༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 37 & 38*
Green Park suka isa, ya yi parking ya fito sannan ya bude mata kofa yace ta fito, tayi kamar ba zata sauko daga motar ba, amma ya takura mata, babu yadda ta iya haka ta sakko fuskarta cike da damuwa.
Yace "Ki saki fuskarki kada a gane kina cikin damuwa kin ga wajen jama'a ne, babu abinda zai sameki. Ice cream kawai zamu sha sai na maida ke gida."
Haka dai ya rika fada mata abinda zai sa ta rage damuwar, yana gaba tana biye dashi a baya. Kallo daya zaka yi mata ka fahimci baƙuwa ce a irin wannan waje, bata saba zuwa ba. Wata 'yar rumfa suka isa da aka yi mata rufin ciyawar zana. Kujeru ne masu zaman mutum bibiyu ko mutum uku ko huɗu har ma fiye da haka da tebura a tsakiyarsu.
Wajen me zaman mutane biyun suka isa Kabir yace, "Bisimillah zauna a nan ina zuwa."
Bin umarninsa ya zamewa Usainah tilas, domin babu yadda zata yi. Ba wanda ta sani a wajen banda shi. Zama tayi yayin da shi kuma ya nufi wajen da mutum zai fadi abinda yake so a kawo masa. Ice cream da wani haɗaɗɗen snack aka kawo musu.
Ya zauna kan ɗaya kujerar yana fuskantar Usainah yace, "To bisimillah ga ice cream ki sha ko."
Usainah fuskarta a ɗaure ba alamar fara'a tace, "Bana sha na ƙoshi."
Ya yi murmushi tare da cewa, "Wai har sau nawa zance ki kwantar da hankalinki, idan wani abu zan yi miki na cutarwa ba irin wannan wajen zan kawo ki ba. Kuma a matsayin ƙanwata na dauke ki, ki saki jikinki babu abinda zai sameki na rantse har da Allah lafiya zan maida ke gida."
Bata son cigaba da yi masa musu ko sa'insa, dan haka alatilas ta ɗan fara shan ice cream ɗin, shima yana sha yana sakar mata murmushi.
Yace, "Abinda yasa na dauko ki muka zo nan shine, ina son na faɗa miki abinda ke zuciya, wataƙila ma kin ɗan san wani abu kaɗan. Bakomai bane illa sonki da nake yi. Zan aure ki ne da gaske nake, nasan zaki ji maganar kamar a mafarki ko, to ba mafarki bane a ido biyu nake fada miki wannan maganar kuma har cikin zuciyata haka nake nufi. Ina sonki, ina sonki, ina sonki. Bana son jin duk wani uzurin da zaki bani a kan matsayi ko rashin dacewar ki dani. Indai kina sona ki amsa min yanzu a nan, sannan ina son ki ɗan bani tarihin rayuwarki."
BINABASA MO ANG
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."