༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 115 & 116*
Yau ce ranar dasu Usainah zasu koma can Bompai bayan shafe kwanaki bakwai cif suna hutun sallah ita da Mami a unguwar Tudun Wada. Tun safe Kabir ya kira Usainah yake mata tuni cewa yau ne fa ranar da zasu koma tare da bata umarnin lallai su dawo da wuri, shi kam da zasu dawo kafin karfe goma na safe 10:00am da sun kyauta masa.
Amsa masa kawai Usainah tayi da cewa to zasu dawo da wurin domin kada ya fara fadan nasa da ya saba. Duk kuwa da wannan gargadi da Kabir din yayi musu na lallai su dawo da wuri, amma hakan bai samu, maganarsa bata sa sunyi gaggawa ba. A tsanake suka yi shirinsu, sai bayan la'asar sosai suka kammala misalin karfe 5:00pm na yammaci.
Dama tuni sunyi sallama da Baba tun safe lokacin da zai fita, ya yi musu addu'a tare da sa musu albarka. Bayan sun yiwa Inna sallama, waje suka fito wajen mota, Hassanah da Khalid ne suka yo musu rakiya. Sun dan jima a kofar gidan suna hira da Hassanah kamar kada su rabu, kowa ransa babu dadi za'a rabu.
Mami kwalla ta fara zubarwa saboda tsananin shakuwa da tayi da Hassanah, dama ita haka Mami take bata da wuyar sabawa da jama'a, musamman wajen da ta samu shimfidar fuska. Dakyar Usainah ta rarrashe ta da cewa,
“Ki daina kuka mana abin farin ciki ne fa ya hada mu, ya ya kuma zaki kare shi da kuka. Ai ba mun rabu ba kenan har abada, kin manta cewa duk sati ina zuwa ganin gida, ba sai mu rika zuwa tare ba.”
Hassanah ta rungume Mami tana cewa, “Kiyi hakuri ba rabuwa fa muka yi ba, muna tare. Kamar yadda Usainah tace, zamu cigaba da kasancewa tare muna ganin juna koda ba kullun bane. Nima wallahi bana jin dadin tafiyar nan d zaku yi, kiyi hakuri kinji ki daina kukan.”
Ta fada tana share mata hawayen, Mami ta sauke wata gajerar ajiyar zuciya sannan tace,
“Shikenan na daina babu komai, na gode Allah ya saka da alkairi.”
Khalid dake tsaye a wajen hawayen shima ya fara tare da cewa,
“Anty Mami dan Allah kada ku tafi ku zauna a nan.”
CZYTASZ
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."