima Habib din mikewar ya yi ya fito daga falon domin cika umarninta. Wajen masu aikace-aikacen girki gidan ya nufa yasa aka zubo musu abinci. Da yake Habib mutum ne marar girman kai tare dashi aka dauko abincin aka kawowa su Hassanah. Mero ta dauko abinci shi kuma ya dauko ruwa da lemo suka ajiye gaban su Hassanah.
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."