༺ *MATAKIN NASARA* ༻
━━━━💞༺۵༻💞━━━━*_For indeed, with hardship there will be ease Qur'an 94:5._*
Written by:
*Sɑdik ɑbubukɑr*Wɑttpɑd @sɑdikgg
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
*_ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ᴜɴɢᴜᴡᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀsᴜ ᴅᴜᴋ ʙᴀsᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ ✍️✍️✍️._*
*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*
*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌**_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Pɑge 11 & 12*
Misalin karfe 1:45pm na rana Habib ya sake dawowa da abinci lafiyayye da nama zuƙu-zuƙu, daidai lokacin ita ma Usainah ta kawo abincin da ta dafa a gida - shinkafa da wake ne da mai da yaji da salad.
A wannan lokacin ne Habib ya samu sukunin keɓewa guri guda dasu Hassanar, tace, “Na rasa wace irin kalma zan furta a bakina domin nuna godiyata gareka, mun gode mun gode.”
“Karki damu da yin min godiya, Allah zaki yiwa godiya. Wannan abu da muke ni da mahaifiyata kanmu muke yiwa.”
“Godiya ta zama dole ayi maka, wanda duk baya godewa mutane to ba zai taɓa godewa Allah ba, saboda haka ina kara jaddada godiyata gareka Allah ya saka da alkairi.”
Sun jima suna hira su ukun, daga karshe yace zai tafi, ya bude mota ya dauko waya da layi sabbi kar! ya mikawa Hassanah tare da cewa, “Ga wannan wayar ki rike saboda idan akwai wani abu da ake bukata sai ki kirani, number ta na cikin layin.”
Wani irin yanayi taji ta tsunduma ciki, tunda take bata taɓa yin koda mafarkin rike waya ba, Allah me iko, Allah nagode maka, ni kam wane irin abu zan yiwa wannan bawan Allahn na faranta masa ransa? Na rasa ma ya ya zanyi masa godiya?.
A zuciyarta take wannan maganar bayan da ya mika mata wayar sai bakinta ya kulle ta gaza cewa komai ɗan lokaci me tsayi aka dauka sunyi shiru kafin daga bisani Habib ya dakatar da shirun da cewa,
“Ki karɓa mana tafiya zanyi, kuma idan na tafi ta hakane kawai zan san yadda ake ciki, duk abinda za'a bukata ki sanar dani kawai.”
“Dan Allah ka barshi babu abinda za'a bukata ma, bayan naga duk an gama komai hajiya ta biya, ni dai ka barshi kawai dan Allah, wannan ɗawainiyar ma da kake ta isa haka, Allah ya saka da mafificin alkairi mun gode sosai.”
Fishi ya ɗanyi har ya sauya fuskarsa kadan sannan yace, “Akwai abu guda ɗaya da bana so, idan nayi abu bana so ace ba'a so, duk abubuwan da nake yi ba tambayata kika yi ba, nine nayi niyya, kuma haka naga mahaifiyata nayi. Sai dai idan alherin ne bakya so, to sai na ƙyaleki, amma gaskiya bana son na sake baki wani abun kice ba zaki karɓa ba.”
YOU ARE READING
༺ *MATAKIN NASARA* ༻
General FictionCikin firgici da razani Umma ta yo kansa tana girgiza shi tare da yin salati, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, Mustapha me ya same ka, LA'ILAHA ILLALLAHU, na shiga uku. Wannan yaro da na sani da ban faɗa maka wannan magana ba."