༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 57 & 58*
Murmushi Usainah tayi tare da sunkuyar da kanta tace, “Kai ma dai baka jin kunyar yin magana.”
“Ki bari kawai na gama cin nawa sai na rika saka miki a bakinki kina ci, hakan kike so koh?”
Zame murfin plate din tayi ta fara ci a hankali, domin ta san kaɗan daga aikin Kabir din ne, zai iya aikata abinda ya fada baya jin kunyar hajiya ma bare kuma wata Mami.
Kanta sunkuye take ciki, Mami tace, “Wallahi idan kika ƙware ko sannu ba zan miki ba, kin wani sunkuyar da kai ƙasa, ke gaki me kunya ko, me yasa baki zauna a gida ba tunda kunya kike ji?”
Ɗago kai Usainah tayi tare da cewa, “Malama bana son rashin mutunci kinji, har fata kike min na ƙware, idan na ƙware din ina ruwanki.”
Nan dai suka ci wanda zasu iya ci suka sha ruwa da lemon, sannan suka sake ɗora wata hirar sosai. Kabir ya tsaya ya ƙarewa Usainah kallon ciki da bai dinta, gaba da bayanta, sama da ƙasanta. Wato kyakkyawar yarinya ce fa.
A zuciyarsa yake cewa, “Gaskiya ba ƙaramin dace nayi ba, Allah ya yi halitta a nan wajen. Na tsinci dami a kala, 'lu'u-lu'u a juji' kenan inji Hausawa. Hajiya na son yi min cikas, wai wani Farhan kyakkyawa ce? Taje can ta rike kyanta ni na sayar.”
Sun jima a wajen shaƙatawar, sannan suka taso suka shiga mota. Basu zame ko ina ba sai Country Mall, Kabir ya yi parking suka shiga ya dubi su Usainah yace, “To gashi nan sai kuyi shopping din duk abinda kuke so kuma.”
Cart suka tura suna zagayawa cikin mall din nan, duk abinda suka gani dangin alawowi da biscuits da chocolate kala-kala dauka suke suna sakawa cikin cart. Shi kuwa Kabir wata madarar yoghurt da hajiya ke so ya dauko mata jarka biyu.
Suka tura kayan wajen biyan kudin, aka buga total, Kabir ya zaro katin cirar kudinsa ya mika suka cire kudinsu. Daga nan kuma gida suka nufo kai tsaye.
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."